Chapter 103
Chapter 103
kika saba". Yana rufe baki ta ce "Ni Iyah Basiru Ado Gogel idan ka mayar da ni ban yafe maka ba, ko da gwal aka yi ka na barka, ai da tun farko nasan kallon fasi'ka kake mini, da ka yi tsararo na bika, wallahi Mukhtar ko zaman mota bana fatan ya sake hadamu balle zaman aure! Idan har ni diyar Malam Basiru da Malama Salamatu ce na barka. Koda kai ne autan maza, idan kuma ban aikiata abin da ka jefe ni da shi ba, to na yafe maka, idan kuma na aikata ubangiji ya bayyana ni, na kunyata na kuma tozarta a idon duniya". Ta juya ta tafi sai da taje ba'kin kofar barin falon ta juyo, suka hada ido tunda kallonta kawai yake yi, ta ce "ka manta ka sanni domin kuwa daga yau nima na rufe shafinka, sannan hidimar da kake yi da ni ta makaranta ka dakatar bana so, ban bu'katar komai daga gareka, idan kuma har na ji alert din kudi zan mayar wa da Mahmoud, turowar kuma na nufin in sha Allah baza ka rabu da Hajiya lafiya ba". Ta juya da saurin gaske ta fita, ta bar shi a tsaye cikin mugun mamakin kalaman da ta jefa masa, mafi tayar da hankalin a ciki shine alakanta Jawad da datti, ko makaho ya shafa ya san Jawad jininsa ne, domin komai na jikin Jawad nasa ne, hatta tawadar Allah da Mk yake da ita akan lebansa Jawad na da ita. Bugu da kari da ta masa fatan mugun alkaba'i na rashin gamawa da duniya lafiya, to ai mahaifiyar ka itace duniyar ka. Da kyar ya ja kafarsa ya isa kan kujera ya fadi yaraf yana jin tamkar kansa ba a jikinsa yake ba tsabar nauyin da ya masa. Zuciyarsa ta kuntata sosai, gumi ya dinga karyo masa, fargabar auren da zai yi gobe ta sake nunkuwa, fishin da ya gani a tare da Sa'adah ya sake kassara shi, Anya haka kawai Sa'a ta bar shi kuwa, wanne irin so yake mata haka? Ya dinga tambayar kansa, a cikin wannan yanayin 'Karfi ya dawo ya tarar da shi. Cike da tausayawa ya ce "Bichi ka dawo da Sa'a itace matsalar ka, Ina jin fargaba kar hawan jininka ya sababa maka ciwon zuciya". A shake sosai Mk ya ce "Dan Allah 'Karfi ya zanyi ne, ban son auren nan da zan yi, ka taimake ni ka 'boye Ni". Ido kawai 'KARRFI ya zuba masa amma zuciyarsa sai harbawa take fiye da 'kima saboda yadda maganar Mk take nuni da rashin nutsuwar da mai yin ta yake ciki. Amma ya san ganin Sa'adatu ne ya gigitashi haka, da kansa Mahmoud ya dinga jinjinawa kansa, ya tabbatar Mk na mutuwar son Sa'a amma ya tabbatar bai fi shi sonta ba, kawai girman aminci ke hakurkurtar da shi, sau tari zuciyarsa da tunaninsa na fa'da masa ba haramun bane, ya gwada Sa'arsa kawai, amma da ya tuna girman Mk da tarin sadaukarwar da ya masa a baya, sai ya ji a ransa ana barin halak dan kunya! A fili Mahmoud ya ce " Ashe dai ni jarumi ne na gaske, Allah ka samu a cikin masu yin soyayya da abota saboda Kai". Mk da yake fama da zafin da Sa'a ta hada masa, bai fahimci 'Karfi ba bare ya nemi fashin ba'ki kan kalamansa. Hannuwan Mk ya ru'ko ya ce "ka yi hakuri nasan yadda kake ji, auren Nan na cikin kaddarar ka, ka karbe shi da zuciya daya, ubangiji zai buda maka kirjinka in sha Allah! Fatana dai ka dawo da Ummu Jawad, ka sau'ka'ka muku wannan dambarwar tura ta fara kaiwa bango, bana son a kai matakin da zata janye nadamarta tunda ka ki bata damar da zata gyara kuskuren ta, wallahi yarinyar nan ta gane kurenta, komin sharrin zuciya da mahassadi ansan dai ta nutsu ta fahimci rayuwa yanzu". Ido jawur Mk ya ce "mumunar karyace baka ga Tijarar da ta mini ba yanzu, sosai ta wulakanta ni tare da yi mini mugun fata, ashe so yana zama tsiya?" Mahmoud ya fahimci Mk yana cikin tension sosai sai ya kyale shi, ya rasa gane wannan masifar ta Mk, Yana son abu yana cutar kansa, yana cutar Yar mutane, haushin yadda Mk yake wulakanta Iyah yana neman samun muhalli a zuciyarsa. **** Ikon Allah kawai ya kaita gida lafiya, domin daga gidan Mahmoud ba tasan ya aka yi ta isa titi ba. Haka nan tunda ta hau abin hawa, bata sake sanin inda take ba, sai da Mai adaidaita ya ce "Malama mun iso fa, ta daga kai ta ganta jikin shagon da suke kwatance da shi, a sukwane ta fice yana ta Kiran ta tsaya ta karbi canjinta amma ina, ba ta tsaya din ba, ta dai samu sukunin daga masa hannu alamun ta bar masa. Tamkar an jefota haka Inna ta ganta ta fa'do, ta shige dakinta ta kwanta ta dinga gunjin kuka mai dafa zuciyar Dan Adam, kuka take yi na kaicon yadda rayuwa bata zuwa mata a yadda ta zace ta, kuka take yi akan kalaman Mk da suke nuni karara kallon mai cin amanar aure yake mata, wanne irin zalunci ne wannan? A hanzarce Inna ta bita dakin ya zauna kusa da ita, ta dauki kanta ta dora a cinyarta, a tausashe ta ce "Iyah ki daina bibiyar Muutar, ba zai mayar da ke ba, ki fita harkar sa idan ba kina son ni na fita a harkar ki bane, ki fuskanci rayuwar ki, ki bawa wasu dama kafin ya dawo kasar kema ki yi aurenki". Kuka kawai Sa'a ta ke yi na fitar hankali har da shidewa, sosai hankalin Inna ya tashi mussaman da taga yadda lebunan bakin yarta suka kubura tabbacin an musu dukan zalunci. Kwalla ta cika idonta ta ce Muutar ne ya dake ki haka? Me kika mayar da kanki ne Iyah? To saurare ni da kyau, kinsan daukan kafafuwan da kike yi kina binsa ba komai bane face Ballagazanci, duk shashancin namiji kuwa bai son Ballagazar mace! Wallahi ba zai saurare ki a cikin wannan halin ba, ki fita a harkar sa, ki manta da shi, ki tattara shi ki watsar, ba shi kadai bane namijin kirki ba, Ina tabbatar miki Sa'adatu akwai wadda suke son ki kwatankwacin son da Muutar ya miki, ki kwantar da hankalin ki, zaki Sha mamaki". Idonta dauke da hawaye ta kalli Inna da mamakin jin ta ambaci zahirin sunanta, Bata taba jin ta fa'di hakan ba, saboda riko da al'adar ba a fadar sunan uwar miji. "So nake na manta shi Inna, amma na kasa! fada min me zanyi na huta da azabar da nake ji ta rashin sa" Ta fa'da cikin rushewa da kuka sosai. "Ki ji a ranki yanzu ba kece a gabansa ba, da yana sonki, da ya hadaku ku biyu ya aura, hakan ma wani nau'i ne na ladabtarwa tunda komai nasa zai raba muku biyu ne maimakon da, da bashi da komai a gabansa sai ke da 'dan ki, na sani ke kika jawowa kanki komai ya miki, amma ai ya ladabtar da ke, sannan kin yi nadama kin sauke girman Kai kin bada ha'kuri, ya kamata ya yi ha'kuri shekaru hudu yana jan ki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157