Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 101

Chapter 101

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Sa'adah bata san mai yake going ba, sai ta fasa fa'da dan kuwa be kamata ace a bakinta aminiyarta zata ji wannan ba'kin labarin ba. Tasan da tana da waya da ta ji. Baffah da kansa ya fa'da wa Innah da Iyah auren Mk, ba Sa'a kawai ba hatta Inna kuka ta fashe da shi mussaman da ya tabbatar musu ya siyar da fili daya cikin filayen Sa'a ya biyawa Mk sadakin auren. Sosai suka tayar masa da hankalin sa domin irin kukan da suke tamkar ance Sumayya ta yi mutuwar fuju'a ne. Har cikin ran Inna take jin wani irin azabben kishi na ratsa ta, bata san kishi ba sai a ranar tunda ta wanzu ita kadai ne a wurin mijinta A kuma ranar ta fara jin tsanar Mk irin wadda bata yi zaton zata yi masa ba. Kuka na fitar hankali Sa'adah take yi 'karshe ta dinga kelaya amai ta hanci da baka. Hankalin Inna da Baffah ya yi tashin gauron zabi. Ranar Inna a wurin Sa'adah ta kwana karon farko da ta bar mijinta shi ka'dai alhalin suna gida 'daya. Sosai Inna ta ke jin takaicin Baffah a ranta, idan ba zai yi kishin 'yarsa ba, menene zai siyar mata da kadararta ya bawa tsohon mijinta kudin dan yayi aure, babbar damuwar ba wai Rashi ne yasa akayi hakan ba, kawai dan ya nunawa duniya har da shi a cikin masu musgunawa farin-cikin Iyah. Washagari da rashin kuzari ainun Iyah ta tashi, babban damuwarta ta ga Mk, ganin Inna ta shiga wanka yasa ta dauko wayarta ta 'kira layinsa, tana ta wasi-wasi ko an rufe layin?. Ai kuwa bugu 'daya ya shiga, da sauri ya 'daga zuciyar sa tana bugawa. "Malam ina son ganinka, ya za'a yi?" Yadda ya ji muryar ta, da yadda ta yi maganar ya san zancen aurensa ya sameta. "Ki saurare ni zan zo nan da awa guda". "Ni dai mu ha'du gidan 'KARFI". "Ok yanzu haka Ina gidan sai kin iso, ina jiran ki". Yana ajiye wayar Mahmoud na fitowa daga kicin 'dauke da ruwan roba da tumblers guda biyu, ya dire wa Mk yana ta faman cin magani, ko abincin da suka gama ci, haka suka ci tamkar kurame adalilin fishin da Mahmoud yake yi da auren da Mk zai yi nan da kwanaki biyu. Mk ya kalli Mahmod ya ce "Karfi ka daina wannan tunbatsar! kwanaki 'kalilan suka rage mini, na bar maka 'kasar ka huta da ganina". Da rauni ya yi maganar hakan yasa Mahmoud sassautawa ya ce "Mk tunda ka amince zaka auri yarinyar nan, to ka hada su da Sa'adah, wallahi kai take jira, ko mai ta yi maka ai ka hukunta ta, shekaru hudu ba wata hudu bane, ba kuma sati hudu bane, Ni kaina na taya ka jin kunyar Baffah, wallahi tallahi karfin hali kawai yake yi akan lamarin ku, shi ya haifi Sa'adah, alkunyar da yake yi fa ta kai geji". Kallo 'daya zaka yi wa Mk ka gane kalamin Mahmod sun sanyaya masa jiki kwarai da gaske, amma baya jin zai iya yin wannan al'amarin, ya kalle shi ya ce. "Mahmoud na 'dade da gane ban da kirki, Ni da kaina zaluntar kaina nake yi, saboda wallahi har ya zuwa yau ban huta da kewarta ba, ban daina jin cewar na tafka asarar rashinta ba, ina son na rayu da ita, amma tsoron ta nake ji, ko ayyanawa na yi a zuciyata ya kamata na bata wata damar, sai na shiga ru'du da tashin hankali". Ya yi shiru yana sakin ajiyar zuciya! Ya 'dora da cewa "wata'kila wannan na cikin 'kaddarata, na rayu a duniya ba da wadda nake so ba, alhalin tana raye". Mahmoud ya rasa abin cewa, tausayin Sa'a yake ji, amma yanzu har Mukhtar 'din tausayi ya bashi, ya tabbatar a matu'kar takure yake da 'kadddarar da ta fado masa na auren Farida ba'katatan Suna cikin haka! Yayan Mahmoud ya kira shi a waya, da sauri ya mi'ke yana cewa " yau tawa ta same ni wurin Auwal, sai da ya yi ta gargadi kar na bar shi yana jirah na. Mukallin mota ya 'dauka da sauri akan center table din da ke tsakiyar falon. Ya kalli Mk da ke kishingide bai da niyyar tashi, ya ce "ko na je na dawo?" Kai kawai Mk ya iya 'dagawa a dalilin mutuwar jiki, saboda yadda al'amarin Sa'adah ke damunsa. A hanzarce Mahmoud ya fita ya na fadin "saboda gidan ba kowa yasa ka yarda ka zauna". Da yake matar Mahmoud din sunje Kaduna bikin cousin sister dinta sai jibi zasu dawo. Mahmoud na fita 'kofar gidan inda ya ajiye motarsa, bai shiga da ita cikin gidan ba, saboda yasan ba wani jimawa zasu yi ba, kawai sai ganin Sa'adatu ya yi tana bawa mai adaidaitanm sahun da ya kawota, ku'dinsa. Da sauri ya karasa kusa da ita yana mata barka da zuwa, yana jin wani irin yanayin da ya ganta a ciki, alamun rashin lafiya da rasnin kwanciyar hankali baro baro a jikinta. Ba dan 'karfin dangantakar sa da Mk ba, da ya aure yarinyar nan ko ya huta da motsawar da zuciyarsa ke yi a duk sadda zai ganta, kai so masifa ne, Madallah da mutanan da suke sadaukar da soyayyar su dan halacci, aminci, ko masalaha. Suka gaisa, ta tambayi iyalinsa, Har zaice matarsa bata gidan, sai kuma ya yi shiru, ya ce "ki shiga, zan je na dawo". Ya dinga addua da fatan sulhu a tsakaninta da Mk. Tana shiga, kai-tsaye bangaren matar gidan ta dosa, ta dinga knocking, jim ka'dan Mk ya leko daga bangaren maigidan yana cewa "iso nan, bata nan matar gidan". Ta shiga falon da sallama, ta gaishe shi, sai kuma ta kasa magana, sun Jima a zaune suna ta sake-sake a zuci. Mk ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "ina jin ki, kin ce zamu yi magana". "Malam da gaske ne wai aure zaka yi?" Zuciyarsa ta buga, mamaki ya kama shi na yadda ya ji fargaba ta kama shi, saboda yadda ta yi tambayar muryarta na rawa. Ya kasa koda motsi, hakan ya tabbatar mata da gaske auren zai yi". Hawaye ya balle mata, ta ce " Na shirya fa'da maka gaskiya". Ya ce "Ina sauraron ki, waya baki kayayyaki nan?" Cikin kuka mai yawa ta ce Khalil ne! ya bani agogo da rigunan Jawad tsarabar Egypt, shine ita kuma Halima ta ce da ya bar agogon ya siya mini waya! sai kuma ya hado har da wayar". Ransa ya matu'kar baci tamkar yanzu abin ya faru, ya fesar da iskar bacin rai, ya ce "Ta hannun wa sa'kon ya same ki?" Da kukan ta ce "wallahi Safina da Halima ne suka kawo mini! wannan itace gaskiyar magana ban munafunce ka ba". Idonsa ya ka'da ya yi jawur dan tsananin kishi, ya ce "Munafunci kuma na nawa Sa'a! Ni dai kafin ki yi hakan wallahi ban ta'ba tunanin zaki mini wannan Munafuncin da aurena akan ki ba". Kukan Sa'adah ya 'karu ta ce "Tsautsayi ne, ban ta'ba yin haka ba, wallahi a lokacin da kayan suka zo sai da na ce tsoron kar gani nake yi ba zan karba ba". Ransa ya sake ri'banya baci a tunzure ya ce "Amma da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});