Chapter 109
Chapter 109
siya miki". Hawaye ya cika mata idanuwa, ta yi kokarin gogewa ba tare da ya gani ba. Sai da ta shanye kukan da ya zo mata ta shafa kansa ta ce "Allah ya nufa Jawad, ubangiji ya maka albarka, idan ka je ka dinga sallah da wuri, komai Anti ta ce ka yi, kada ka yi mata musu kawai ka yi, ka dage da karatu sosai banda wasa, domin wadda zai siyi jirgi sai ya zama mai jin maganar iyayensa ya kuma yi karatu tukuru. U.K. A airport suka tarar da Mk yana fama jiran isowar su, da Jawad ya hango shi, da gudu ya nufe shi, da azama Mk ya daga shi sama domin abin da Jawad ya ke so kenan ya ga Babansa ya daga shi sama ya'ki yarda ya girma. Taxi suka hau, zuwa gidan da zasu zauna, a hawa na takwas gidan yake dan haka Suka shiga lifta abin da ya burge Jawad, domin dai shine bai santa ba, tunda Farida ta saba fita kasashen waje. Gajiyar hanyar da suka kwaso bai hana Mk sake dorawa Farida wata gajiyar ba, domin a matu'kar takure yake sai da ya samu ya zubar da abin da ya takura shi sannan ya ji shi daidai. Rayuwa suke cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Mk ya shayar da Farida mamaki da ya samar mata gurbin karatu a Jami'ar da yake inda zata yi masters dinta duk dai akan sanin magungunan (Pharmacy). Ya ce " wurin aikin ki sun baki damar tafiya ne dan ki zurfafa ilimin ki, gara mu ki kiyaye ka'ida, sannan kema baza ki yi zaman kadaici idan bana nan, kuma Jawad yana school" Cikin gaskiya da amana take ri'ke da Jawad komai yake so yi masa take yi, duk sadda ta je makaranta bata mantawa sai ta siyo masa abinda zai ji da'di, sun shaku sosai, da ke mai son jiki ne indai suna zaune to kuwa rabin jikinsa yana jikinta, sau tari Mk ke cewa "kina fama da kanki, amma sai ki kama katon yaro ki jingina wa kanki". Murmushi take yi ta ce "Duka duka nawa ne adadin nauyinsa?" Sosai ta samu saukin Ciwonta duk tashin da zai yi baya kayar da ita, kamar sadda take Nigeria, domin kwararren likitan ('kashi) take gani a asibitin jamiar, sannan zurfafa ilimin da take a fannin magunguna ya na taimakawa wurin sake sanin maganin da ya kamace ta. Jawad yana ta karatunsa domin haziki ne sosai kamar Babansa bai yiwo shiriritar uwarsa ba, ko acan da suke da tsarin ilimi mai nagarta sosai yake ja, domin parfomance dinsa is very high hakan na farantawa iyayen nasa rai shiyasa komai ya ce yana so suke rige rigen yi masa. Ba abin da yake damunsa sai rashin Jin muryar uwarsa a waya, tunda Mk yana ha'dasu da Hajiyar Bichi, da kuma Baffah, amma ya kasa samun layin Inna da Sa'adah ta ke amfani da shi, ita kuma tunda take ganin missed call din lambar waje ta kuma gane lambar Ingila ce sai ta yi blocking din layin shiyasa basa samun layin. kunyar Baffah take hana Mk tambayarta. Rannan Jawad sun gaisa da Baffa ya ce "Baffah ka bawa Mami wayar zan yi magana da ita". Baffah da bai san Iyah ta rufe musu hanyar samunta ba ya ce "yanzu tana makaranta, Ni kuma bana gida ku nemeta a layinta ko na Innar ta. Domin kuwa basu jima da barin kasar ba ta ce da Sumayya tana son waya, a satin ta turo mata da kudin waya mai tsadar gaske, tunda murna suke yi ta yarda zata ri'ke waya, alamun ta cire komai a ranta akan Mk, zata fuskaanci rayuwarta ta gaba. Tsawon wattanni takwas kenan Jawad bai ji muryar uwarsa ba, a hankali sai abin yake 'dan ta'ba shi har abin ya fara bayyana a komai nasa, ya rage yawan surutu, ya daina walwala a tsakanin su, ya zama shiru shiru, sannan yafi son zaman daki fiye da falo. Abin ya fara damun su mussaman Farida, ta yi tambayar duniya ya ce ba komai, Mk da ya gaji da yadda Farida take yawan damuwa da canjin Jawad ya ce "kifa daina damuwa, tunda dai ba wani abin aka masa ba, miskilin yaro ne na gaske, ni na yi mamakin yadda ya sake da ke tashi guda". A marairaice ta ce "gaskiya akwai abin da yake damunsa domin ai ba haka ya ke ba, kamata yayi mu gano damuwarsa ko da cikin hikima ne". Ranar alhamis da yamma, Mk da Jawad suna gida, yayin da Farida ta ke makaranta adalilin tana da lectures. Cikin hikima ya hilaci Jawad akan ya ji me ya kawo changes din da suke gani a tare da shi, tunda bai fi sati da canjin nasa ba. Cikin muryar kuka Jawad ya ce "Mamina! Na dade ban ganta ba, sannan tunda na zo bamu yi waya ba". ya fada yana rushewa da kukan sosai. Jikin Mk ya yi sanyi yasan Jawad ya yi kokari wattanni takwas da yawa, domin bai taba yin wata daya bai ganta ba, ko da yake hannun Hajiya duk karshen wata sai ya je ya yi kwanaki biyu. Sannan tun farko yafi kulafacin uwarsa fiye da shi. Jikinsa ya janyo shi yana fa'din ka yi shiru yau din nan zaku gaisa, ai da tun farko ka fa'da mini wannan ne damuwarka da tuni na magance maka ita. Da kuka sosai Jawad ya ce "Am scared Malam". Da mamaki sosai ya ce "Mai ya ke firgita ka?" Last week na kalli wani firm a Fox movie (pendamic) yaron ciki ya tafi boarding school, shiru shiru bai ga mamar ta je ba, sannan baya samunta a waya Ashe she was died bai sani ba". Kuka sosai ya sake barkewa da shi, zuciyar Mk ta dinga bugawa tamkar Sa'adatu ta mutu ne da gaske sune basu sani ba, domin yadda ya santa da Jawad bai zaci za'a shafe wannan wattannin bata nemi jin lafiyarsa ba. Anya tunanin Jawad ba gaskiya bane? Ya kasa cewa komai bare ya rarrashe shi wani irin abu ke masa yawo a jikinsa, ga dai sanyi a garin amma wata irin zufa ne ta fara karyo masa. Ya dauko waya ya dinga gwada layin Inna amma sam baya tafiya. Dabara ta fa'dowa Mk ya dinga lalubo lambar Zainab Ma'aji amma bashi da ita. Ya rasa yadda zai yi sosai Jawad ya firgita shi shima. Da kyar ya shawo kan Jawad ya yi shiru bayan ya yi masa al'kawarin idan har ba'a sameta a waya ba, zai shirya musu tafiya Nigeria next week. Duk kokarin Mk ya samu Sa'a a waya ya ci tura. Tunda ko Baffah da ya mata maganar Jawad na ta cikiyarta ta daure ta kira shi su gaisa. Kai tsaye ta ce "idan da rabon zamu gana zai dawo ya tarar da ni, Ni bazan kira shi ba, tunda ba shi da wayar kansa". Daga Baffa har Inna ba wadda ya tilastata. Mk da ya gaji da kiran lambar Baffah yana cewa tana Makaranta ko shi baya gida, sai ya kira layin Sumayya ya bawa Jawad suka yi magana yana ta mata kukan yana expecting Mami has gone. Tausayinsa ya cika zuciyar Sumayya, ta dinga lallashinsa tare da al'kawarin daga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157