Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 151

Chapter 151

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana murmushin da wurshiryarta ta bayyana, hawaye kuma ya zubo mata Ta ce "Malam". Farin-ciki ya dirar masa fiye da wadda yake ciki, rabon da ya ji ta ambaci Malam a bakinta, tun ranar da suka hadu a gidan 'Karfi kafin komai ya tabarbare musu. Ya sa baki yana lashe dukkan hawayenta da yake zubowa. Ya yi gyaran murya ya ce "nan da kwanaki shida zaki tare, Ranar juma'ah mai zuwa. Yanzu mu je ki za'bi funtures din da kike so, masu harkar 'kawata gida, za su zo su shirya miki". A hankali ta ce "Na gode sosai! Amma ka barsu, domin yanzu ina da kishiya idan ta gane haka na zo, zata samu dama akaina". Ya kalleta ido cikin ido tsawon lokaci sannan ya ce "Na ta'ba rokon ki a shekarun baya ina so ki ji a ranki nima tamkar Sumayya nake a wurin ki, ashe baki dauke ni hakan ba?" Ta kasa bashi amsa. Ya ce "Wallahi Sa'adah ko wani kika aura ni zan miki komai da uba yake yiwa yarsa domin Baffah zan yiwa, lokaci ya yi da zai huta, a yanzu abin da nake ji game da shi ba wai kallon mahaifinki nake masa ba, kallon nawa uban nake masa, domin ya mini abin da na tabbatar uba ne kawai zai yi wa 'dansa. Na yarda da maganar da ake cewa ko baka haihu ba, idan ka yi alheri ga marayu da masu rauni, ka zauna da mutane lafiya, ka yi hakuri da cutarwarsu, to ubangiji sai ya turo maka wadda zai yi maka abin da ko 'danka ba zai maka ba, haka nan idan kana da zuri'a ubangiji zai baka wadda zai jibanci lamarinsu ko da baka numfashi". Baffah uba na ne, da ubangiji ya bashi, komai zan yiwa jinisa a duniya ban biya shi ba, dan haka ki yarda da ni, ko ba aure a tsakaninmu Ni din mai yi miki komai ne, mai kuma tsaya miki ne a ko Ina". Ya yi shiru! Sai kuma ya cigaba da cewa "wanccan gidan da kike magana akai tun ranar da kika ce mini filin ki Baffah ya siyar ya bani ku'di, zuciyata take ta bugu akan na baki shi kyauta, sai dai bani da halin bawa Farida irinsa, dan haka na bawa Jawad shi, na je an canja takardun, sunan Jawad ne akai. Idan na gamsu sosai zan iya ware miki gida, shikenan sai ki koma gidan d'anki kafin na samu damar da zan sake yi muku wasu gidajen a jere amma ko haraba ba zan ha'da ku ba". Karon farko da tasa hannu da kanta ta rungume shi tana kuka 'kasa-'kasa. Ta tabbatar da gaske Malam din nata ne har yau. Ta ce" na gode sosai ubangiji ya fini yabawa. Zan iya kokarina ban tayar da hankalinka ba, ba zan cuci matarka ta hanyar asiri, ko sharri ko zagon kasa ba, lafiyarta da mutuncinta har ma da dukiyarta amanace a gare ni, na yi maka al'kawarin ba zan tsokaneta ba, ba zan taba mutuncinta ba, ba zan yi shirka dan na farraqa tsakaninku ba, na yarda 'kaddararka ce itama. Amma abin da nake so ka yi mini dalci a ciki shine ni ban iya munafunci ba, am straight forward, ka ja mata kunne akan tsokanar da take fakar idon mutane tana yi mini, ba zan yi gaba da ita ba, amma kuma babu aminci a tsakaninmu da zamu zama so close, kowa ta yi harkar gabanta". Jiki na rawa ya dinga fa'din"thank you! Thank you so much my love". Saboda ba 'karamin nutsuwa ya samu na saukowar ta botsarar tasa ba,😅 ya dinga neman tsari da abin da zaisa ta sake mur'dewa. Ya tabbatar har zuciyarsa tsoron fishinta yake yi, tsoron ta birkice yake yi, 'karfin hali kawai yake gwada mata, idan yana bagarar da ita ko yana nuna mata iyakarta. Bai nemi ya sake ta'ba ta ba, duk da yana bu'katar hakan. A waya ta zabi furniture's din da take so, amma Mk ya canja mata da masu tsadar gaske, ta dinga jin tausayinsa, shikuma so yake ya wanke mata zuciya, ya sani dan ta kwantar masa da hankali ne, da kuma son ya fahimci ita yanzu ba luxury life a gabanta yasa ta zabi masu sau'kin kudi, shikuma sai ya daure ya siya mata masu daraja sosai tunda ya yi 'karfi yanzu, business dinsa yana garawa 'kwarai da gaske. Ya mayar da ita gida, suka rabu cikin shau'ki tamkar wani abin bai ta'ba gittawa a tsakaninsu ba. Kai-tsaye gida ya wuce tunda biyar ta yi, ya samu Farida a falo ta yi kwalliya ta sha kyau, ga abinci a dining, yana jiransa, ya dinga jin kunyar me zai ce mata kuma yau? Tunda yake fita da Sa'a baya cin abincin rana a gida, saboda tare yake ci da Sa'adah. Ya daure ya bita zuwa dinning din, ta zuba masa brown sphagetti da ta ji kayan lambu, sai papper fish a gefe. Ya dan ci ka'dan ya ture domin ya riga ya shafa'a ya ci a waje. Takaici ya 'kume Farida, idonta ya ciko da 'kwalla. Ya kalleta ya ce "menene yake damunki?" Da rawar murya ta ce "yau kusan kwanaki goma baka cin abinci na, jiyan nan ka gama yi mini al'kawarin yau zaka dawo mu yini tare, kai ka ce na yi maka wannan nau'in abincin, na yi kuma ka bar mini abina". "Yi ha'kuri my ferial! ba haka bane, ai dai kinsan duk safiyar duniya da abincin ki nake karin kumallo, idan na yi aiki na gaji ne, yunwa ta kamani sai na kasa daurewa na je capteria na ci, amma yi hakuri zan dinga jurewa". Yana rufe baki ta ce duk zamana da kai ban san kana zuwa capetaria kullum ba, sai yanzu dai da ka yi Kome! Na san abin da nake yi, Ina sawa abin da nake so ido fiye da kaina, kullum ka cire kayanka scent din Gogel nake ji, ban yi magana bane saboda na sani matarkace kuma cike kake da 'dokin sake dawowar ku abu guda, amma kuma shikenan sai abin ya zama ba waiwaye tun yanzu kake son sai dukkan rauni na ya bayyana? Ka yini a wajenta, ka dawo mini gida a gajiye da ka kwanta sai barci". Ta fa'da muryar ta na rawa. Sanin da ya yi ita din ba mai 'korafi ba ce, sai ya gano lallai bango ya nemi kaita, ya sani kuma da gaske ne ya watsar da ita a wannan tsukun. Dan haka ya sassauta murya ya ce "very sorry my dear! Ko ka'dan ba abin da kike nufi bane, amma tunda na bata miki, ki yi hakuri ki sake yi mini afuwa da uzziri. Ubangiji ya miki albarka, ke mai hakuri ce, mai kuma fahimta ce." Da haka ya lallaba ya jata bedroom, second round din da bai yi da Sa'a ba, ita ya yi da ita. Sai daf da magariba suka samu kansu, a gurguje ya yi wanka ya wuce masallaci, yana jinjinawa duk Namiji da yake da mace sama da guda, yake kuma tsaye dan ya yi adalci. Sai da ya dawo ya fa'da mata Sa'adah zata tare ranar juma'ah mai zuwa, ita kuma zata tare juma'a ta sama. A ranta ta ji ita

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});