Chapter 63
Chapter 63
na yafe miki, amma ki dinga sanin abin da za ki dinga fada mini". Da azama ta ce "In sha Allah, sannan don Allah ka hakura da kai Jawad Lagos, idan Allah ya kai mu na haihu sai ka kai shi, sannan ya kara girma". "Wannan ne kuma ba zai yiwu ba, ba kula shi, kike yi ba, idan na fita kullum hankalina, ba a kwance yake ba, Allah-Allah nake na dawo na kula da shi, kin ga aikina yana bu'katar nutsuwata, don haka ki yi hakuri, idan ya isa shiga makaranta zan dauko shi, idan kuma ta nuna sha'awar ci gaba da rike shi, to zan bar mata". Ta sake ri'ke hannun sa sosai, tana fadin, "Wallahi zan kula da shi fiye da yana jariri". "Na ji zan bar shi amma bisa sharadi". Da sauri ta ce, "Ina jin ka ko mene ne zan yi" Ya kalle ta ya ga ta matsu ta ji sharadin. Ya nisa ya ce "Ba za a yaye shi ba har sai na ce". Da sauri ta ce, "Na yarda, har sai na haihu ma". "Ni ba ruwana da haihuwa, ko kin haihu idan da yiyuwar ya ci gaba da sha, za ki dinga shayar da shi, idan lokacin sa ya yi, sai a cire shi! Idan kin amince da haka shike nan, idan bai miki ba, tabbas gobe zai bar gidan nan". Kai tsaye ta ce "shike nan na amince". Ya janyo ta, ya kwantar da ita a saman kirjinsa, yana shafa bayanta, yana fadin, "Allah Ya miki albarka Ya sauke ki lafiya." Yana ta ba ta misalai masu dadi, ba akanta aka fara irin wannan ba, sannan matan so ne su ke yin kwane.🤣 Rawahul Mk. ```Alkalamin *Surayya Dahiru* ✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 61-62. Washegari da karsashi Sa'adah ta tashi, kafin karfe bakwai na safe, ta kammala soya dankalin turawa da sauce, gefe kuma ta dama kunun gyada da ake yi da danyar shinkafa. Sai da ta share falon, sannan ta kai kayan abincin bayan ta shimfida ledar cin abinci. Tana cikin share tsakar gidan ya fito yana sabe da Jawad, ya kalle ta, ya ce, "sannu da aiki." Ba tare da ta dago ba ta amsa da, "yauwa!" Yana tsaye yana kallon ta har ta gama shararta ta kwashe, ta wanke hannuwanta, sannan suka rankaya zuwa falon, shi ya zuba musu, suka karya, Jawad na kwance yana ta shure-shure da furzar da yawu tabbacin yana cikin yanayin masu yin hakori. Suna kammalawa, ya shiga wanka, ya fito a shirye cikin shudin (blue) jeans da fararar shirt, mai yarfin blue, sai tashin kamshinsa yake yi. Har cikin dakinta ya bi ta ya tarar wanka ta yi wa Jawad, tun kafin a gama shirya shi ya yi barci. Cike da farinciki ya mikar da ita tsaye, ya ja ta jikinsa, ya rungume, ya rasa kalmar da zai fada mata, kowacce kalma sai ya ga ta yi kadan ta wakilci yadda yake jin ta a rayuwarsa, a karshe dai cewa ya yi "I really love you Sa'adah. Stay blessed!" Ya sake ta ya juya ya tafi ba tare da ya sake cewa komai ba. Ta dade a tsaye, cikin sanyi jiki, kalaman ba karamin tasiri suka yi a zuciyarta ba, da kyar ta tattara kayan Jawad ta mayar da komai inda yake, ita ma ta yo nata wankan ta shirya, ta kwanta kusa da Jawad, suka sha barci, don sai kusan sha biyun rana suka farka, ta fara kokarin hada abincin rana. Haka rayuwarsu ta ci gaba da gudana, ranar da tashi da karfin jiki, za ta yi komai, ranar da kuma jikin ba dadi zai yi abin da zai iya, kullum cikin tattalin ta yake, ba ya kaunar abin da zai tunzura ta, mai ha'kuri ne, amma a wannan yanayin da gimbiyar take ciki, ya sake ninka hakurinsa akan lamarinta kwarai da gaske yake tausayin ta. Har cikin ya shiga wata shida ba wanda ya sani, saboda kwatakwata ta ki fita, duk son ta da ta fita unguwa musamman gidansu, ko gidan su MK, amma yanzu juyin duniya ya yi da ita, fur ta ki zuwa, sai dai ta gaishe su ta waya. Tun Inna ba ta damuwa da rashin zuwanta har ta fara damuwa, idan lissafin ta daidai ne tunda ta koma gidanta sau daya ta je musu, sannan aka yi wattanni shida da zuwan. Ranar nan suna waya ta ce, "Iyah wato yanzu Jawad da mijinki sun debe miki kewata ko?" Da sauri ta ce, "Haba dai Inna! Kullum fa idan ban ji muryarki ba, kin san ba na jin dadi, har yaushe na same su! da za su dauke mini hankali?" "To ai gani na yi muna gari daya, amma ki iya shafe rabin shekara ba ki zo kin gan mu, mun gan ki ba. Mijin ki duk bayan sati biyu zai zo ya gaishe mu, abin mamaki har ki iya ba shi Jawad ya kawo mana, amma ke shiru! Anya za ki yi imani kuwa?" Jin haka ya sa Sa'adah ta fashe da kuka, tana fadin, "Ban da lafiya fa Inna duk zuwan da Uncle din yake yi bai taba fada muku ba?" A gaggauce ta ce "Me yake damun ki?" Kuka kawai take yi, da kyar ta ce "Ni dai idan na mutu ki yafe mini, ba da gangan na ki zuwa ba". Sai ta katse wayar tana goge hawayen, a fili ta ce, "Na san gobe zan gan ki kin zo, kin ga abin da nake boyewa." Hakan kuwa! Inna kwana ta yi tana zullumin wane ciwo ne ya addabi Iyah haka? Karfe goma na safe ta isa gidan don ma Baffa ne ya hana ta fitowar sassafe, da tuni ta dade da zuwa. Mamakin cikin da ta gani jikin Iyah ya zarta wanda ta yi a lokacin cikin Jawad, ta rasa mai za ta ce musamman da ta ga ya yi kwari, har yana shirin fitowa duniya. Ganin irin kallon mamakin da Innar ta bi ta da shi, yasa ta kifa kai a hannun kujera ta fara sana'ar kuka. Da tausayawa Inna tace, "Ni kin san akan koke-koken nan naki, muke batawa, mene ne kuma na kukan? Mene ne yake damun ki?" Sanin bata da matsalar komai sai na cikin nan da ya mata shigar sauri yasa ta kasa cewa uffan. "Idan na fahimce ki, halin da kike ciki yasa kika mayar da kanki mujiya a cikin jama'a, ke baki san baiwa ce Uabngiji ya miki ba, ai ba kowacce mace ke samun damar samun irin wannan haihuwar ba". Ta ja numfashi ta ci gaba da cewa "jiyan nan aka mana tarihin Nana Fadima a Islamiyyar da na shiga, ashe Sayyadi Hassan da Sayyadi Husain ba tagwaye ba ne? Duk zatona 'yan biyu ne, ashe daban-daban aka haife su amma Malamai sun yi ittikafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157