Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yi sosai ta na jin wata irin nutsuwa ta na shigar ta. Ashe har haka matsayinta yake, ashe darajarta ta kai haka? kai ta hau girgizawa, ta ce, "A a ban da matsalar komai wallahi, kawai dai fargaba nake kar ka canja mini kar ka juya mini baya". Murmushi ya yi yasan tana da hujjarta tunda an yi hakan a baya, don haka sai ya ce, "Aure ya wuce wasa ba na fatan kuma na rabu da matar aure na akan wata matar, ki cire wannan tunanin don yanzu ke ce matata, zan iya ha'kura da ita, matu'kar ta ce ba za ta zauna da ke ba, ke ko ba zan iya rabuwa da ke akan ta ba" Sai kawai ta saki kukan da take ta haniniya da shi akan kar ya zubo, ya 'dago ta ya shiga lashe hawayen nata, wanda na tsananin murnar maganganunsa ne ko da ba haka ba ne a zuciyarsa ya nuna mata girmamawa tare da karramawa, ta kuma gamsu yana son ta sosai. "Ubangiji Ya sanya alheri ya zaunar da mu lafiya, Allah ya 'kara maka lafiya, da bu'din arziki ya kuma hore maka ikon yin adalci" Amin ya ke ta fa'di tare da jin ba abu mai dadi a duniya irin mace ta gari, mai fahimta, mai kuma ilimi da aiki da shi, don sau tari shedanun matan masu ilimin ne, kawai aiki da shi ne ba sa yi. A fili ya ce, "Ubangiji Ya miki albarka My Feri-Feri, Allah Ya ba ki rabo mai amfani." Zuciyarta ta yi fes ta na jin dadin wannan addu'ar da yake yawaita yi mata na albarka da samun zuri'a mai albarka. Suna haka har aka kira La'asar sannan suka mike shi ya yi Alwala ya yi masallaci ita kuma ta yi a 'dakinta. Bayan ya dawo Masallaci bai shiga gidan ba a 'kofar gidan ya samu gefe ya zauna ya ciro wayarshi ya fara lalubo lambarta, karon farko bayan shudewar lokaci mai yawa, daf da za ta tsinke ya ji ta dauka, Sallama ta yi, ya amsa, sai kuma ta ja bakinta ta tsuke, shi kansa sai al'amarin ya zo mishi a bai bai, cikin 'karfin halin da aka san namiji da shi ya ce, "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Cike da son ta nuna mishi ba shi da sauran matsayi a zuciyarta ta ce, "Waye?" Bai yi mamaki ba, dan haka sai ya nufin 'kunsa mata takaici shima. "Wadda ki ke ta sallar dare ne akansa". Yana rufe baki ta ce, "Babu wannan halittar" tare da kashe wayarta. Zuciyarta na bugawa wai yau mafarki take ne ko kuwa da gaske Malam ne ya kira ta taka nas? Wacce iriin sa'a yau ta tashi da ita? tana tuna kalaminshi na 'karshen maganar su a wani lokaci da ya shu'de, sai ta ji murnarta ta koma ciki, ba za ta saurare shi ba har sai ya janye kalamunshi, da kallon da yake mata, idan ko ba haka ba, to tabbas ba za ta sake mu'amala da shi ba, bare babbar mu'amala irin ta aure, ko da hakan na nufin mutuwarta ne. Al'kalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼✍🏼 [5/16, 13:26] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR* *Fatan Alheri ga* _DANDALIN MUM KHADY_. 🤝🏽 15-16 Mamakin ta ne ya yi matu'kar kama shi wai yau shi ta kashe ma waya? Anya Sa'adah za ta canja hali kuwa? Sake 'kiran ta ya yi a karo na biyu, amma ga mamakin sa har 'kiran ya katse ba ta 'daga ba. Ya ri'ke wayar ya yi jim cikin sanyin jiki da tunani iri iri. Ya san kirkinta ya fi sharrinta yawa, har yau kuma, shi dai a idanuwanshi bai ga wacce ta iya tsara kwalliya da gayu irin Sa'adah ba, ma'abociyar son 'kyale-'kyale ce, kusan wannan dabi'ar tata na son kayan 'kawa masu tsadar gaske ya taimaka wurin sake jefa aurensu cikin garari. Lambar amininshi ya lalubo Dr. Mahmoud Karfi, ba ta dade tana dokawa ba, ya ji an 'dauka, tare da sallama, kai tsaye MK ya ce, "Kana Ina?" Daga can bangaren ya amsa da cewa, "Ina makaranta, lafiya?" "Lafiya Lau jira ni gani nan zuwa" Ya katse wayar ya mi'ke ya shiga gida, ya dauki mukullin motarshi, tare da yi wa matarshi sallamar ya fita, ta bi shi da addu'ar dawowa lafiya. "Kai tsaye sabuwar Jami'ar Bayaro ya nufa, bai bi takan ofishin saba, ya zarce ofis din Dr. Mahmoud Karfi. Da sallama ya shiga shi ka'dai ya tarar yana dakon isowarsa, musabaha suka yi, Dr. Karfi ya dube shi, "Ka sa ni tunani iri iri fa" Jim MK ya yi tare da cewa, "Wallahi ru'dani na shiga, ka san Hajiya ta matsa akan maganar na dawo da yarinyar nan, to dai yanzu na amsa mata akan na amince bayan na yi addua na kuma ji na aminta da lamarin. Wai yau na 'kira ta a waya da farko ce mini ta yi waye?" Dariya ta so subuce wa Dr. 'Karfi, amma ya kirne, shi kuma ya zarce da cewa, "Karshe kuma sai ta kashe mini waya" "Alhamdulillah!" 'Karfi ya furta a fili tare da cewa "Ni na da'de ina ji a jikina idan dai ba mutuwa ce ta sure dayanku ba, to kuwa za ku sake ha'dewa. Shi yasa na kyale ka ka sami nutsuwa, ka san dai Sa'adah ta bi ka iyakar bi akan ka yafe mata, amma ba ka yi ba, ka zo ka yi aure dole ta gaji ta yi fishi, amma na san fishin ba mai yawa ba ne, tunda tana son ka." A sanyaye ya ce, "Anya kuwa? ba ku san ta ba ne, a makarantar su Jawad fa baka ga iya shegen da ta mini a bainar nasi ba" Dariyar da Dr. 'Karfi ya ke ri'kewa ta subuce, ya hau yi sosai, har ta sha'kar da MK, don haka sai ya mike ya ce, "Na gode" Da sauri 'Karfi ya ruko shi ya na fadin, "Yi hakuri ka zauna ai ba mu gama ba" Cikin fushi ya ce, "Ya zan zo maka da matsalar da ta dame ni, ka sani gaba kana mini dariya ka mayar da ni mahauka ci!" "Wane ni Allah ya huci zuciyarka zauna mu gama" 'Karfi ya fada bayan ya shanye dariyarshi. Komawa ya yi ya zauna amma fuskar nan a ha'de. "Yanzu ka san me? Zan je na same ta mu yi magana, idan ya so sai mu koma tare, daga nan kuma shike nan sanda za ka je ma ba zan sani ba" Cikin cin magani ya ce "Ni wallahi bazan ta zarya a wajenta ta na mini iya shege ba, yanzun ma Hajiya ce ta matsa amma banda haka ta je can ta 'karaci tsiyarta" Mahmoud ya ce, "Yanzu ma damuwar da na gani a fuskarka, akan ta kashe maka waya, Hajiya ce ta matsa ka fada mini?" Tsaki ya ja, ya san sha'kiyanci zai masa, tunda idan akwai wanda ya san yadda yake son Sa'adah to kuwa Mahmoud ne. Sai kawai ya mi'ke ya fice yana fadin, "Sai ka

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});