Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Wai waye?" Ba a jima ba ya dawo ya ce, "Wai Mukhtar ne." Dadi ya kamata da sauri ta ce, "Je ka ce ta na zuwa." Ta juya ta ga hakimar ko motsawa ba ta yi ba tana ci gaba da yankan farcenta, kamar za ta yi magana sai kuma ta shanye, tana mai son ganin iya gudun ruwanta. Fiye da shudewar mintina goma tana zaune ta gama yankewar. Amma sai ta tsiri kankarewa, zuciyar Inna ta hau ba tare da Iyah ta ankaraba, kawai ta ji saukar duka da mafici a zabure ta mike tana dire-diren shagwaba tana cewa, "Me na yi kuma na duka Inna?" Dakuwa ta mata da hannunta na dama tare da cewa, "Za ki wuce ki dauko mayafinki ko kuwa?" Ta shige dakinta tana cewa "Daga zuwansa zan debi jiki na fita, ba jan aji ba komai, salon ya ga arhata." Mahaifiyarta bin ta yi da kallo, jiki a sanyaye ta rasa bakin magana, ta shiga dakinta ta fito da lemon kwalba guda biyu, da Swan roba biyu, da tuni Baffa ya tanada saboda zuwansa, ta zuba mata a kan faranti mai kyau ta ajiye. Kan dole ta bi ta dakin a zaune ta same ta ta sake gyara fuskar ta yi kyau sosai ga mayafin da ya dace da zaren surfanin dake jikin rigar, kamshin tsadadden turaren Escada sai tashi yake a dukkan dakin! Sassautawa ta yi ta ce, "Yanzu zama ki ka sake yi Iyah? ko ba komai ai malaminki ne, malami kuwa ai kamar uba ne, ki duba fa tsawon lokacin da kika shanya shi yana faman jiran ki?" Bata ce komai ba ta mi'ke ta fice ta dauki tabarma, ganin ruwa da lemo a kusa da tabarmar yasa ta ganewar iyayenta sun fi ta kambama lamarin MK. Tabarma kawai ta dauka ta nufi zauren, a tsaye ya jigina da bango ta same shi. Sanye yake da farar shadda kal (Bankole style) ya dora hula ba'ka, kafarsa dauke da bakaken cover shoe. Sallama ta yi tare da shimfida tabarma sai da ya zauna sannan ta zauna ta gaishe shi. Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamshin turarensa na Versace da wanda ta yi amfani da shi Escada suka cakude suka cika zauren da wani irin lafiyayyen kamshi mai nutsar da zuciya. Tsawon mintina suna zaune shiru, ita kanta a kasa yake tana ta wasa da yatsun hannunta da ta musu kwalliya da zobuna (fashion). Shi kuma kawai kallon ta yake yi, yana nazarin yadda ta iya tsara simple kwalliya ta burgewa tamkar wacce take karantar fashion and design. Gani ya yi ta mik'e tana cewa, Ina zuwa." Ba ta jima ba ta dawo dauke da faranti a hannunta ta ajiye a gabansa. Ta koma in da tashi ta zauna. Can ya nisa ya ce, "Wai fishin ne har yanzu?" Takaicin sa ya makure mata wuya, tunda ya zo ban da kallon ta bai ce komai ba, sai gaisuwar da ya amsa mata ba karsashi, shi ne yanzu zai ce wai fishi take yi, so yake ta saki baki ta masa hira bayan shi ya kame bakinsa ya tsuke, saboda yana jin isa? Don haka sai kawai ta daure fuska sosai, sannan ta juyar da kanta gefe ba tare da ta ce ko mai ba. Dariya ta kamashi ya murmusa, sannan ya ce, "Ke kullum a cikin fishi kike? Da kin san yadda murmushi yake sake kawata miki fuska da kullum kin kasance a cikinsa" Ba ta ce komai ba, ya yi shiru yana nazarin mai zai ce da zai sa ta kula shi. Ya nisa ya ce, "Babana ya yaba da karbar da Baffa ya masa, ya yi murna sosai har cewa ya yi na iya zaben suruki, yana fatan a ce ke ma ki yo halin karamci irin na gidanku " Ba ta ce komai ba amma ta sassauta daurewar fishin, yana kula da ita, don haka sai ya sake cewa, "Kin san kafin na zo raina a bace yake da ke amma kina fitowa na ga wannan kwallliyar da aka cancanda mini sai na ji na manta komai! Ke kawai nake gani kin cika ko ina fiye da duniyar gaba'daya!" Dadi ya kamata ta murmusa kadan, amma ba ta ce uffan ba. Ya dade yana rarrashi kafin ta ware su yi hirarsu, cikin dabara ya tabbatar mata ai ya gan ta da Khalil suna hira a class shi ne kuma dalilin da ya hana shi zuwa, don Allah ta kiyaye. Ba ta musa ba, cike da dariya ta ce, "Shi ne dalilin da ya sa ka ninka dukan da ka mini?" "E, saboda ki ji dan kadan cikin takaicin da nake kwana ina tashi a cikinsa." Bai tafi ba sai da aka fara kiran sallar maghrib, ya mike yana cewa kawo mini buta na yi alwala. Tana tsaye har ya yi alwalarsa ya mayar da agogon da ya cire ya zura hannu ya ciro sabbin yan dari-dari da suka sha turare guda ashirin ya mika mata da 'kyar ta karba wanda sai da ya rantse akan sai ta karba, sannan ta sa hannu biyu ta karba, ita kanta a ranta addu'a take Allah ya sa kar ya mayar da kudinsa! Ta ga samu ta ga rashi 😁 a wancan shekarun dubu biyu tana da daraja ba kamar yanzu ba. Ta kalle shi a kunyace ta ce, "Ka tsaya sai ka rasa sahun gaba, Baffa yana ta cewa kullum a sahun gaba kake sallah." Dadi ya kama shi tare da cewa, "Ashe har kamfen Baffa yake mini a gunki, lallai ki ce na kwantar da hankalina, na same ki na gama! Amma yanzu ba na iya zuwa wurin da yake yin sallah, kunyarsa nake ji." "Ta yi dariya sosai ta ce, "To kuma a ina kake yi?" Ya kalleta yana jin wani irin abu na tsirga masa da sauri ya fice yana cewa, Nan Masallacin bayan layi nake zuwa." Ya tabbatar sai ya sake alwala saboda yadda ya tsinci kansa cikin yanayi na sha'awa sosai. Bata lura da yanayinsa ba ta dauka kawai gaggawa yake yi tunda an tayar da sallah, shi yasa bai bari sun yi sallama ba. Sai da ta yi sallah sannan ta je falo gun Inna ta mika mata kudin da ya ba ta, za ta fita ta ce "Zo ki zauna." Kusa da ita ta zauna, a hankali ta ce, "Ina fatan dai ba shi da matsala ko Iyah!" Dariya ta kama Sa'adah ta cije ba ta yi ba, amma sai ta yi nufin tsokanar Innar, don haka sai ta ce "Ba shi da matsalar komai Inna amma gaskiya ni wanzancin da yake yi ne bai mini ba!" Ta fada a dake tamkar gaske. Salati sosai Inna take yi tana karawa, amma sai ta taushi zuciyarta cikin lallashi ta ce, "Iyah mene ne laifin sana'arsa saboda Allah? Ai abin alfaharinmu ne duka ace matasanmu sun daina zaman banza, sun daina zaman jiran gwamnati ta basu abin yi, ke yanzu raina wanzancin kika yi? To bari ki ji tun a lokacin ma'aiki akwai wanzamai, sannan duk inda wanzamai suke mutane ne masu amana masu kuma tsananin zumunci, bare kawai don yana da shagon aski sai ki mayar da shi wanzami?" Dariyar da take dannewa ta kubuce ganin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});