Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wanka, ta shirya cikin guntuwar rigar barci cotton marar nauyi, ta zauna shan black tea, amma zuciyarta na tunanin ko MK ya yi barci, ko me yake yi, ko shima fishin zai dauka yau ba zai zo 'dakinta ba? Ta dade a falo kafin ta kashe fitila da fanka ta shige daki ta kwanta, adduar barci ta karanta ta shafe jikinta, tana ta tunani, sai ta ji shigowarsa, dadi ya ratsa ta har da sakin ajiyar zuciya. Yana tsaye ya kunna fitila idonsu ya hadu, nan da nan ta dauke idonta, ya kashe fitilar ya nufi gadon yana kwanciya ya janyo ta jikinsa ya saki ajiyar zuciya tare da fadin "Ni ba zan iya fushi mai yawa da ke ba, bacin ran da kika sa ni dazu na yafe miki kin ji My Sa'adah! Ke ma ki yafe mini abin da na miki, ki kuma fada mini din kar na sake maimatawa a gaba". Uffan ba ta ce ba, amma farinciki ke ratsa ta yadda yake ta rawar jiki da neman sulhu. "Kin ji" Bai jira amsarta ba ya sake cewa " Don Allah me na yi haka har zuciyarki ta gaji da zaman mu tare, ban yi zaton akwai abin da zan yi ki daina sona ba". Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, hawaye ya cika mata ido, cikin rawar murya ta ce "Ban daina sonka ba ai, kawai ha'kura zan yi don shi ne ya fi alheri tun ba ka juya mini baya ka fara wulakantani ba". Jikinsa ya yi sanyi kalau, a sanyaye ya ce "Mafarki kika yi akan zan juya miki baya, yanzu a zaman da muka yi ba ki fahimci irin son da nake miki ba? Kin fi karfin ki wulakanta a hannuna." Ta kasa cewa komai saboda tana bude baki kuka za ta yi. Ya sake cewa "Na ji dadi da ba daina sona kika yi ba, ina hada ki da girman Allah ki fitar da ni daga duhu, me na yi miki?" Kukan da ta ke matsewa ya subuce mata, hawaye har a kan kirjinsa, ya rasa abin da ya ke masa dadi, hankalinsa, in sun kai dubu to a tashe suke. Haka ya dinga jijjigata yana shafa gadon bayanta tare da fadin sorry, tamkar mai mata bita. Da kyar ya shawo kanta ta bude baki ta ce "Tun farko na so na hakura da aurenka saboda yadda kake nuna mini am nothing to you, sai dai na san Baffa ba zai fahimce ni ba, tunda sai da ya tambaye ni na ce ina sonka, iyayenka sun zo gunsa to ba ni da sauran dama, ban isa na ce na fasa ya saurare ni ba". Ta sarara, ta ja hanci sannan ta dora da fadin, "Muna cikin wannan yanayin, sai na yi kuskuren shiga motar saurayi, kuskuren da ni kaina na yarda ban kyauta ba, ba irin ha'kurin da ban baka ba amma ka 'ki, karshe na sake yin wani kuskuren na dauki jiki na bi ka har inda kake, don ka gane yadda fushin ka ya hana ni zaman lafiya. Sai ka bi ni da wulakanci kala-kala har ka iya ce mini Ballagaza akan idona!" Kukanta ya dawo sabo, ta shiga yin sa har da rerawa tamkar a cikin nisha'di take, don kawai ta sake tayar masa da hankali, ai kuwa gogan ya kasa cewa komai tsabar yadda komai ya tsaya masa, yana tuno Baba Idi da ya ce lamarin mata yana da gigitarwa, tabbas ya yarda ga shi 'yar yarinya karama tana neman zautar da shi. Cikin kukan ta ce "Tun lokacin na tabbatar barin ka shi ya fi alheri, tunda za ka iya jifa na da wannan mummunar kalmar a ranka, sai kuma na ga gara na nuna maka ni ba ballagaza ba ce, hakan kuma ba zai yiwu ba sai mun yi aure dole, zuwa yanzu na san ka gane in ma ni Ballagazan ce ko a kasin hakan". Tsawon lokaci MK ya kasa bude baki ya yi magana. Ya yi shiru yana jin kukanta har cikin kwakwalwarsa. Da kyar ya bude baki murya ba sauti ya ce, "Ba har zuciyata nake nufi wannan kalmar ba, subul da baka na yi". Da sauri ta ce"Ai sai da na tambaye ka, ni ce ballagaza, ka ce e, idan akwai kalmomin da suka fita muni na hada da su domin na siffantu da hakan". "Billahillazi Baby kishi ne ya rufe mini ido a lokacin, amma ba har zuciyata hakan nake nufi ba, na yarda na yi laifi ki yi ha'kuri na tabbatar ke din katangaggiya ce". Zamewa ta yi a jikinsa ta koma karshen gado tana sake sabunta kukan da take yi tare da fadin, "Ni ba zan hakura ba, kai ne za ka yi ha'kuri kar ka wahalar da ni". Mirginawa ya yi ya tarar da ita a karshen gadon, ya riko ta tana tirjewa, kukan gaske take yi, har da bubbuga kafa tamkar yar karamar yarinya. Kwantar da murya ya yi sosai tare da cewa "Babyna tsaya ki ji, tsakaninki da Allah, tunda muka yi aure wacce kalar soyayya ce ba na yi miki?" Cikin kukan ta ce "Ai don ka ga zargin da kake mini ba gaskiya ba ne, bayan haka kuma kana hutawa da ni". Ya rasa ta inda zai bullo wa wannan yarinyar, ya nisa ya ce "Zaman da muka yi na wata biyu har da doriya, ban yi wani abin da kika gamsu son ki nake yi da iyakacin gaskiyata ba? Ko a lokacin da kike ganin ba na tarairayarki, ai kona mini rai kike yi, na ce ba na son ganin ki da dan iskan yaron nan, amma ba ki ji ba, haka na yi ta ha'kuri ba don ina son ki ba za mu yi auren ne?" Ya sake tausasa murya ya ci gaba da fadin, "Saboda Allah indai dama ba wani abu ne a ranki ba, mene ne na dawo da abin da ya wuce, ba haka kawai na fada miki maganar da kika kullace ni a ranki ba, ke kika janyo, ko ba ni da alaka da ke zan yi kishi yanayin da na gan ki, a matsayinki na mace mai daraja". Ya yi shiru yana jin shesshekar kukanta, tana ta ajiyar zuciya tamkar wadda ya yini yana dukanta. "Na roke ki, ki daina kukan nan haka, na yarda ban kyauta ba ki yi hakuri". Ta yi shiru, kamar yadda ya roka din har da gyara kwanciya, da lulluba alamun barci za ta yi, tana sakin ajiyar zuciya, a ranta kuma tana fadin sai kuma rikicin gobe. Ya so su kasance tare, amma saboda tsoron kar ta ci gaba da masa kuka yasa ya kyale ta, ba a jima ba ya ji saukar numfashinta alamun barci ya yi awon gaba da ita. Ya saki gauron numfashi, ya haska fuskarta, da hasken wayarsa ya ga hawaye duk ya bushe a fuskar, kuma wani abin dariya ita da kanta ta boye fuskarta a jikinsa. Tsintar kansa ya yi da gyara mata kwanciyar yadda za ta ji dadin barcin. Ya dawo Masallaci, ya tarar ta dira sabon kuka ga akwati a kan gado sai zuba kaya take yi tamkar mai shirin yin balaguron wata guda. Zama ya yi gefen gadon yana kallon ikon

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});