Chapter 51
Chapter 51
doro cake din da yasa a fridge, yana jin farincikin ruwa da lemon da Mahmoud ya kawo musu na ratsa shi. Da kansa ya dauka ya kai musu, Sumayya sai sannu take masa tare da fadin "Ga yara kuma sai ka dauko da kanka, sannu na gode". Murmushi ya yi tare da cewa, "Ba komai Aunty". Alwala ya yi, ya fito daga waje ya tsaya ya kira Abba ya danka masa sabbin kudi na dubu biyu,"Ku sayi sweet kai da kannenka". Fir Abba kin karba ya yi, tare da cewa "An hana mu karbar kudi Uncle" Dole sai Sa'adah ya kira ya ba ta, ya ce ta ba su. Ta kalle shi bayan Abba ya koma falon ta ce "Fita za ka yi ne? "Masallaci zan je daga nan kuma zan je gida". Bata rai ta yi sosai "Ba dadewa za su yi ba Uncle, so kake na yi ta zama ni kadai? tunda dare ya yi kawai ka bari gobe ka je da wuri". "To" Kawai ya ce ya daga labulen falo ya ce, "Anty Allah ya mayar da ku lafiya, mun gode sosai." Ita ma ta amsa cike da mutuntawa. Daki suka shige, suka bar yaran a falo suna kallo suna fama da cin cake. Jan kunne da nasiha iri-iri Sumayya ta sake yi wa Sa'adah. Ta dauko wata leda a jakarta mai dauke da tambarin Welcare,ta mi'ka mata ta ce ki adana su sosai, likitan ya ce za ki iya shan wannan ba komai. Ganin da Sumayya ta yi Sa'adah ba ta bude ledar ba yasa ta ce "To ki bude mana na nuna miki yadda za ki sha". Kin budewa ta yi, sai Sumayya ce ta bude ta fito da su, daya a cikin wata yar roba yake mai kyau an rubuta Women's Formula. "Kinga wannan na robar Multivitamin ne 100 pieces ne kullum daya za ki sha" Sai wannan ta nuna na kwalin shi ba kullum ba sai ranar da kika so. Ki kula da shi mai tsada ne sosai, daurewa na yi na siyo miki package dinsa, kafin ya kare dai na san za'a dade sosai". Ba tare da ta kalli fuskar Sumayya ba ta ce "Na gane, na gode." Ta mayar da su ledar. ganyin wata takarda a ciki yasa ta janyo ashe recit din kudin ne, ganin yawan kudin da maganin suka lashe musamman na kwalin ya matu'kar ba wa Sa'adah mamaki. Ta fito dana kwalin tana dudduba mene ne special a tare da shi da ya yi wannan darajar haka? "Viagra" Ta furta sunansa a fili, a kunyace ta sake cewa "Na gode sosai Anty". Sumayya ta muskuta ta tsare Sa'adah da kallo mai tsanani sannan ta ce "Ina rokon ki Iyah kar ki jefa kanki a hallakar da MATAN YAU suka jefa kansu na shaye-shayen magunguna barkatai marasa fa'ida da inganci, da sunan mallakar miji. Kar ki yarda da wannan bankaurar wallahi ba a mallakar miji da wannan sai dai ki ta asarar kudaden ki, karshe ki hadu da ciwon da zai raba ki da mijin gaba'daya". Cike da wauta Sa'adah ta ce "Fada mini abin da zan yi na mallake shi kamar yadda kika mallaki mijinki". Dariya sosai Sumayya ta dinga yi har da kwanciya akan gado, lamarin da ya fusata Sa'adah, kawai sai ta fashe da kuka, da kyar Sumayya ta hadiye dariyar ta shiga rarrashinta. "Yanzu mene ne abin kuka Iyah?" "To akan me za ki mini dariya kamar mahaukaciya?". "Tambayar ki ce ta ba ni dariya, amma nutsu ki ji mai zance miki. Mace tana kama mijinta da girki mai da'di, da kuma ba shi kulawa ta musamman a shimfida, da kuma tsaftar jiki da ta muhalli. Amma wadannan kadai, ba zai sa ta mallake shi ba, sai ta yi ha'kuri ta bi ra'ayin sa akan komai, ko da kuwa ita ba hakan take so ba, ya zama ba ta da ra'ayin kanta sai na mijinta, ta iya ladabi da biyayya, ta kiyaye harshenta akansa. Ina tabbatar miki idan kika hada wadannan abubuwan sai kin mallake shi fiye da yadda kike so". Tura baki gaba ta yi tana goge hawayen idonta, ta sake cewa "To idan ina son ya zama mijin ta ce fa?" Mamaki da tsoro ya kama Sumayya, wai wannan yar mitsitsiyar yarinyar auren jiya, ita ce ke son ta mallake miji, bayan mallakar kuma ta mayar da shi mijin ta ce. Wane irin son zuciya ne ya shigo wa matan wannan zamanin haka? Sumayya tsintar kanta ta yi da ri'ko hannun kanwarta ta kalle ta da tarin kauna sannan ta ce, "Abubuwan da na fada su ne za su miki jagora akan komai, sai kuma ki hada da addu'ar Allah ya zaunar da ku lafiya cikin aminci da tausayi. Amma karki yarda da kawayen da za su ba ki maganin mata ko a saki a hanyar zuwa wurin malamai wallahi ba za ki samu yadda kike so ba, ba komai a wannan hanyar sai bata da lalacewa". Ta dan tsahirta kafin ta zarce da fadin "Ki ba shi dama ya zama sarki a gidansa, ke kuma ki zama baiwa kuma bafadiyarsa, duk abin da kika san yana so, ki masa tun kafin ya bu'kata haka nan ki guji abin da baya so kafin ya ankarar da ke, ina tabbatar miki idan kin yin hakan bayan mallakar da za ki masa zai ya zame miki mijin kan ta ce ma, matu'kar yana rayuwa kan tsarin ilimi da shari'a ne. Ga turaren wuta nan Inna ta ce a kawo miki sai dazu suka iso, ni ma na diba na ga masu kyau ne, har da na tsugunno". Ta mike tana fadin, "Kin ga an dade da idar da sallah bari mu tafi". Da za su tafi rungume juna suka yi kuka kowacce ta ke yi tamkar ba za su sake haduwa ba. A dole suka rabu Sumayya na mata fatan zaman lafiya da zuri'a mai albarka. Ba su jima da tafiya ba ta zuba gawayi a kasko ta zuba kalanzir tare da kyasta ashana, ta barshi a tsakar gida, ta share falon inda su Khalifa suka bata. Sannan ta shiga wanka, sai da ta yi sallar Isha, sannan ta duba ta ga wutar ta kama, ta dauko ta zuba turaren. Kan ka ce kwabo gida ya cika da kamshi, sai kallon agogo take yi,har tara na shirin yi bai dawo ba. Daidai lokacin ya dawo, waya ya kira, ta fita ta bude masa, kamar dazu ba mayafi a tare da ita. Suna tafe yana fadin "idan za ki fito ki dinga saka hijab, ban son wani ya hango ki a haka". Ta amsa da tom. Tunda ga tsakar gida yake jin daddadan kamshi, suna shiga falon ya rikota yana cewa "Madalla da Antyn mu, irin wannan kamshi haka". Ita dai ba ta ce komai ba, sai da suka zauna ta ce "Sannu da dawowa" Ya amsa mata cike da walwala. "Shi ne ka tafi ka bar ni ni kadai har tsoro ya fara kamani". Ta fada cike da shagwaba. "Ai kuwa dai gara ki cire tsoro, kin san har sha dayan dare ina kaiwa a shago". Murmushi ta yi kawai ba ta ce komai ba, amma a zuciyarta tana raya ba za ta yarda da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157