Chapter 149
Chapter 149
kuma shine gaskiyar magana, ba zai yiwu kina wulakanta ni tun yanzu ba, sannan ki yi tunanin zan miki abin da kike so, bakya yarda da ni, na sani ko tariyar aka yi haka zaki cigaba da yi mini, dan haka ki zauna ki haihu a gida. Zuwa lokacin idan kin ji a ranki, kin shirya zama da ni bisa tsarin sharia sai na saka ranar tariyar". Hawaye ya dinga zubo mata ba kakkautawa, a hankali ta ce "kar ka mini haka dan Allah". Nan da nan ko ya ci laya da cewa "Wallahi ba zan yi abin da kike so alhalin har yau din nan bani da mutunci a idonki ba, inace dai jikina ne ba kya so ya rabe ki? To ba zan sake ba, zan ta siyo miki nama da yogurt da duk abin da kike son ci, nima kuma in sha Allah ba zaki ji, ko ki ga na mutu ba adalilin ba kya yarda da ni". Ta dinga kuka sosai, ya dinga jin wani iri, ya sassauta ya ce "daina kukan haka! Ta shi mu tafi" "Ni ba inda zani sai an tsayar da maganar nan". "To ai na gama, sai dai tunda ni zan biki dole, sai ki tsara na ki, ki kuma sa ni biyayyar dole". Ta goge hawayen ta ce "Na yarda ni zan bika". Ya mi'ke ya ce "To tashi mu tafi, tunda Ni na zartar da nawa hukuncin, ba kuma zan canja ba, sai na tabbatar da gaske kin daina mini wulakanci". Da rawar murya ta ce "Ai yanzu ma na yarda! Ba zan sake tureka ba". Da'di ya yi matu'kar kamashi, dama abin da yake so kenan. Da rawar jiki ya isa ya rungumeta. Ya dinga jifa da Hijabinta da komai ma, haka ya dauki lokaci yana abin da ya ga dama da ita. Yayin da itakuma ta ke share hawaye. Har ya yi wanka ya fito bata bar kuka irin na sharbe ba. Ya waske ya yi kamar bai gani ba. Suna tafe a mota da rawar murya ta ce "Yanzu yaushe ne tariyar?" A gajarce ya ce "sai kin daina mini kukan da babu dalili, sai na gamsu da gaske idan kin tare din zaki barni na dinga samu nutsuwa da ke". Da kuka ta ce "kawai na gane yawo kake mini da hankali! Dan kasan ka gama da ni, inace yanzun ba abin da baka yi da ni ba, amma yanzu kana wata magana". "Tabbas na yi, amma mai na tsinta ban da bacin rai, dame kika taimake ni? inace zama kika yi tamkar ruwa, sannan kina ta Kuka". A matu'kar gajiye ta ce "To ai ba zan sake yi maka kukan ba". "To zame mini tamkar gawa fa?" Da sauri ta ce "Na daina". "To ki bari sai na tabbatar da gaske kin daina din har zuciyarki". Cikin kwantar da murya ta ce "yaushe to zaka tabbatar din?" Ya dauke kai ya ce mu barshi nan da wata daya, idan yanayin biyayyar da kike mini ya gamsar da ni, shikenan sai ki tare abin ki". Da rawar murya ta ce "idan na kara wata Innah zata gane halin da nake ciki". "To wai ke wannan boye boyen da kike yi na menene? Abin kunya ne, Inace an daura auren?" "Ni dai bana so a sani ne kawai". Ya murmusa ya ce "ai dole ki ji kunya, kin gama fadin ba kya sona a gabansu, sai gashi daga dan ta'ba ki ka'dan, kin yi ciki, ai dole ki ji kunya, ina kika kai 'kiyayyar?" Ta kasa bashi amsa. To mu barshi sati biyu nan gaba, amma sai na tabbatar fah". Tunda ga wannan ranar Mk ya mayar da Sa'a tamkar ya tare da ita ne, domin kullum sai ya fita da ita, ya yi abin da zai yi sannan su dawo. Har satin biyun ta cika amma baice komai ba, a lokacin cikinta yana shirin shiga wata na uku. Rannan suna gidan da suke yini, zuwansu kenan, ta kalle shi, ta ce na gane so kake dai sai na kunyata dole. Banda haka menene bana yi maka Kullum sai ka fita da ni, amma ka dage akan bana yi maka yadda kake so? Fa'da mini me zan yi maka kuma?" Cikin rashin damuwa ya ce "ba Kya mayar mini da martani kamar da can, sannan kullum na kusance ki da kuka ake karewa, ke yarinyace? Sannan ba har zuciyarki kike amincewa ba, kina yarda ne akan dole, sai dan kina son ki tare kar agane kina da ciki. Abin da baki gane ba, ni ba abin kunya na yi ba, tunda na yi hakuri sai da aka 'daura aure, ke kika ce ba zaki tare ba da bakin ki. Babana ya goya miki baya, yanzu kuma sai ki dame ni da maganar tariya alhalin kin san inda zaki fa'di kin matsu ki tare, asa ni dole, ko bana so". Ya nisa ya ce "ki kira Baba da bakinki kice zaki tare". Idonta ya ciko da kwalla ta ce "Kaine zaka kira ka ce ka shawo kaina na amince, idan ya nemi jin ta bakina sai na yi shiru alamun kunya, shikenan sai ya gane ina bu'katar tarewar da gaske". Ya tsura mata ido ya murmusa ya ce "Sannu Sa'adah! Ke idan kina son abu, kin iya shirya zance". Daga haka ya janyota jikinsa yana kissing dinta. Sai dai yau yana kammalawa ta dinga kelaya amai tana kuka. Sosai ta yi, sai da ta kammala ta koma gefe ta cigaba da kukanta. Haka Mk ya kwashe Aman nan, ya sa tissue ya goge. Ya kalleta ya ce "je ki yi wanka". Bata Musa ba ta mike ta shiga toilet. Ta fito ta same shi ya yi tagumi da hannuwa biyu. Ta zauna a sanyaye. Ya kalleta ya ce "Anya kuwa Sa'adatu kina jin tsoron ubangiji? Anya kuwa baki kafirta ba?" Da saurinta ta dago ya ce "kwarai kuwa! Na sani kishi ne yake son halaka ki! Amma ki sani ubangiji ne ya halasta, sannan shine ya bada umarnin a auri bibbiyu ko uku ko hudu. Aaya ce sukutum cikin al'kura'ani mai girma. 'Kin amincewa da hukuncin Allah kuwa tamkar ka kafirta ne". Ya yi shiru yana nazarinta. Ya nisa ya cigaba da cewa "ina jiye miki kada ki halaka kanki, ki halaka ni, Ina jiye miki tsoron kada na samu aljannah adalilin ba'kin cikin da kike ta 'kunsa mini, ke kuma ki tsince kanki a wuta. Annabi ya ce akwai mazan da suke rabauta da aljannah adalilin hakuri da taurin kan matayensu da kaifin harshensu. Ina jiye miki na shiga aljannah, na hadu da Farida ba da ke ba". Dai-dai nan ta rushe da wani irin kuka, fiye da kukan da ta yi ranar da ya saketa. Da sauri ya matso ya rungumeta, domin ya tabbatar wannan kukan ba na shagwaba ko iyashege bane, na tsantsar damuwa ne. Bai hanata ba, ya barta ta yi, iya yinta, ganin yana neman wuce ka'ida ya sanya ya fara lallashinta da gwalagwalan kalmomin da suke nuna kololuwar matsayinta a zuciyarsa. Cikin kukan ta ce "Me yasa sai ita zaka aura? Me yasa na shafe shekaru hudu, Ina binka ka mini afuwa ka 'ki, karshe sai ka hukunta ni da auren
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157