Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 113

Chapter 113

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin shekaru uku da aure, Mk na iyakacin kokarinsa wurin kwantar mata da hankali ya na tabbatar mata zai cigaba da sonta ko bata haihu ba. Amma deep inside his heart ba abin da yake so irin yaga an masa haihuwa, ya matsu ya samarwa Jawad gishirin duniya. Watan Mk uku da dawowa Jami'ar ta yi bikin karrama shi, tare da bashi mukamin Dr! Sannan ya zama shine H.O.D na English department. Wanda shine mafi karancin shekarun da ya taba zama Head of Department. A wannan lokacin kuma mahaifin Farida ya bashi dan'kareren guda a Rijiyar Zaki, a matsayin kyautar karramawarsa ya taya shi murnar kammala karatunsa. Gida ne mai kyau, mai dauke da bangare biyu, matu'ka da gaske gidan Flat ne amma ya tsaru kwarai da gaske. Har Jawad ya shekara Sa'adah bata ta'ba zuwa masa ziyara ranar visiting din ba adalilin tana gujewa haduwarta da Mukhtar. Sai dai Sumaayya da Inna su je, haka Farida da Mk da Hajiya duk suna zuwa. Sai visiting din karshe wadda suka hadu da Mk har zuwa ranar da Mahmoud ya je gurinta da neman sulhu da irin bijirewar da Innah ta yi akan maganarta da Mk. *'karshen labarin abin da ya faru a Rayuwar Sa'adah da take fatan matan da suke cikin waccan rayuwar da ta yi a baya su hankalta kafin komai ya kubuce musu*. *Surayya Dee* ✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Assalama Alaikum*! *Tsokaci* *Ina jinjina da godiya ga dimbin masu bibiyar wannan labari na *HALIN YAU* ina kuma jin dadin yadda kuke sharhi akan labarin, Allah Ya bar zumunci*. *Bayan haka zan so na yi dan tsokaci game da wata sa'dara a cikin labarin, a shafin baya da na saki. Watau daidai wajen da MK ya tare da Farida a hotel din Tahir na yini daya. Wasu daga cikin masu kokarin bibiyar littafin kullum, sun yi sharhi akan cewa don me MK ba zai bari har sai sun tafi UK ba kamar yadda aka tsara? Me yasa bai yi hakurin ya nuna zumudinsa wanda hakan tamkar cin fuska da tozarci ne ga Sa'adah?* *To abin da nake son na ja hankalin masu bibiyar labarin shi ne, a dabi'a ta namiji wannan ba komai ba ne. Idan har namiji na bukatar abu idonsa rufewa yake ya manta da komai, musamman ma bukatar kwanciyar aure. Abin a halittar maza yake, don haka shi MK bai yi haka da nufin muzantawa ga Sa'adah ba ko kuma jin cewa Farida ta fita. Sai dan a fahimci kaso casa'in da tara da digo Tara na mazan Yau haka suke, domin zasu iya kwanciya da macen da bama sonta suke ba, kawai dan su biya bukatar su ne sabanin da yaje wahalar gaske mace ta sallamawa wadda bata so kanta Akan tana so sai alatilas.* *Watakila tsawon lokacin da ya dauka ne yasa shi gaza hakurin jurewa har sai sun tafi UK din*. *Ina fatan masoya Iyah za su fahimci MK kuma su yi masa uzuri.* *Wasalam*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 91-92. *Barkan mu da Dawowa* *Asalin labarin*. Kwana Sa'a ta yi tana juyi, Abu goma da ashirin sun cakude mata, na farko idan ta ce bata son Mk ta yi karya, duk yadda take jin haushin sa, da jin bacin rai akan lamarinsa, bai hana ta ji wani irin murna da farin-cikin dawowarsa ba. na biyu kuma bata jin a karan kanta zata saurare shi har sai ya janye kalamansa, sannan kishin auren Farida da ya yi yana matu'kar kassara tunaninta, yana gushe dukkan farin cikin da take ciki, haka nan yana sanya mata jin haushinsa marar misaltuwa, sannan ya sababa mata jarumtar da zata iya yin fito na fito da shi. Sai kuma fargabar yadda Inna ta zafafa lamarin ta da shi. Haka gari ya waye ta tashi da idanuwanta a kumbure ga ciwon kai tabbacin babu isasshen barci a tare da ita. Tana tsakar gida tana brush ta dinga jiyo sautin wayarta, bata wani damu ba tana raya koma waye ya sake kira. Maimakon ta shiga dakinta, dakin Innarta ta shige ta sameta ta idar da sallar walaha. Ta sake gaisheta tunda sun riga sun gaisa tun asuba. Ta zuba mata ido ta ce "Iyah wani Mafarki na yi da ya tayar mini da hankali, amma zan bishi da sadaka da kuma addu'a domin ba abin da sadaka bata wanke shi, kema ki tsananta addu'a ki kuma fita harkar Muutar tun baku sake jefa mana ba'kin cikin da ya zarta wadda muka shiga a baya ba". A sanyaye Sa'adah ta ce "wani abin kika gani ne marar Da'di Innah?" Da sauri Inna ta ce "ai idan akace marar da'di da sauki, abin da na gani muninsa ya zarce hankali, abin a nemi tsari ne, ba a kanmu kawai ba, akan kowanne musulmi ma, Malamin islamiyarmu ya ce ba kyu fa'dar Mafarki marar kyau domin duk yadda aka fassara maka shi haka zai zo maka, dan haka zan kame bakina , na bishi da istigifari da sadaka, ina sake jan kunnenki ki sake nesanta kan ki da Muutar". A tsorace Sa'a ta ce "To Inna zan kiyaye in sha Allah, ashana zaki bani, ta kicin din na jefata a ruwa ban lura ba". Ta karba ta fita, tana Kissimmee kissimmen mafarkin Inna da dukkan alama ita da Mk ya shafa. Haka ta yini sukuku har yamma, Innar ma haka take ba kuzari adalilin mafarkin da ya mata tsaye a zuci, domin ta san da wahalar gaske ta yi Mafarki amma idan ta yi, ta kuma tashi da abin a kanta ma'ana bata manta ba, to kuwa lah shakka sai abin ya faru ko da ba kwabo da kwabo ba. Amma kaso sittin sai ya zama reality. Mafarki ta yi wai Muutar na ta bin Sa'a da gudu, suna ta tseren, so yake ya kamota amma tana ta zille masa ga wani abu Abu a nade a hannunsa, sun ci gudu, har Sa'a ta gajiya ta zube a kasa tana haki ya karaso, da gudu ya jefa mata abin da yake ta faman kankame shi, tamkar 'kwai. Da kuka Sa'adah ta bude ashe jariri ne, maimakon ta ga Sa'adah ta mayar masa da abinsa, sai kawai ta ga ta hau shayar da shi, cikin zafin nama ta nufi Sa'a, tana zuwa tasa hannu da nufin fisge yaron sai kawai ji ta yi an tureta da wani irin karfin da ya zarta na bil'adama, ta sake yun'kurin sake kwace yaron, aka sake turata cikin wani irin rami. Da wata irin murya ta ji ance "Zaki iya mutuwa akan wannan yaron, domin 'dansu ne, ke ce shamakin zuwansa duniya, to kuwa zai zo, idan baki yi Sa'a bama a dakinki zasu yi cikin su haifar miki shi a matsayin shege". Da kyar Inna ta fito a cikin ramin nan bayan ta kukkuje kafafuwanta, dai dai lokacin Kuma ta farka adalilin Kiran

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});