Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Mall wanda a lokacin aka bude shi, suka kashe kudin nan tas a wurin siyan kayan kwalliya, da takalmi da jaka. daga Country Mall suka rabu kowa ya yi gidansu, Sa'adah zuciyarta sai wasiwasi take yi mai za ta cewa Inna akan wadannan kayan? Ta tabbatar uwarta ba sakaryar uwa ba ce! Duk wani motsinta akan idonta ne, wa za ta ce ya ba ta wadannan kayan? A ina ta zubar da nasihar da kullum take yi mata idan za ta fita na kar ta tsaya da saurayi a hanya, ko dazu kafin ta fita sai da ta jaddada mata duk mai son ta ya zo gidansu ya same ta, kar ta yarda a tsayar da ita a hanya. Ta gama tunaninta kaf ba ta sami kalaman da zai shiga zuciyar mahaifiyarta, ta fahimce ta ba, don haka kai tsaye gidan su Zainab ta sauka, ta ba ta ajiyar kayan tare da ce mata khalil ne ya ba ta, ba ta son a gani a gida, don ta san idan ta fada wa Zainab gaskiyar magana sai ta iya zuwa ta fada wa Inna tunda ta tsani abotarsu da Halima, kullum sai tace mata, "Sa'adah ki kiyayi kawance da Halima Mu'az ba wayewarku daya ba, ba kuma irin tarbiyarku daya ba" Da kyar Zainab ta karbi kayan bayan ta gama mata mitar ita a rayuwa ba ta son shiga shirgin rashin gaskiya, ban da rashin gaskiya ina ke ina sauraran wasu mazan tunda dai kin san namiji daya za ki aura! Kuma kin tsayar da wanda kika aminta da shi. Sa'adah da yake mafita ta ke nema sai ta yi mukus ta kasa tanka wa Zainab tamkar ba ita ce mafadaciyar nan ba. Tana isa gida ta tarar da Baffa ya dawo daga Gogel, ta yi farincikin dawowarsa amma a gefe takaicin yadda za a ci gaba da yin tuwo ba kakkautawa take yi. A kwanakin da baya nan hilatar Inna ta ke yi ba sa yin tuwo amma yanzu kam ba hilar da za ta mata ta yarda, tunda tafi girmama ra'ayin Baffa fiye da komai, sannan kuma ba za ta bari ta yi nata girkin ba, ce mata ta ke yi nan ba gidanki ba ne, ki bari idan kin yi naki gidan sai ki yi yadda kike so. Kallo daya Inna ta mata ta gano rashin gaskiya a tare da ita, ba ta mata magana ba, sai da ta gama da hidimar Baffa ya fita waje. Sannan ta iske ta a daki tana game a waya, ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta ta ce, "Iya na ga sauyi a tare da ke mai kike ciki ne da har ban cancanci na sani ba?" Duk da yadda Sa'adah ta maze akan ita ba komai, bai gamsar da Innar ba, amma sai ta ce, shike nan Iyah! Ki sani tun kafin ki san kanki na san ki, tun kafin ki yi dabarar boye mini halin da ki ke ciki nake tattalin ki, don haka komai za ki yi, zan gane. Ki sani idan har mu ba mu san mai kika yi ba, Ubangiji ya sani! Shi ne kuma zai kama ki saboda ha'intar da kike kokarin yi Mana." Ta fada tana kallon ta irin kallon nan mai tsanani. Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai musamman kallon da uwar take mata mai kama da ban yarda da ke ba, sai ta ce, "Ni fa Inna ban je ko ina ba." "Iyah ai ban ce kin je wani gun ba amma fada mini ina kuka biya daga asibitin sannan bayan Zainab da wa ku ka hadu a tafiyar?" "Yan makarantar mu ne kawai Inna" "To wa ye kuma ya ce yana son Zainab?" "Babu!" Ta sake ri'ko hannun ta sosai sannan ta ce "Waye ya tsayar da Iyah?" Kai tsaye ta ce "Kai Inna ni fa ban kula shi ba, wani mutum ne tsoho ne fa!" "To tsohon ba namiji ba ne?" Idan har nagari ne kuma kina son sa ai magana ta kare! Ba za mu miki dole ba, don haka ko waye ya tsayar da ke idan kin ga ya miki ki turo shi wurin mahaifinki, laifin da za ki mana shine ki yaudare mu, ki yi abin da kika san ba za ki iya yi akan idon mu ba, ina abin da ya ba ki?" Dariya ta kwace wa Sa'a ta ce " Ban karba ba Inna" Ita ma Innar dariyar ta yi tare da cewa "Ban yarda ba Iyah! Na san ki da martaba kalmar nan ta ba kyau mayar da hannun kyauta baya, amma na san Iyah ba za ta boye mini duk wata kyauta da za ta samu ba. Don ta san ba zan ki ta da alheri ba, sai dai na kiyaye ta daga fada wa hatsarin MAZAN YAU musamman da ba gidansu aka biyo ta ba." Tana fadin haka sai ta mike ta fice ta bar Sa'adah da sanyin jiki da kunya iri-iri suna saukar mata a lokaci guda. A ranta kuma fadi take, "Ko yara nawa ne irinta suka dace da samun tsayayyiyar uwa mai sa ido akan duk wani motsin 'ya'yanta?" A fili kuma ta furta "Madalla da uwa irin Inna!" Tana Jin komai za ta yi In Sha Allah ba za ta tozarta tarbiyar da Inna ke yi a kanta ba gajiyawa ba, amma kuma ba ta jin, za ta ki karbar duk wata kyauta da za a mata kawai dai boyewa ne ba za ta sake yi ba. don haka da kanta ta fada wa Alhaji Mamman gaskiya cewa gidansu na gaba kadan da wancan da ta fada masa da farko, haka nan hatta Khalil ta ba shi damar zuwa, ta gaji da boye-boye tunda wanda take yi domin sa ba fin su son ta ya yi ba, ita ce dai tafi son sa. Yawan wayar da Alhaji Mamman yake mata ba kakkautawa, sau tari ma gajiya take yi da amsa kiran nasa, ya sake sa ta raina kulawar MK, tunda dai yanzu ai ta gama karatun tunda ada uzurin kar ya raba mata hankali a karatu ya gabatar. Amma har yau ya ki canjawa idan ya kira ta da safe ba zai kara kira ba sai da daddaare shi ma a ya dade su yi maganar mintina uku, sabanin Khalil da Alhaji Mamman sai su shafe fin awa akan waya suna neman saye zuciyarta tamkar ba kati suke sawa ba. Tana yawan tambayar kanta shin Uncle MK soyayya ne bai iya ba, ko kuwa matsayinta ne a zuciyarsa bai kai ya mata yadda su Khalil ke mata ba? Zuwan ma bai canja ba sau daya a sati, duk da kullum sai ya zo unguwar, sannan ba ya mata kyautar bajinta kololuwar kyautar sa dubu biyu, sai dai karshen wata ya kan hado mata shopping din kayan kwalliya masu matsakaicin kudi da tarkacen alawowi masu dadi da biscuit, wanda ba sa dadata da kasa saboda yadda Alhaji Mamman da khalil mai sato kudin iyayensa suke mata barin kudi. Wani zuwa da Alhaji Mamman ya yi ya fa'da mata matansa biyu, da yara bakwai, bai boye mata shi dan majalisar jaha ba ne mai wakiltar karamar hukumar Gezawa, uwargidansa na can Gezawa yayin da amarya ke nan cikin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});