Chapter 108
Chapter 108
kaza mana, amma yau duk sun yi likimo tabbacin sun watsa shi a kwandon shara.p A sanyaye sosai ya bar gidan. Washagari kuwa ya bi jirgin Mangal air zuwa Lagos daga can ya shiga jirgin arik air zuwa kasar Birtaniya. Haka Sa'adah ta cigaba da jinyar zuciyarta, tana samun karfin guiwa wurin mahaifanta da Sumayya, domin Baffah da ya ga sun hade masa kai a gidan dole ya ajiye powaer sa ta maigida ya lallashe su da kalmomi masu laushi, da kuma sanin muhimmancin hakuri. Ya sake fa'da musu ba su fi shi takaicin auren Mukhtar ba, amma tunda shari'a bata hana shi ba, akan me shi zai kullace shi? Ya rufe da cewa "kuna ganin laifina dan ban roki Mutari ya zauna da ke akan dole ba, alakawari na yi ba zan bada auren 'yata ba sai a inda nasan za ta yi daraja, a farko da yake so ai na bashi, idan kum zaki fadi gaskiya ai ya ri'ke ki da daraja! a yanzu kuma, da baya so, bashi da abin da zan kalla da zan nemi ya zauna da ke akan tilas, hakuri wuya ne da shi, idan aka daure sannu a hankali za'a cimma buri". Ya nisa ya sake 'daure su da cewa "A zatona Salamatu, da ke da yaran da kika haifa mini da kuma duk abin da kuka mallaka zan yi iko da ku kai tsaye, ba tare da jin shakku ko fargaba ba, amma tunda laifine dan na yi ikon da abin da yake mallakin Iyah ne to ku mini afuwa, Iyah ta bini bashi in sha Allah zan biya a hankali" Kunyar kalamansa suka kama su mussaman Innah da ta bari hankalinta ya kwace akan wannan lamarin. A ranta ta dinga fa'din babbar jarrabawar da aka yiwa mata kishi ne, domin da yawa Mata sun halaka adalilin kishi, da yawa sun rasa Imani, ubangiji ka tsare mu ka sau'ka'ka mana. Hakuri suka bashi, Innah ta ce "Ba siyar da filin bane ya ta'ba ni ba, yadda ka shiga cikin lamarin auren ka yi kane kane ne ya kidima ni, amma ka mini afuwa wallahi ban taba jin bin da ya dama mini lissafi irin halin da na ga Iyah a ciki ba, amma Alhamdulillah komai ai ya wuce ina rokon kar Allah ya sake maimata mana wannan wakiar". Sa'adah ta nisa ta ce " Dayan filin ma na barka maka Baffa tsakani da Allah bana so, tunda na mallakesu ne adalilin Mukhtar. Kawai so nake ka daina nunawa ya fini a gurin ka, sannan ka mini afuwa akan komai ka daina fushi da ni, domin a yanzu Ni Mukhtar ya zalunta". Ya yi murmushi ya ce " ko Sumayya ba ta fiki ba Iyata, amma ina son ki gane gaskiya ko kuna tare da Mutari ba zan 'ki shiga hidimar auren sa ba, domin ya mini alkairori daban daban da bazan mance su ba, duk girman kuskure kuwa bai kamata Dan adam ya shafawa idonsa toka ya mance alheri ba, nasani hukuncin da ya dauka akan ki ya yi tsauri da yawa, adalcin da nake yi masa shine ban san mai kika yi masa ba, sannan auren da yayi ba zaluntarki ya yi ba, domin kuwa ko kuna tare zai yi aure shari'a ta bashi dama, idan yana so kuma zai iya adalci. Fatana ki kwantar da hankalin, ki yi hakuri in sha Allah komai zai daidaita miki, Na da'de da ya yafe miki Iyah, fatana ki bu'de zuciyarki ki fuskanci goben ki, sai kinyi nazari hadi da tsinkaye masu zurfi sannan gobenki zata inganta, na yarda da nutsuwar ki a yanzu, na kuma gamsu a kame kike dan haka bana fargabar zamanki! Amma ba ina nufin kita zama a hakan bane, ki bawa masu sonki kofar da za su tunkare ki, domin a hakan kika samu Mutari, yanzu kuma da kika barwa Allah ya miki zabi, ina da yakinin ba zai barki haka ba". Jikinsu ya sake yin sanyi, suna gasgata maganganunsa, mussaman Sa'adah da take jin karfin zuciya na dirar mata, tana hango ya kamata ta budewa kanta kofofin farin-ciki, zata dawo da kwalliyar da ta da'de da daina yi, sannan zata sake dagewa a makaranta domin a yanzu da Mukhtar ya auri Farida sai take ganin tamkar ya raina arzikinsu ne. *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 16/06. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji ta'ba wannan LABARIN ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Gaisuwa da fatan alheri ga* *HADIZA TINAU*. *Ki yi yadda kike so da wannan shafin, farar mai farar zuciya, ubangiji ya yi mana abin da bamu yi zati ba na alheri* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 89- 90. Maganganun Baffah sun sake 'karawa Sa'a kwarin guiwar gina sabuwar rayuwar da babu Mk a cikinta. Tana kwance har tsakiyar dare tana nazarin yadda zata koma sabuwar Sa'adah da bata san Mk ba, ta nisa tana hakaito abubawan da zata nema, bata da bu'katar sutura domin tana da su ba adadi tsadaddun gaske, da yawansu ma bata sake waiwaryasu ba. Kayan kwalliya da waya tafi bukata a yanzu, sai hanyar da zata dinga samun ku'di tunda yanzu bata bu'katar na Mukhtar, tasan shima ba zai yi gigin bata ba. Ta sani iyayenta da Sumayya suna iyakar kokarinta amma dai ba zai yiwu ace dukkan lalurarta sai an yi mata ba. Saura kwana uku tafiyar su Jawad, Ahamad ya kawo shi gurin Sa'adah inji Hajiya ya kwana mata biyu, tare da sallama, tunda Mk ya yi aure Hajiya ta shiga cikin wani hali na kunyar Sa'a da iyayen ta, mussaman da Mk ya fada mata Baffan Sa'a ne ya biya masa sadaki, sai ta ji inama ace Hajiya Babbace a raye ita kuma a mace, tasan Hajiyar ta fita juriya da shanye 'bacin rai. Sosai Sa'adah ta samu sau'kin zuciya cikin sati biyu nan, domin ko da ta ji tafiyar da Farida da Jawad za su yi bata wani damu ba, illah ta ji ba da'di, Jawad ne ma ya nemi karya mata zuciya da yawan tambayoyinsa akan me yasa ba zata bisu ba? Da daddare suna kwance kansa na kirjinta yana bata labarin abubuwan da zai siyo mata idan zai dawo. Can ya ce "to kawai Mami mu tafi tare mana, kema ai baki taba hawa jirgi ba". A hankali ta ce "Malam bai ce na je ba, Aunty Amarya ya ce ta je". "Mami idan kin je ai ba zai yi fa'da ba". Cike da soyayyar 'danta ta ce "Ai bai biya mini kudin jirgi ba". Ya yi shiru sai ya ce "Na ji kafin ya tafi ya fa'dawa Hajiya, Baban Antin ya ce shi zai biya kudin tafiyar mu". Zuciyarta'daya ta ce " To ka ga ba ni a tafiya kenan tunda Ni Baffahna bashi da ku'di". Ya yi shiru, can kuma ya kalleta tamkar wadda aka kitsa masa ya nisa! ya ce "Ni zan tara ku'di da yawa na kai ki, har jirgin ma zan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157