Chapter 82
Chapter 82
ya barta tana kukan ita yake yi wa baki da mugun fata?. SURAYYA DAHIRU ✍️✍️ 18/04 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKAWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 75_77 Hannu ta 'dora aka ta dinga kuka,tana fadin "Hasbunallahi wa ni'imal wakil". Har akayi azahar tana zaune inda take, ba abin da tasa a bakinta, duk da ga tiren abincin nan a gabanta, ba idonta kawai ba, hatta fuskar ta kumbura ta aune sosai saboda kuka, ta fada ta yi zuru zuru, ta dinga lissafin adadin rikicinsu, aduk fa'dan da zasu yi ita take janyowa, ta sake tuno adadin alherinsa hatta iyayenta bai huta da yi musu alheri ba, tun kafin ma ya aureta. Ta sake tuna duk laifin da take ganin ya mata cikin biyu ne, ko dai kawai zuciyarta ta raya mata ya Mata kaza a matsayin musgunawa, sai wadda 'kawayenta zasu ce ya yi a makaranta, ko ya mayar da ita Bagidajiya, alhalin ita tasan yadda yake girmamata yake girmama dukkan ra'ayin ta, amma sai tunanin ta ya bace ta biye musu. Ta tuna yadda yake tsananin son su zauna lafiya, su rayu cikin walwala da mutuntata juna, sai gashi yau da bakinsa yana la'antar zaman lafiya, yana fa'din bai yafe mata ba, idan ta zauna lafiya da shi. Idan ta yi wadannan tunaninka sai ta rushe da kuka, tana yi tana cewa "wallahi da gaske na gane gaskiya". 'Kiran sallah ya sa ta tashi, ta yi alwallah ta yi sallah, ruwan Lipton kawai ta sha. Tana zaune har dare! sallah ke tayar da ita, gefe kuma tana tunanin Jawad, da ya nan da ya debe mata kewa, yau kwanansa uku a gidan Samira, tunda suna hutu. Akan idonta ya dawo, kusan a guje ta sha gabansa tana kuka, tana cewa "Dan Allah ka yi ha'kuri, ya girgiza da ganin yadda fuskarta ta koma a yini 'daya kacal, ta so bashi tausayi amma da ya tuna haka take idan tana son abu, da zarar ta samu muradinta kuma za ta sake kirkiro wata matsalar. Ya dubeta ya ce "Ba ki fara kuka ba, sai burina na raba Safina da gararanba a titi ya cika" Ta kalleshi a razane, bai damu ba ya ce "babban burina ta zame mini amarya, na tabbatar zan sami nutsuwa da ita, ki adana hawayenki zuwa wannan lokacin". A gurin ta yi fa'duwar yan bori tana kuka tamkar yarinya har da tirza 'kafa irin yadda Jawad ya ke yi. tsaki ya mata yana fadin "Ba kuka ba ko bubburwa za ki yi bai dame ni ba". Ya shige ya rufe kofarsa. Washagari daga sallar asuba bai dawo gidan ba, hankalin ta ya tashi ba ka'dan ba, ta kalli agogo ta ga har karfe uku ta tabbatar yana shago tunda yau lahadi. Abin duniya ya taru, ya mata yawa, idan ta tuna kalamunsa wai son Safina ya ke yi, sai taji tamkar ta shide, ta tuno yanayin halittar su daya, ko a makaranta ana yawan fadin dirin jikin su shigen iri daya ne, da gaske za ta iya daukan hankalinsa kenan? Hawaye ya sake goce mata, karon farko da ta fara jin tsanar Safina a ranta, tana raya ba zata kuma ganin dariyarta ba, bare ta ga fuskar zama a gidanta Maganar ta mata ciwo fiye da zaton mai zato. Tana zaune ta ji wayarta ta hau kuwwa, da hanzari ta dauka, ganin Hajiyar Bichi ce, tun daga muryarta Hajiyar ta gane ba ta cikin sukuni. "A kwance kike ne Sa'a? na ji muryarki ba walwala". Duk yadda ta ke danne kukan sai da ya subuce mata, hankalin Hajiya ya tashi ta dinga tambayar ta dalili amma ta kasa yin magana, sai kukan kawai. Dai dai lokacin kuma Mk na zaune dakin Hajiya yana cin alalan gwangwani da ya ji lafiyayyen manja da yaji. Ta kashe wayarta ta zubawa Mk ido, tana jin takaicinsa na kamata, a kausashe tace "mai ya hada ka da Sa'a?" A nutse ya ajiye cokalin hannunsa, ya kalleta yace "Me tace na yi mata?" Ranta ya sake baci ta ce " Na tambaye ka, ka amsa mini da tambaya! Na lura da kai, ka mayar da ni shashar uwa, duk sadda ka sami matsala da matarka sai ka tattaro ka dawo da kwanon abincinka wurina saboda ka zubar mini da mutunci a idon yarinya, amma zan gyara". Ya yi sukuri dan yasan gaskiya ta fada, yana yin hakan. A raunane yace "Hajiya ni fa ba abin da ya ha'damu, kinsan kuma yadda nake son 'dan'danon girkinki, dan na yi aure shikenan sai bazan ci ba?". Ido kawai ta kafe shi da shi, tun yana murmushi har ya fara shafa 'keyarsa, yana jin kallon na shiga jikinsa, yana tuna lokutan baya na 'kuruciya, idan Hajiya ta musu irin wannan kallon take suke shiga hankalin su, saboda yadda ya 'kunshi abubuwa da yawa ba sai ta yi magana ba . "Tashi ka kaini gidan, na ji ba'asin kukan da take ta faman yi, wa ya sani ma ko dukan ta ka yi". "Haba Hajiya! Kinsan dai ban samu tarbiyar dukan mace ba, ita kukan banza ne da ita, duk sadda zuciyarta ta raya mata, kuka take yi, da dalili ko babu". "Mahaukaciya ce ai". Jin amsar Hajiya yasa shi yin shiru ya lura ranta a bace yake da shi, ya mi'ke ya dauki waya da mukallin motarsa da ke gefensa ya kalleta ya ce "Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, ina jiran ki a mota". Kozai kozai suka tarar da ita, cikin kwanaki uku kacal gaba'daya ta lalace, karon farko da Hajiya ta ganta kaca kaca, kullum fes zata tarar da ita, haka muhallinta. Hajiya ta ka'du kwarai da yadda ta ganta, da sauri ta isa kusa da ita, ta ri'ke ta, ita kuma ganin ta sami mai rarrashinta yasa ta kwantar da kanta a jikin Hajiyan ta dinga rera kukan tamkar mai wa'ka. Mamaki ya kama Mk! ya coge a bakin kofa yana kallon kukan shagwaba da iskanci a wurin Sa'adah, ta masa laifi, ta kai 'kararsa. Ya na'de hannunsa a 'kirjinsa, yana sauraren 'korafin da ta ke rattabawa Hajiya! "kuskure na masa cikin rashin sani, na yarda na yi laifi, na bashi hakuri tamkar harsena zai tsinke ya ki ha'kura, yanzu kuma sai ya fara soyayya da kawata dan ya ci mini fuska ya kuma janyo mini raini" Cikin kuka sosai take bayanin. Hajiya ta rasa mai za tace! ta fahimci Sa'a ba 'karamin kishi ne da ita ba, kishin nata kuma ya zarce ka'ida, amma da ta lura har da 'kuruciya a kanta, sannan dabi'a ce ta matan YAU sawa miji ido da kuma 'dorawa kai zazzafan kishi tamkar wadda aka musu busharar an janye ayar da ta bawa maza damar auren abin da ya musu da'di, daga mata biyu, uku ko hudu. A hankali ta ce "akan yana da budurwa ki ka maida kanki haka, Ina ruwan ki? ki daina sa ido ko bibiyarsa, ba ruwan ki da abin da yake yi matu'kar bai tauye miki hakkin ki ba, idan kuma ya na 'ketare dokokin shari'a wannan kuma tsakaninsa da ubangijinsa ne". Kan Sa'adah na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157