Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Allah, da Asubar fari za ta fara masifa tamkar jiya ba ta yi ba, duk irin ha'kurin da ya ba ta ashe bakam ta masa. Yana kallon yadda ta gama shirya akwatin ya kasa cewa komai saboda gaba'daya He is speechless. Wanka ya ga ta shiga yana zaune ta fito, ta shirya cikin riga da skirt na English wears, skirt (purple) iya guiwarta rigar kuma body hug (pink) an rubuta *BABY GIRL* ta kama ta ainun musamman daga kirji, ta gyara zaman ribon dinta a kitsonta na shuku, ta masa kyau ba kadan ba, har ya dinga raya don ta tayar masa da hankali ne yasa ta yin wannan shigar da Asubar nan tunda ta san yau ya kwana bai taba ta ba. Ta shafe jikinta da turararuka kala-kala tun daga na jiki har na kaya, sannan ta dora bakar doguwar riga akan kayan ta yane fuskarta da dan mayafin rigar. Ta dauko takalmi da jaka ta saka sannan ta ja akwatin ta nufi kofar barin dakin. Wata irin fizga ya mata ta dawo da baya kamar za ta fadi sai kuma ta dire kan kafafunta. Kafin ta yi magana ya riga ta da cewa "Me kike shirin yi ne haka, ina ce tun jiya magana ta wuce?" Hawaye yana zubar mata ta ce "Wallahi ba ta wuce ba don kuwa ni ba zan sake zama da kai ba". Dariya ce ta subuce masa wadda babu nisha'di ya ce "Ok tunda haka ki ka zaba shike nan, sai na ga wadda zai raba ki da ni". Ta juya za ta sake fita, wannan karon da karfin gaske ya janyo ta ya jefa ta gado tare da fadin "Wannan shi ne gangan, ba za ki fita ko ina ba, bai wani bata lokaci ba ya bita ya turmushe ya sakar mata dukkan nauyinsa. Ta kasa koda kwakkwaran motsi, sai da ya tabbatar ta yi laushi sannan ya daga ta, sai kuka take masa mai sauti bai kula ba, sarrafa ta yake yi kawai, tun tana tirjewa har abin ya shiga jikinta ta yi lakwas ta sallama. Tsawon lokaci kafin ya samu nutsuwa. Sai da ya huta sannan ya tashi ya fita bayan ya zura jallabiyarsa, a shirye ya fito hannunsa ri'ke da mukallin mashin, tana kwance inda ya barta tana kallon sa, ta tura baki gaba ta dauke kai. Murmushi ya yi ya ce "Kin ga kwana uku ke nan ina fita da yunwa amma yau a koshe zan fita, kullum haka zan dinga miki". Harara ta watsa masa tare da cewa "Idan na zauna ba". Murmushi ya yi tare da fadin "Ba inda za ki iya tafiya ki bar ni, wa zai iya da wannan fitinar ta ki ai sai ni din". Ganin magana yake nema yasa ta daina tankawa. "Zan tafi, ki tashi ki yi wanka ki karya, idan na dawo ban tarar da abinci ba, ki tabbatar ke ce abincin." Ya fita yana fadin "Sai na dawo." A fili sharewa ta yi amma a zuciyarta addu'a take masa. Yana barin tsakar gida ya janyo kofar ya rufe ta da kwado ya saka mukallin a dan jikin flowers, ya fitar da mashin dinsa, ya bar kofar gate din ba tare da ya rufe da jamlock ba. Wanka ta sake yi, tana yi tana tsaki, haka kawai an mayar da mutum kamar agwagwa wanka dai wanka dai ba kakkautawa. Ta mayar da kayan da ya cire mata bayan ta shafa mai, doguwar rigar ta ninke ta mayar durowa, sai da ta gyara gidan fes ta share ta goge ko ina. Ta kunna risho ta dora tukunya don dafa indomie, dogon Hijabi ta dauko ta saka, ta dauki kaskon turaren wuta, lekawa za ta yi ta samu yaron da zai samo mata garwashi a gidan Maman Nana, jan duniya kofa ta'ki budewa ga shi kuma ba da mukulli aka rufe ba, kan dole ta ha'kura bayan ta hango kwado ta yar karamar kofa, murmushi ta yi tana fadin "Ya dauka da gaske tafiyar zan yi". Tana karyawa ta yi wanke-wanke, ta dora abincin rana, farar macaroni ta dafa ta fito da miyar kifi daga fridge ta dumama ta bar ta akan rishon, ta juye macaronin a foodflask ta ajiye, ta tsinci kanta da son hada masa zobo, nan da nan ta dafa ta hada ta saka a fridge. Sai da ta gyara kicin din sannan ta tafi ta kwanta, ba ta jima da kwanciyar ba, barci ya yi awon gaba da ita. Bude ido ta yi ta gan shi tsaye a kanta alamun shi ya tashe ta, mi'ka ta yi ta sake juyawa don ta ci gaba da yin barcin. "Ki tashi ki yi sallah biyu fa ta wuce". Kan dole ta tashi don kuwa ba karamin jin dadin barcin ta yi ba, har ta idar yana kishingide a gefen gadon, ya kalle ta ya ce "Kin yi abincin, ko kuwa ke ce abincin?" "Don Allah ka barni na ji da abin da ya dame ni, ina dai rufe ni ka yi, ba ka tunanin faruwar gobara ko wani abu na ibtila'i, ina kulle ba?". Cike da rashin damuwa ya ce "Na fi ki tattalin lafiyar ki, na riga da na yi riga-kafin komai. Ba ki amsa mini tambayar da na yi ba?" Shiru ta yi ta kyale shi, ganin haka ya mike ya na cire rigar shaddar jikinsa, ya cire wandon, ya yi saura daga shi sai Boxer da singileti. Inda take zaune ya nufa ya mikar da ita yana fadin "Taso". Kwacewa ta yi ta fita falo a guje, tana fadin, "Wallahi ba za ka tsofar da ni ba, ga abincin can a kicin". Yana dariya ya biyo ta ya zauna a kujera ya ce "Zubo mana" "Ni na koshi". "To ni zubo mini". Ta fita tana kunkuni ai tun farko shi ne ya'ke zubo musu abinci, sai yau zai ce ita za ta zubo. Haka ta shiryo masa abincin har da zobo, dadi ya kama shi sosai, ya dinga cin abincin hannu baka hannu kwarya, tabbacin tunda ya fita bai sa komai a cikinsa ba. Yana kallon yadda ta zauna a falo ya san ta ki shiga daki ne don kar ya mata wani abu, abin da ba ta sani ba a falon ma ba abin da zai fasa. "Sa'adah! Don Allah mu shirya haka nan, wallahi na gaji da fushinki, ki yi hakuri kin ji na janye wallahi ke kamila ce, mai kirki ce". Ko kallon sa ba ta yi ba, bare ta amsa masa. "Kin ga siyar mini da fushin to". Ta zumbura baki sosai, ta sake yin shiru. "Ki shirya gobe na kai ki, ki yini a wurin Inna, idan za mu dawo sai mu tsaya a Sahad store mu sayo iron din da ki ka ce na sayo miki" Nan ma shiru ta yi. "Kin ji" "Ni wallahi albarka". "Tom shike nan satin sama makaranta za ta tura mu Jami'ar Jos Seminar, ki shirya mu je, ki gaida Anti Sumayya". Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta. Shi ma murmushin ya yi tare da tambayar "Kin sayar?" Kai ta daga tare da cewa "E amma fa har da fitar goben". "Na sani ai, tunda mun shirya, mu je ki taya ni barci, kin san

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});