Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 85

Chapter 85

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

manta da su, ta leka ta ga rigunan Jawad ne da agogon ta, sai kwalin wayar Blackberry, ta jefa kan gado akan sai ta dawo zata san yadda zata yi ta nunawa Mk rigunan, dan ta fara sakawa Jawad tunda tsadaddu ne. Ta dauko wayar daga inda take boyewa, ta jona a caji, ta shirya ta rufe gidan ta fita, zuwa bayan layinsu inda take kitson. Mk da ya fito daga gidan rasuwar gidan Mahmoud suka zarce adalilin motar Mahmoud din ta lalace, dan haka ya kai shi, ai kuwa Jawad ya ce anan zai zauna wurin Dady. Anan ya 'bata lokaci, ganin hadari ya hadu sai ya yanke hukuncin komawa gida ya huta bayan la'asar sai ya je wurin Hajiya. Ya isa gidan, da mukallin hannun sa ya bude gidan, ya shiga, dakinsa ya kwanta sai ya tuna yana son dauko Agogon sa dake dakin Sa'adah da bai dauko ba, kullum sai ya fita yake tunawa. Ya mike ya doshi dakinta, ya duba ya dauko Agogon, har ya kai bakin kofa sai ledar kan gadon ta ja hankalinsa, mussaman da ta kasance ta waje ce, dan haka sai ya koma ya dauko ya bude, ganin kaya ne, ya zazzage su akan gadon, kayan Jawad basu dauki hankalinsa kamar tsadadden agogo da kuma kwalin wayar ba. Zuciyarsa ta dinga bugawa, wani irin tsoro, da razani suka shige shi, shaidan ya kawowa zuciyar sa caffa! kawai sai ya dinga tuno sadda take cewa matan bariki na mallakar duk abin da suke so cikin gaggawa. Innalillahi wa ilaihir raji'un kawai ya ke ambata, ya kalli socket ya hango wayar da bai san da ita ba, ya karasa gurin ya dauko, yana dubawa, ganin Blackberry ce kuma babbar sai hankalinsa ya sake tashi, ya kasa budewa saboda ta sa mata password. Da yake data a kunnen ta ke Ya dinga ganin sakonni na shigowa ba jinkiri. Ya dinga jin jiri na katantanwa da shi, bai taba jin tashin hankali irin na yau ba,me Sa'adah take yi haka? A ranar ya gane duk yadda yake daukarta ta wuce nan. Kusan mintina talatin yana zaune a dakin nata, cikin tashin hankali iri iri. Daidai lokacin ta shigo gidan a sukwane, tunda ta ga motarsa a waje ta shigo a hanzarce, zuciya na 'bari, ba ta yi zaton zai dawo ba, wacce irin 'kaddara tasa ta bar kayan nan da waya a fili? Kai tsaye 'dakinsa ta shiga dan ganin wanne kallo zai mata? Har 'bandaki baya nan, bugun zuciyar ta ya karu, cikin shahada ta nufi ta nufi falon , bata ganshi ba, fargabar ta ta 'karu ta tabbatar ya ga wayar nan. 'Karfin hali ta lalubo ta dora a fuskarta duk kuwa da zuciya da gangar jikinta sun 'ki karban wannan 'karfin halin. Da sallama a bakinta ta shiga dakin, yanayin da ta iske shi, sai da ya ka'da mata 'ya'yan hanji. Bai 'dago ya kalleta ba, amma ya amsa sallamarta da murya marar amo. Ta aro jarumtar 'boye kaduwar da take ciki, ta matsa kusa da shi tana cewa "Ba ka jin dadi ne, da kace sai yamma za ka dawo, a Ina ka baro Jawad?" Ya dago yana kallon ta, yana jin wata irin tsanar ta na neman Samun muhalli a zuciyar sa. Bai amsa mata ba, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya tashi ya yi ta dukanta. marar gaskiya akace ko a ruwa gumi ya ke yi, ta dinga jin 'barin jiki irin na fargaba, ta yi sukuri tamkar ace 'kyat ta fece da gudu. Ya mi'ke ya isa inda take tsaye yace " A Ina kika samo wadannan kayayyaki masu daraja?" Cikin rawar murya tace "Anty Sumayya ta aiko mana, dama na fito da su idan ka dawo, ka gani" Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke shirya zancen da babu azanci a cikinsa, ledar kayan ta nuna daga Egypt kayan suke, sannan a cikin kwalin wayar akwai risit din siyan wayar a ciki mai dauke da sunanta a takaice( S.B). Kwanan watan ya nuna ta kai wattanni biyu a hannun ta. Ya ce "Sumayya yaushe ta je Egypt ban sani ba? Ta hannun wa sa'kon ya same ki?" Ta muzanta kwarai da gaske, ta kasa bude baki ta yi magana. Ya dauko wayar yana cewa "Wannan wayar da ta lashe manyan ku'da'de Sumayya ta aiko miki? Ko kuma saurayin ki, ki ka fa'dawa mijinki ya gaza?" Ya mi'ka mata ya ce "Bu'de mini! tashin hankalin ta ya ninku, Baki na rawa ta ce "kar ka yi aiki da zato, wayar Halima ce ba tawa ba". Idonsa ya canja zuwa jah, jijiyoyin kansa suka bayyana ru'du ru'du, makoshinsa ya bushe, zuciyarsa ta cushe da tsananin bacin rai, hankalin sa ya kai 'kololuwa wurin tashi. "A zafafe sosai ya ce " wacce maganar zan kama, wayar Halimace ko Sumayya ce ta kawo miki? ki bude min wayar nan tun kafin na tozarta ki, domin sai na dauke ki munje gaban Halima, Ina rantse miki da ubangiji agaban Baffa za'a yi komai". Ta fara kuka tana cewa "Ajiya ta kawo mini itama ba tata bace, dan Allah ka yi hakuri, gaskiya na fada maka". Karon farko da hakurinsa ya kwace ya dauke ta wani irin mari mai katse ji da gani na wucin gadi! ya ce "Da aurena Sa'adatu, da aurena akan ki? Idan wayar Halima ce to wannan Agogon da kayan na uwar waye?" Tsananin zafin marin yasa habo ya goce mata, duk da hakan bata damu ba, asalima kukan tsayawa ya yi cak duk da hakan furucinsa ya fi firgita ta sama da marin A gigice ta ce " gaskiya na fada maka, ka yarda da Ni" Ta riga ta kudiri aniyar komai zai mata ba zata bude ba, domin a jiya ma sun yi chart da Khalil, duk da ba wani dirty abubuwa suka tattauna ba, amma akwai maganganun da ba zata so Mk ya gani ba, mussaman hotunan sa da ya turo mata, ita kuma ta tura masa na Jawad. Hankalin Mk ya kai ma'kura wurin tashi ya matsa kusa da ita sosai yace "ki bude min wayar nan idan ba so kike ki wulakanta kanki ba". ta karba, amma ilahirin jikinta rawa yake yi na tsananin tsoro da firgici. Fiye da mintina goma tana ri'ke da waya amma ta 'ki budeta, lamarin da ya sanya Mk ya ce ta fita suje gidan su Halima, ya tasa ta a gaba har tsakar gida, anan ta coge akan ita ba zata je gidansu wata Halima ba. Ya nuna ta da yatsa ya ce "Billahillazi sai kin je, daukota zamu yi, muje gaban Baffa shine al'kalin wannan jahilcin na ki". Ta rasa inda zata tsoma ranta, ta tabbatar Halima kai tsaye za ta ce ba wayarta bace tunda ba ta 'ki ta kashe auren Mk ba dama. Ya koma 'daki dauko mukallin mota, tashin hankali yasa ya kasa ganin inda ya ajiye, yana cikin dube dube kawai sai jin 'karar fashewar abu ya ji da karfin gaske. Ya fito da sauri, ya ga wayar ta rotsa, ta fashe sosai, ta wargaje yadda ba zata tashi ko ta moru ba. Bai san sadda ya isa gareta ba, ya sha'keta sosai, sai da ya lura tana dab da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});