Chapter 145
Chapter 145
iyashege ba. Da ace kin ji rarrashin da na miki, da kin ga yadda zan tarairaye ki, na lallashe ki, amma yanzu ko bubburwa zaki yi ba ruwana da ke, bare na san kina sakalcin banza". Da rawar murya irin tana gaf da fashewa da kuka ta ce "kin yarda da na yi da kai ya isa ka gane sonka ne ba na yi, haka karfin da ka gwada mini, da har yanzu nake Jin ciwo a inda ka bubbbga mini guiwar hannunka ya almata mini kaima sha'awa ta kawai kake yi, amma ba so ba". "Eh bana son ki". Ya bata amsa a ta'kaice. Ba'kin ciki ya turniketa ta ce "Allah ya kawo zazzabi anjima zaka gane lalle nima bana sonka". Ya ma'ke kafada ya ce "Ameen! Ciwo na kan kowa, nawa ya yi kyau ai. Kema kuma na ki na tafe, domin ciwo ai ba a fatansa, idan yau kaine, gobe na ga waninka. Idan ubangiji ya juya abin ya dawo kanki, a lokacin zaki gane tsiyar ki ka'dan ce". Ya mike ya na cewa "To ni kam dama kwanaki uku iyalina ta san zan yi. Yau kam ko hayar direban da zai tuka ni zuwa Kano, zan yi, bare kuma Ina fatan ubangiji ya bani ikon tukin da kaina. Don bana cikin mutane masu yiwa masoyansu 'karya ko butulci, ko danne musu hakkin su". Zuciyarta ta buga da tsananin gaske, ta san shagube ya yi mata, sannan kai tsaye yake nuna mata yau gurin Farida zai kwana, domin kwana ukun da ta bashi ya cika. Haka suka dawo Kano, ba wani jituwa a tsakanin su. Ya sauketa a kofar gidansu ya ja motarsa ya yi gaba. Tunda ya ajiyeta yake jin tamkar ya rusa ihu, shi dai ko zasu kwana suna Yar tsama yafi son ya ganta a kusa da shi, ko da ba zata kula shi ba, haka nan shima ko ba zai mata maganar ba, amma dai ya ganta kusa da shi shine samun nutsuwarsa, ko shareta da yake yi, Karfin hali kawai yake yi da son kwatar kansa a hannunta, tunda ya san halin iyashegenta. *Bayan sati biyu* Tunda Suka dawo kullum Mk sai ya Kira Sa'a a waya, sau tari bata dauka, ranar da ta yi niyya ta dauka, to kuwa zai ta yi mata magana ne, sai ta yi kamar bata ji shi ba. Bai yi fishi ba, a hakan dai yake 'kiranta, zuwa ne dai ba ya yi. Wani lokacin ma zai je shagon Baffah su sha hirarsu, amma ba ya neman Sa'a. Suna cikin haka tafiya ta same shi zuwa jahar Akwa-ibom. Zasu yi wani bincike a Jami'ar jahar na tsawon wata 'daya. Ya gama lissafinsa ba zai yiwu ta tafi da Farida ba, domin aikinta ba irin wadda za'a yi masa shan ruwan tsuntsaye bane. A zuciyarsa yafi dokin tafiya da Sa'a tunda dai har yau bata bashi dama ba, ko waccan ma, da tsiya tsiya aka yi, shikuma so yake, ayi da yardarta da amincewarta, ta yadda zata shayar da shi kalololin soyayyarta masu gigita shi. Saura kwanaki biyu ya yi tafiyar ya iske Sa'adah a gidan Sumayya. Suna zaune a falon mai gidan. Ya sassauta murya ya ce "Tafiya ce ta same ni, zuwa south, shine nake son ki yi mini rakiya, zan jima domin zan shafe akallah wata guda". Ta girgiza kai ta re da cewa "ba inda zani". "Umarni fa na baki". "Gaskiya ba zanje ba, tunda dai ban tare ba, umarninka baya kaina, ka je ka tafi da wadda idan ka yi tafiya baka wuce adadin kwanakin daka fa'da mata zaka yi, saboda sonta da isar da ta yi. Ya numfasa tare da mikewa yana cewa "na gode sosai da wannan shawarar, ya ajiye mata kudi masu auki, ga su nan ko wani uzzirin zai taso miki, sai na dawo". Har ya kai bakin kofa, sai kuma ya juyo, ya kalleta ya ce "zuwa yaushe kika shirya tarewar?" Kai tsaye ta ce "idan abin da nake so ya samu nan da wattanni hudu". Ba'kin ciki ya kama shi, amma sai ya yi nufin su raba bacin ran tare ya ce "To kawai a barshi a rabin shekara mana, wattanni shida kenan"! "To kawai mu bar shi a shekarar kawai". Ta fa'da a kufule sosai. Ya yi tafiyarsa ba tare da ya sake cewa uffan ba". Sai itace tana ganin fitarsa ta fashe da kuka sosai, tana gasgata da gaske ne yafi son Farida akanta. Mk yana tuki amma a fili yake cewa " Ubangi ka mallaka mini zuciyar Sa'adatu da tunaninta, Allah ba zan iya ba, kaine mai sarrafa zukatan bayinka, Allah ka hore mini wannan yarinyar da take neman manna mini hauka, bayan hawan jinin da nake fama da shi adalilinta! Kai ka jarrabi zuciyata akanta, ubangiji kar ka jarrabe ni a cikin hankalina da tunanina akan sha'aninta". Haka ya tafi Uyo shi ka'dai tamkar ba mai mata biyu ba, amma a kullum yana ro'kon ubangiji akan a mallaka masa tunaninta tamkar yadda aka mallaka masa zuciyarta, hakanan duk sallar duniya sai ya roki Ubangiji akan a sassautawa Sa'adah kishin dake neman jefasu yanayin da yake tunanin sun yi bankwana da shi. Satinsa biyu da tafiya Wanda ya yi dai dai da watansu daya da dawowa daga Sokoto. Sa'a ta kasa gane kanta, bata ciwon komai, amma yini take tana zubar da miyau, da ta gaji sai take fama da alawowi ko cingum, ko kuma kaninfari. Matu'kar kuwa ba komai a bakinta to kuwa miyau zai cika mata shi. Ga 'dan karen barci. Da kanta ta yiwa kanta alkalanci tabbas ciki ne da ita, domin tana iya hakaito haka cikin Jawad ya yi mata. Duk da yadda ta gamsu tana da ciki sai da ta yiwa kanta gwaji da P.T strip, sakamakon kuwa ya kasance positive. Wani irin tashin hankali ya dinga ziyaryarta, ita kuwa da wanne ido zata kalli Innah da kuma Anty Sumayya?. Da wanne irin harshen zata musu bayanin da zasu gamsu, sau 'daya tak wani abu ya gitta a tsakanin ta da Mk, shima kuma ba da sonta da yardarta ba, fin karfi ya gwada mata. Mk ya shammaceta kwarai da gaske, gashi yanzu ya dawo da asalin halayyarsa ta bagarar da ita da lamarinta. Ta nisa tana tunanin hanyar da zata bi ta boyewa Innah halin da take ciki. Ta shafa cikin tana Jin wata irin zazzafar soyyaarsa na huda dukkan sassan jikinta. Cikin Jawad ta same shi cikin kuruciya, da kuma sa Rai za'a samu tunda tana ganin da anyi aure ake samun ciki a haihu. Cikin kanwarsa kuma bai zo mata a sadda take so ba, asalima unwanted pregnancy ne, sai dai bayan ta haifeta ta dora ido akanta aka dora mata sonta fiye da tsammani, a yanzu da hankali ya shigeta ta tabbata tana jin son cikin jikinta kwatankwacin yadda take jin son Jawad. Shine kuma cikin da ta yi 'mararin samuwarsa duk da bai zo a lokacin da ya kamata ba. Washagari ta nufi asibiti, aka yi mata gwaji na sosai, sakamakon dai 'dayane da wadda ta yi da kanta. Ta dawo gida tana ayyana lissafin zuwanta Sokoto, lissafin cikinta wanda yana shirin shiga sati na biyar. A yanzu ba abin da take so
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157