Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ka samo mini wata makarantar." "E na fadi hakan! €amma nima sai da nace idan na ji kina da dalili, to ban gamsu da wannan dalilin ba." Ta yi 'kasa da kanta,"Ai dama na san ba zaka mini adalci ba, tunda abin ya shafe ta." Ido ya zuba matat kamar kishi take da Farida, amma kuma ai shi ba wacce ya ce yana so a cikinsu, daga Ubangiji sai shi sai zuciyarshi su kasan me yake ciki. "Wai ta ina ta zama Bebina?" Da sauri ta ce, "Saboda kullum bakinka baya gajiya da ambaton ta, duk fadin makarantar nan da ita kake misali, alhalin ba ita ce kawai daliba mai 'kwazo ba, sannan za ta tsokane ni, amma har da kai a masu gaskata ta, ni kuma a 'karyata ni" Ta fada cike da takaici kwarai da gaske. Ya nisa, "To ai nace ba zan sake shiga case din ki ba" Ya sake sassauta murya ya ce "Sa'adah!" Har cikin jikinta sai da 'kiran ya ratsa, jikinta ya yi sanyi, ya sake kiran a karo na biyu. "Sa'adah!" Ba ta amsa ba amma ta dago ta zuba mishi manyan idanuwanta da sukayi ja saboda kuka. "Idan na ce ke ce Bebin nawa fa?" Da sauri ta yi 'kasa da kanta saboda yadda maganar ta dirar mata a ba zata! kuma yanayin sa ya matu'kar sa kunya ta kama ta. "Ki dago ki amsa mini." Ya fada murya ba amo. Ganin ta kasa magana, ya fara gaskata zarginsa na ita ma tana son sa, ya nisa tare da cewa. "Ban so na fada miki sirrin zuciyata yanzu ba, na so sai kin kammala karatunki, sai na zo na nemi aurenki a gidanku, amma ke na lura gaba'daya kallon wani 'dan ta'adda kike mini, idan za ki yarda da ni, ni ba son Farida nake yi ba, amma na san ina tausayin ta, sannan idan ke ba ki amince mini ba, to tabbas zan iya maye gurbinki da ita" Wani takaicin ya sake kama ta akwai alamun tausayin nan zai iya rikidewa zuwa soyayya kamar yadda Zainab Ma'aji ta hasaso, abin da take ayyanawa a ranta ke nan. Ya gaji da jiran amsarta ya ce, "Kin yi shiru?" 'Kasa ta sake yi da kanta cikin fushi ta amsa, "Tunda har za ka iya maye gurbina da ita, kawai ka ri'ke ta tun yanzu ai dama ita ce a ranka." Ta fada murya na rawa. "Wai ke kam wacce irin yarinya ce mai 'karyata na gaba da ita? Kin sa na fada miki sirrin zuciya ta, amma kina 'karyata ni. zan maimata miki a karon 'karshe, ke ce Bebina ba Farida ba, da gaske auren ki nake son yi, don nan ba gidan da zan yi wasa ba ne". Ya mi'ke yana sa takalmi, yana ci gaba da fadin, "Idan kin amince kin kuma gaskata ni, to lallai gobe na gan ki a makaranta, zan kuma fada miki wata magana. Rashin zuwan ki amsa ne na baki amince da soyayya ta ba, ba kuma ki gaskata ni ba, kin ga ba zancen ki ji ma maganar da zamu yi, zan tafi sai yadda hali ya yi ki gaida Inna!" Ya juya ya fice. Alkalamin SURAYYA DAHIRU. ✍🏼✍🏼 [5/26, 20:33] Aminan Ibrahim: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Dan Allah masu son Halin Yau! Daga farko, ku dinga tambaya a group, a kullum nakan turawa mutane daban daban sama da sau goma, nasan soyayyar labarin ne ta kawo hakan, amma abin yana mini yawa mussaman da kullum'kara yin nisa muke yi! Idan anturo ku dinga tarawa, idan antambaya ku yi sharing, yanzu aka fara, labari na gaba, JAZAKUMULLAHI KHAIR.* *Comments din ku na sani nisha'di na gode sosai fans Allah ya fini yabawa* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 29. Ta jima zaune a gun, tana jin wani irin nisha'di tare da shauki yana ratsa zuciyarta da gangar jikinta gaba'daya, tana tuno yadda ya lankwashe murya yana fadin, "Ke ce Bebina ba Farida ba" Cike da farin-ciki ta na'de tabarma ta shiga gida, dakin Inna ta fara shiga ta shaida mata ta dawo sannan ta jigine mata tabarma inda ta dauka. 'Dakinta ta shiga, ta fara tattara uniform din da ba ta wanke su ba, ta fita tsakar gida ta hau wanki, hatta sandal sai da ta wanke ta shanya, tana gamawa ana kiran Maghrib. Koda Inna ta fito ta ga shanyar uniform uffan ba ta ce mata ba. Sai da Baffa ya shigo bayan sallar Isha ta je ta durkusa gabansu, ta shaida musu gobe za ta je makaranta, Inna dai ba ta tanka ba, Baffa ne ya ce, "Allah ya kai mu" Ta dade a tsugunne tana jinta wani iri, ta san fushi suke da ita dukkansu musamman Inna. don haka sai ta sanyaya murya ta ce, "Don Allah ku yi ha'kuri na san ban kyautata muku ba, na yi musu da ku, ku yi mini afuwa" Ta fada cikin muryar kuka, kasancewar Baffa ya fi mata sassauci, shi ne ya fara tankawa da cewa, "Ni ban san inda kika samo dabi'ar yin musu da iyaye ba Iyah? Ni da kaina na rarrashe ki akan wannan maganar kika kafe, kika nuna mini ni ne zan bi ki ba ke za ki bi ni ba". Jikinta ya yi mugun sanyi ta shiga kuka na sosai tana jin kunyar maganganunsa na matu'kar ratsata, musamman yadda komai take so yana kokarin yi mata duk kuwa da wani abin don ya faranta mata yake yi, ba don yana so ko yana da karfin yi ba. Cikin kuka sosai ta ce, "Don Allah ka yi ha'kuri Baffa In Sha Allah ba zan sake ba." Ya nisa ya ce, "Shike nan na yafe miki, amma ki kiyaye, wannan ba dabi'ar kwarai bace, musamman kasancewar ki mace, ko wani daban wanda kika san ya girme miki ya ce miki kar ki yi kaza, ai kin mutunta shi ki bar abin kasancewar ya fi ki hangen nesa, bare kuma ni mahaifinki da ba zan cutar da ke ba ta kowacce fuska". A hankali ta ce, "In Sha Allah zan kiyaye, na gode Allah ya kara lafiya da nisan kwana Baffa". Cike da tarin soyayya mai yawa ya amsa mata da, "Amin Mamana!" Sai kuma ta juya ga Inna da ba ta tsoma musu baki ba ta ce, "Don Allah Inna ke ma ki yi ha'kuri da bacin ran da na saku". "Ni ba ki yi mini komai ba Iyah, amma tabbas inda ta ra'ayina za a bi kin gama yin boko tunda ke naki karatun na raini ne, haka siddan ana wahala da ke rana tsaka ki hau iyashegen ke ba kya son makarantar sai an canja miki, alhalin tun farkon samun wannan makarantar kin san ta fi karfinmu, amma kika kafe sai ita, kina kallon yadda yar'uwarki da mijinta suke 'dawainiya da ke, mu ma muna irin namu kokarin tunda wahalhalun makarantar yawa ne da su, sai kuma don kin raina mu ki ce lallai sai kin bar makarantar kin koma wata saboda ki nuna duk wahalar da ake yi akan makarantar

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});