Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 139

Chapter 139

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ji shiga ba, ta dinga yun'kurin bude baki ta yi magana amma hakan ya gagari Kundila. Ta dinga karanto addu'a, amma duk da hakan sai da hawaye ya goce mata, wani irin tukuki ya mamaye zuciyarta, ta dinga jin tamkar ta mutu ta huta. Da sauri ya janyota jikinsa ya rungume sosai, ya dinga fa'din sorry a hankali, wannan rarrashin ya sanya kukan ya kwace sosai, ta dinga yi, shikuma yana saka tissue yana goge mata. Ta jima a hakan, sannan ya ce "Ya isa haka, Yi shiru ki fada mini menene ya kidima ko haka". Cikin kuka ta ce "Tsoro nake ji kar na rasaka, tsoro nake ji kar juya mini baya, tsoro nake ji kar ka kasa yin adalci ka halaka". Cikin rarrashi sosai ya ce "Na ta'ba fa'da miki ba macen da zata sa na rabu da ke saboda ita, sai idan tamu ce ta hado mu, ba yadda za'ayi na juya miki baya Farida! Ina mamakin har yanzu da muka yi shekaru uku baki fahimci iri son da nake miki ba zai tan'kwabu bisa 'karamin dalili marar tushe ba. Ba zan miki 'karya ba, da gaske an jarrabeni akan Sa'a! Amma ki taimake ni ki fa'da mini shin ina miki wani abu da kika kasa gamsuwa son da nake mata, ba zai hana na so ki ba" Ta yi shiru tana ajiyar zuciya! Ta sani bai ta'ba mata wani abu da zata ce baya sonta, ko ya tauye ta ba, amma da ace zata iya da ta ce so take ya fi sonta akan Gogel, sai dai ba zata iya ba, shima kuma bata jin zai iya hakan, tunda ta san ubangiji ne yake cusa soyayya a zukatan bayi. Ya sake rungumeta tsantsan ya ce "fa'da mini mana ke nake sauraro" Ta girgiza kai ta ce "Babu" Ya ce "Zan fa'da miki gaskiyar magana! Wallahi ina sonki, Ina tsananin sonki, hakuri da kawaicin ki ya 'kara miki 'kima a idona da zuciyata, kar ki bari kishi ya kwace miki wadannan halayyar, domin kina jan hankalina da su, ina jin kunyar bata miki. Sannan zan ro'ke ki arziki! Ki bani hadin kai ta yadda zan yi muku adalcin da zaki gamsu, idan na kuskure dan Allah ki mini uzziri wallahi ba zanyi abin da muzanta ki da gangan ba". Ta saki ajiyar zuciya taare da cewa "To". Ya dinga yi mata maganganu masu da'di, Wanda wasu ta tabbatar ya fa'da ne dan hankalinta ya kwanta amma dai ta ji da'di kwarai da gaske, ta samu sau'kin daurewar da kirjinta ya yi. Ya kalli agogo ya ga har sha'dayan dare ta gota ya mike da ita cak tamkar yar jinjira ya shige daki da ita ya dire kan gado ya ce"Ashe ma fafaloloce ba nauyi" Ta dan murmusa kadan ba tare da ta ce komai ba. A haka ya dinga hilatarta sai da ya raya daren da ita cikin wata irin soyayya mai tsayawa a zuciyar mace. Har ranar daurin aure ta zo ba wani jituwa tsakanin Mk da Sa'adah. Ranar juma'ah 15/7 aka sake daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel akaro na biyu akan sadaki Mai darajah. Sai yamma suka baro Gogel, duk yadda Mahmoud ya so suje gun amarya Amma Mk ya ce ba inda za shi. Dr 'Karfi ya kalli Dr Mk da ya yi kicin kicin da fuska ya ja tsaki ya ce "aikin kawai duk wani cin magananinka na 'karya ne, wato yanzu ka sami kwanciyar hankali shine zaka hau wani fiffika, to dan ma dai tsiyar Sa'adah ta fi taka, yanzun nan zata sumar da kai, farfadowa sai a gadon asibiti". Fuska a daure Mk ya ce 'Tunda ba a lahira zan ji ni ba, ai da sau'ki, ka takura ni fa ". Da dariya 'Karfi ya ce wallahi ka bini a hankali ka san ina da dorinar da idan na zuba maka sau uku, amarcin da kake rawar jikin zaka sabunta shi ba zai yiwu ba". Dariya ta kwace musu dukkansu Mk ya guntse ya ce "Na rantse kuwa da ba zan yarda ba". Har suka rabu caccaka Mk yake sha a wurin Mahmoud. Washagari da hantsi Mk ya yiwa Sa'adah siyayyar komai na amfani, karon farko da shi a karan kansa ya siya ba wai Jawad ya saka shi akan dole ba, ya tuno sadda take cewa idan ya sake yi mata wani abu na alheri ba zai gama da Hajiya lafiya ba. Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya yana ayyana banda zuciya ba a ganinta bare a hukunta ta ai bai kamata zuciyar tasa ta zarme akan soyayyarta haka ba. Ya nisa a fili ya ce "Albarka cin Baffah na yafe wannan maganar". Amma haushin ganinta da Khalil da kuma tariyar da ta ce ba zata yi yanzu ba, ya matu'kar bata masa rai, shiyasa kullum ya yi sallah sai ya roki ya samu dalilin da itace zata nemi ta tare da bakinta. Ya cika mota da kayayyakin ya nufi gidan su Sa'adah. Domin ya kai mata ,tunda yanzu ta rataya a wuyansa, duk da ita bata da niyyar sauke nasa hakkin da ya rataya a wuyanta. Surayya Dahiru ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *GAISUWA GA*. *Haj Zulaihatu Sani Kagara* *Haj Maimuna Beli*. *Hassana 'Danlarabawa*. *Ku Dade, ku yi 'karko irin na Dabino*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 107-108. Sannu a hankali yake yin tuki, har ya isa gidansu Sa'a. A zauren kofar gidan, ya tsaya, ya fito da wayarsa, ya dinga 'kiran layin Sa'adah amma tana gani ta yi mirisisi, yana tsaye Baffah ya shigo, suka gaisa ya ce "Ya ka tsaya shigo mana". Tare suka shiga cikin gidan, Inna ce a Zaune tana kwadon zogale. Mk ya zauna a gefen tabarmar da Baffah yake kai, ya gaida Inna! ta amsa ba yabo ba fallasa. Cikin nutsuwa Mk ya ce "Inna ina neman afuwarki, na sani ni mai laifi ne, amma tunda ubangiji ya sake hadamu ina rokon ayi mini hakuri, bana jin da'din yadda kuke mini ke da Hajiyar Bichi". Kunya ta matu'kar kamata, ta dinga jin wani iri, da kyar ta yi kundubalar cewa "Ni ba fishi nake yi ba, Allah ya kiyaye gaba, yasa albarka a aurenku". Da'di ya yi matu'kar kama Mk, ya yi ta godiya. Baffah ya ce "Idan ka zo, ka dinga shigowa, ai yanzu ba maganar tsayawa a zaure, Ina fatan ku kammala shirin ku da sauri ta tare hankalin kowa ya kwanta". Innah da ta gama 'kwadon ta zubawa Mk, ta kai na Baffa dakinsa sai ta yi shigewarta daki, yayin da Baffah shima ya fita yana cewa Mk "shiga tana ciki, bakam ta yi". Ya shiga dakin ya sameta a zaune cikin kwalliya tamkar ya yi mata waya zai zo, ta yi masa kwalliyar. Ya zauna yana shakar kamshin turarenta, ya kalleta, ya na tuna sadda ta zo wankan haihuwar Jawad irin soyayyar da suke fakar idon Innah suke yi a dakin, amma yanzu ba wani farin-ciki a tare da ita, asalima tunda ta amsa sallamarsa bata sake yin magana ba. Ya daure ya hadiye

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});