Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fadin, "Aiko idan hakane zan baka mamaki, ka saurare ni zuwa anjima".. Ba ta jira cewar shi ba ta daste kiran, ta yi wulli da wayar ta na neman tsari da 'kaddarar da za ta hada su zaman aure da wannan mai tulelen ciki. Kanta ta ji ya cushe musamman yadda Inna ta fara matsa mata a cikin kwanakin nan akan lalle sai ta tsayar da miji cikin manemanta, har zuwa yanzu ba ta jin akwai wani da za ta yi zaman aure da shi kamar Mukhtar Kabir Bichi. Amma ko shi da ta tabbatar da abu 'daya, ta ha'kura da shi ba dan ba ta so ba sai dan ha'kurin shi yafi. Ta kuma gamsu ita ke da laifi da kaso mai yawa na 'kaddarar rabuwar su da Abban Jawad, ta tabbatar ya so ta, son da ba algus amma *HALIN YAU* da rudin 'kawaye ya jefa ta cikin kogin nadama. Irin wanda ake cewa tsalle daya mai jefa mutum rijiya, ya yi dubu bai fito ba! A hankali ta koma ta kwanta tana tariyo rayuwar ta, ta baya, tun kafin haduwarta da Mk Bichi. haduwarsu, aurensu, rabuwarsu, har zuwa yau da take jin duniyar ta yi mata daurin goro. Ashe 'dan Adam baya rabuwa da matsala? Ashe duk matsalar da mace za ta fuskanta indai tana zaune a dakin aurenta matsalar da sauki, akan matsalar rashin auren, da rabuwa da 'ya'yanta? Wanne tabbas mace keda shi a wannan halin na yau, za ta sake samun damar aure a karo na biyu? Idan ta samu din ma ba za ta kauce wa matsalar *HALIN YAU* ba, ko kuma ta tabbata tana aure-aure. Ta nisa ta tuna wata maganar gyara kayanka, da fasihiyar marubuciya, Fadila lamido inda take fadin, *"Uwa da sadaukarwa aka san ta, domin rayuwarta da ta 'ya'yanta, ta inganta.*' To shin ita me ta yi ne dan ganin ta SADAUKAR da komi dan inganta kanta da tilo 'danta? Tabbas ba ta yi ko mai ba, sai rusa farincikin kanta dana 'danta Jawad! Ta yi dalilin da yake rayuwa ba a tsakanin uwa da uba ba, hawaye ya gangaro mata na takaici da kaico iri iri. Ta tuna wani darensu a Abuja, ya dinga rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya, komai take so zai dinga yi mata a hankali, a lokacin ita kuma tana ganin tamkar idan ba ita, ba zai iya rayuwa ba, saboda yadda yake tsananin sonta da kulafacin son zama da ita, duk yadda take ganin aibun su Halima, a yanzu da take fuskantar NADAMAR biyewa Halayyar yau, ta fi ganin aibun kanta da kanta, tabbas zuciyarta da tunanin ta basu mata adalci ba, domin tunda ta taso take jin ana azanci da cewa idan mafa'din magana wawane majiyinta ba zai zama wawa ba, amma ita sai ta zama mahaukaciya ma. Zuciyarta ta sake ba'ki wani irin numfarfashi take yi tamkar mai fama da cutar Asma, hakanan hawayen ba'kin ciki ya kwace mata tamkar mai yin Takaba. ```Alkalamin SURAYYA DAHIRU ```✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR*. 7-8 HAWAYEN nadama marar amfani ya ci gaba da zuba da ga kyawawan idanuwanta ba 'ka'kkautawa, a hankali ta koma ta kwanta, zuciya na suya, rabon da ta shiga irin wannan yanayin tun shekarun baya da suka shude. Shekarun da suka fi kowanne tsauri da tsanani a rayuwarta, a lokacin da ta dinga yun'kurin gyara kuskurenta amma MK bai ba ta wannan damar ba. Duk da ta san ita ke da kaso mai yawa na lalacewar aurensu, tunda ba irin 'kabali da ba'adin da bai mata ba, ba kalar rarrashin da bai yi mata ba. amma tasa hannu har da 'kafafu ta tankwabar da dukkan ha'kurinsa, ta tabbatar akan dole ya rabu da ita, ita kanta ta shaida hakan. Tissue tasa ta goge hawayen da ya 'ki yankewa, take kuma zuciyarta ta yi tsalle ta hasko mata irin kyaun da ya yi cikin tufafin da take matu'kar son ganin sa a ciki wato farin kaya, sam ba ya girma, ba wanda zai kalle shi yace ya kai shekaru arba'in har da biyu. Dan kuwa idan ya ce bai yi auren fari ba, ba wanda zai 'karyata shi, Ubangiji ya mishi kyakkawan jiki matu'ka gaya. Murmushi mai hade da hawaye take yi lokaci guda, saboda yadda ta ji a ranta da zuciyarta domin ita ya yi shigar tare da fatan ko Allah zai sa su hadu, a hankali ta fara jin sau'kin 'kullewar da 'kirjinta ya yi yana raguwa, a dalilin tabbacin da ta sake samu na har yau shi ma yana son ta, dama idan akwai abin data yarda dashi to son da ya ke mata ne. Amma kuma me yasa bai yarda da ita ba? Nan da nan 'kuncin 'kirjinta da ya fara warwarewa ya dawo ya 'kulle fiye da farko idan akwai abin da yake 'daga mata hankali bai wuce rashin amincin daya jefe ta da shi ba, alhalin shine mutum na farko daya kamata ya shede ta, ta kuma zama amintacciya a idonsa, kuka ya 'kwace mata sosai, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta dan kar Inna ta jiyo. Haka ta danna kanta a pillow ta yi kuka mai nuna tsantsar bakin ciki da takaicin da mai yinsa ke ciki, duk yadda zuciyarta ta yi zafi, kanta take 'kalubalanta, ta san ko mai Malam ya yi ko ya ce mata, ba shakka ita ce sila, ita ta janyo. Istigifari ta dinga ambato dan ta sami sau'kin zuciyarta, tsawon lokaci kafin ta ji ta fara samun nutsuwa sai ajiyar zuciya take saukewa. Wayarta ta dauko tana nazarin shin a littafi zata rubuta ne ko a waya? A littafin tafi gamusuwa da ta rubuta tarihin rayuwarta dan ya zama izna ga sauran mata. Idan ta sami halin buga shi, za ta buga dan ya zama gargadi ga duk wacce son zuciya da *HALIN YAU* ke dawainiya da ita. Mi'kewa ta yi tana laluben littafi da biro a cikin jakar karatunta, amma cikin rashin sa'a ba ta samu ba, kowanne ta yi rubutu mai yawa a ciki. Tsaki ta ja, ta rike 'kugu kafin ta yi wani yun'kurin abin yi, ta ji sallamar almajirinsu yana fadin na dawo. Da sauri ta iso ga katifarta, ta 'daga pillow ta dauki gudar dari biyar ta fita ta ba shi, ya siyo mata littafi na rubutu mai shafi tamanin (80 leaves). Daga nan ba ta dawo dakin ba, buta ta dauka dan tayi alwalar la'asar tunda yan mintina ka'dan ne su ka rage. ***** Kwance ya ke kan sofa a dakin barcinsa, ya lumshe ido tamkar mai barci amma a zahiri ba barcin yake yi ba. Tun ranar da ya ga Sa'adah nutsuwa ta masa tutsu duk yadda ya kai ga daurewa har abin ya bayyana a fuskarsa da gangar jikinsa gaba'daya. Wata irin nutsuwa ya gani a tare da ita, wadda bai taba gani a tare da ita ba, gaba'daya ta canja, ilimi da hankali sun matu'kar ratsa ta. ba kamar lokacin da suka rayu tare ba. ko dan ya dauki lokaci mai yawa bai ganta ba ne? Farida ce ta shiga dakin, kusa da 'kafafuwansa ta zauna tana mai jan yatsun 'kafarshi, a hankali cikin sanyin murya da halittarta ce, ta 'kira

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});