Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Lallai Baba ba komi na gode" da haka ta sace ta daina fishi. Shi ko Malam yana tafe yana ayyana abubuwa masu girma game da lamarin ta, komai nata burgeshi yake, bai ta ba ganin halittar da ke daukan hankalinsa irin surar ta ba, kawai wasu daga cikin halayyarta ke 'dimauta tunaninshi su hana shi zaman lafiya amma duk sanda zai dora idonshi a kanta sai ya ji bai ganin komai da kowa sai ita. Har yau har gobe yana son ta, amma ta riga ta shayar da shi bakin cikin da zaman aure zai yi wuya tare da su. Har suka iso Kano tunaninta yake idan ya tuna *happy moments* dinsu yayi murmushi, idan ya tuna *though times* dinsu sai ya ja tsaki ko ya furta ya *Salam* ko *SubhanAllah.* Ba su rabu ba sai da suka zo Gandu ya yi wa direbansu fitila ya wuce, a nan ma sai da Baba ya tsokaneta da cewa "To Sa'adatu wannan fitilar fa da ya yi bata kowa bace, taki ce!" Suka hada baki wurin fadin, "Ai kuwa dai Baba!" suna kuma dariya. ```Alkalamin SURAYYA DAHIRU``` ✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ` https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GABA'DAYA GA* *SADIQ ABUBAKAR* 5-6 Har 'kofar gidan yayarta Sumayya suka kaita dake kan titin Kwankwaso Gandun Albasa, sannan suka juya, Baba direba, nata jaddada mata ta daina saurin fushi mabudin fitina ne, ta yi godiya, tana cewa su Zainab sai nan da kwana uku za ta dawo unguwar tasu lokacin innarta ta dawo daga tafiyar da ta yi. Da sallamarta ta isa cikin katafaren falon Sumayya, ba kowa sai TV da take ta babatu hadi da dan dirin AC da ke tashi a hankali, ga 'kamshin *Air Freshner* dake tashi sannu a hankali, take ta ji duk gajiyar da ta kwaso ta taso mata gabadaya. Dan haka sai kawai ta zube a Kan doguwar kujera ta yi kwanciyar ta ba ta jima da kwanciyar ba, barci mai nauyi ya yi gaba da ita. Sumayya fitowa tayi daga bangaren maigidan, da a yammacin yau aka sallamosu daga asibiti, ta ganta tana ta barci. Murmushi ta yi tare da cewa, "Oh a 'yar wannan tafiyar ne kika gaji har haka?" Ta gyara mata rigarta da ta 'dage, ta shige kicin don hada tea. Hayaniyar yaran gidan ne da suka taso da ga lesson wadda takanas aka dauki malamin da zai zo har gida yana musu bita, yasa ta tashi musamman da 'karamar cikinsu ta fada kanta tana fadin, "Mami yaushe kika dawo?" "Khairat kin san yadda na gaji!" Ta 'daga ta, tana cewa "Ina Yaya Jawad?" "Ya na lafiya, ya ce duk yana gaishe ku" Ta sake cewa, "Mami bai ba da komai ki bani ba?" Daga Sumayya har Sa'adah dariya suka yi yadda Khairat din ta yi. Jakarta ta bude ta dauko wani dan abu a nade da wrapping paper ta ce, "ga shi nan ni kaina sai da ya ro'ke ni kar na bude tunda ban san ma ya saba, ya dai ce mini zan ga abin Khairat don Allah kar na bude." Yayansu Ayman wanda shi ma yana da yayu Abba da Khalifa suna Egypt suna karatu, ta nufa tana cewa, "Bude mini yaya!" Nan da nan ko ya hau warwarewa sai ga Lush Cookies Biscuit har guda biyar sai Teddy Bear 🧸 'yar 'karama mai kyau da yar 'karamar takarda an rubuta little Khairat. Da murna soasai tace "Yaushe to zai dawo Mami?" Anis ne ya ce, "Sai nan da 6 weeks." Ta galla mishi harara, "Na tambaye ka ne?" Da yake sa'kuwar shi ce ba su cika jituwa ba. Ta juya ga yayansu,"Yaya Ayman kwana nawa ne a 6 weeks?" Kai tsaye ya ce mata, "42 days." Da sauri ta ce, "Gobe zan samo stones 42, kullum na dinga minus, ranar da suka 'kare to ranar zai dawo saboda na soya mishi wainar fulawa." Dukkan su dariya ta ba su, amma Sa'adah mamakin wayonta take, tana kallon Anis tana tuna daidai lokacin haihuwar sa ta shiga matsaloli masu yawa da Malam. Shekarunta biyar a duniya amma wayonta da azancinta ya zarce na 'yan shekaru bakwai. mutumiyar Jawad ce sosai ta fi shiri da shi fiye da yayyenta. Shi ma kuma haka yake ji da ita musamman da shi ba shi da 'kani ko 'kanwa sai ya tattara dukkan 'kaunar da yaya yake yi wa 'kanwarshi a kanta. *Bayan kwanaki uku* " Iya Iya dai, na san tabbas daga shigarki ba za ki ce mini wai har kin yi barci mai nauyin da za ki kasa jin kuwwar da wayar ke faman yi ba." Da kanta ta tashi ta leka, ganinta ta yi tana kwance ta 'kudundune ta rufe fuskarta da dukkan hannayenta, "Kin san Allah? Idan kika bari na shigo ba ki tashi ba sai na ci mutuncinki, ai na san sarai kina ji na" Tashin ta yi tana murtsika idanuwanta "Ni fa Inna barci nake yi!" Kafin Innar ta yi magana wayar ta sake daukan ruri a karo na uku dan haka ta kafeta da idanuwa, akan dole Sa'adah ta sa hannu ta amsa wayar. Sannan Inna ta juya ta fita tana fadin, "Shashasha haka ki ke tunanin za mu bar ki ki yi ta zama? Ai tunda kin gama karatun to kuwa wallahi sai dai ki fito da miji cikin jerin wadanda suke son ki dan ba zan yarda da wannan zaman ba. Haka kawai kowa ya zo ki ce bai yi miki ba, kowa bai miki ba, wanda ya yi mikin kuma bai shirya sake zama dake ba. Amma kin kasa gane gaskiya, kin kasa gane ita mace lokacin ta 'kan'kani ne! Bari Baffan naku ya dawo na gaji da halinki!" Sa'adah kuwa da alatilas ta dauki wayar Alh. Mamman wanda dan majalisar tarayya ne mai ci a yanzu, ya so ta tun tana budurwa, a lokacin yana dan majalisar dokoki na jaha, shi ne har yau yake ta bibiya, tun lokacin budurcinta ta san komai game da shi. Mutum ne mai yawan kyauta da kyautatawa, ta tabbatar da hakan, ita kanta ta san ya mata 'barin kudi. Tun a lokacin yana da mata biyu da yara takwas wanda wannan dalilin yana cikin dalilin da ya sa ba tayi marmarin ma auren shi ba, Illa dan ta sami rabonta kawai, to yanzu kuma amaryar ce ta rasu shekaru biyu da suka wuce a wurin haihuwa, shi ne yake ta bin kanta ta maye mishi gurbinta, tunda ya riga ya saba da mace biyu ga kuma tsananin 'kaunarta da yake. A nata bangaren kuwa ba ta fatan 'kaddara ta 'kaddaro ya zamo miji a gareta shi yasa tun watanni shida da suka shude ta yakice shi a dukkan lamarinta, tunda dai kam ai ta riga da samun rabonta🤔. Ta yi amfani da alfarmar shi ta cimma burinta, da kuma mallakar kayan 'kawa na alfarma, idan ko hakane dole ta yi gaggawan wullar da shi tun kafin reshe ya juye da mujiya. Uzirin tana aiki ta ba shi akan za ta 'kira shi anjima, murmushi ya yi ya ce, "Ranar da na ga 'kiran ki a wayata Sa'adah tabbas rana ce mai muhimmanci a raina!" Ya'ke ta yi tare da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});