Chapter 22
Chapter 22
ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Gaisuwar fatan alheri ga Zauren Fadila lamido!* *BA LABARI FANS 2* _MK DA SA'ADAH NA GAISUWA_🥰. 27_28. Cike da fargaba ta zuba wa Zainab ido, zuciyarta na bugawa ta ce, "Ban gane ba?" Muskutawa Zainab din ta yi sannan ta ce "Ina nufin ki toshe dukkan 'kofofin da kika bude na rashin 'da'a a gabanshi, kinga yanzu ya gamsu kin canja, kin shiga sahun 'dalibai masu dagewa, to ki tattaro dukkan ladabi da nutsuwa ki sanya su a fuskarki da dukkan ayyukanki, ba iya haka ba har a zuciya, ina tabbatar miki idan kika yi haka kin rufe 'kofar da zai dinga miki ganin mai 'karancin tarbiya. Sannan ki yi addu'a, ki bar wa Allah za'bi, idan alheri ne kuma an 'kaddara mijin ki ne, kina zaune Allah zai turo miki shi". Shiru ta yi tana nazarin maganganun Zainab, wanda ta tabbatar iyakar gaskiya ta fa'da mata. Ta nisa sannan ta 'dago ta ri'ke hannun Zainab ta ce Na fahimce ki, na kuma gode da shawarar ki, amma don Allah ki ri'ke mini sirrina." Murmushi Zainab ta yi tare da cewa, "Ki sa a ranki amana mu ka yi wannan maganganun, kuma mutum amintacce ne mai 'rike amana. Ina tabbatar miki da ikon Allah baki da matsala da ni" Haka suka ci gaba da hirarsu, bayan sun yi sallar La'asar ba da jimawa ba, ta musu sallama ta tafi, Zainab ta raka ta har kusan gidansu. Tunda suka koma makaranta gaba'daya ta mayar da hankali kan karatu, sannan ta bi shawarar Zainab, don haka gaisuwar girmamawa tare da mutuntawa take wa Uncle MK, har ya ji cewa lallai wannan ita ce Sa'adah 'diyar Malam Basiru, waccan da ta gabata ta aro ce. don haka ya daina duk wani gallazawa da yake mata, sai ma wani shiri da yake da ita. Wanda hakan ya janyo hankalin 'dalibai aka fara gaskata ra'de radin da ake yi cewar son ta yake yi. Wani abin mamakin kuma ita ma Farida sai ta fara jin haushin Sa'adah, tana ganin ta tamkar wata 'yar fashi a soyayya ko mai barazana a rayuwarta. ta san duk yadda take da 'kyaun da ya kai ya kawo, ba ta yaudari kanta ba, ta tabbatar ba za ta nuna wa Sa'adah komai ba, sai fari da gashi da kuma tsayi. Amma batun cikar halitta da kuma boyeyyen kyau da sai an nutsu ake gane shi ta sani Sa'a ta kere mata. Wata rana sun hadu a Biology Lab, kawai Sa'adah sai ji ta yi Farida ta ce "Iyah Basiru" Ranta ya yi mugun 'baci, tunda da izgilanci ta fada mata, take ko ta 'daga murya ta fara mata sababi, saboda Sa'adah mafadaciya ce ta gaske, sai dai kuma ita wacce ta yi tsokanar ta si'dade ta barta a gun. Wanda hakan da ta yi har ya fi wa Sa'a ciwo fiye da tsokanar da ta mata. Shike nan sai Farida ta mayar da tsokanar ta zame mata 'ka'ida sai dai idan ba su hadu guri 'daya ba, ranar kuma a shop suka hadu ta faki ido ta galla mata harara tace, "Sa'ade gwalli" Abinka da wanda aka dade ana tsokana kuma mai 'karancin ha'kuri sai kawai ta zabura ta kai mata wawura, ta sha'ke ta da 'karfin gaske, nan da nan hankalin mutanan gun ya kai kansu, aka taru aka karbe Farida a hannunta, tana mayar da numfashin wahala dan ba 'karamin sha'ka ta sha ba, musamman da ke ba ta da da kuzari saboda rashin cikakkiyar lafiya. Aunty Ngozi malamar (Mathematics) ce ta zo wucewa ta tsaya tana tambayar ba'asi, bayani aka mata wanda kusan duk gurin shaida aka wa Farida cewa tana tsaye kawai aka ga Sa'adatu ta kama ta da kokawa. Saboda haka sai ta tattara su ta tafi da su Staffroom wanda a can aka yi shari'a. Kusan dukkan staff din bayan Farida suka bi, saboda rashin hayaniyarta, ga ta kuma hazi'ka ce, haka aka yi punished din Sa'adah ta hanyar sa ta shara da kuma gargadi mai tsanani, akan komai za a mata ba ta da ikon daukar doka a hannunta. Hatta Uncle MK, Sa'adah ya jawa kunne akan zai yi wahalar gaske Farida ta tsokane ta wanda hakan da yayi yasa ta jin wani takaici ya kama ta fiye da yadda aka ba ta horo bayan kuma ita ce da gaskiya. Wannan abin ya yi matu'kar tsaya wa Sa'adah a ranta, shi yasa ta ji gaba'daya makarantar ta fita akanta musamman ko yaya idan ta ga gilmawarshi da Farida sai ta ji dukkan walwalarta ta kau, duk da dai ba ta da tabbacin abin da take zargi a tsakanin su. Tunda ga nan kuma Farida ba ta sake marmarin tsokanar Gogel ba dan kuwa ta ji 'kamshin mutuwa a hannunta🤩. Ana cikin haka aka fara register din JAMB, tana fada wa Baffan su maganar kai tsaye ya ce mata ba wata jarrabawar shiga Jami'ar da za ta yi don kuwa aure zai mata idan mijin ya yarda sai ya siya mata ta yi a 'dakinta. Wannan ma na cikin damuwar da ta sake sa mata tsanar FGC KANO. Dukkan 'yan ajinsu za su yi wannan jarrabawar sai ita kadai ce a ajin za a ce ba za ta yi ba. Wanne irin koma baya ne wannan? Wannan ba da kai har ina? Kamarta ace ita ce koma baya a komai?🤔 Sa'adah ke nan! Wadannan damuwowin sai suka sa ta ji gara ta koma asalin makarantar da ta bari a baya ta zana jarrabawar kammala sakandire, nan ma da ta gabatar da maganar gaban Baffa tare da ba shi uzirin ai ba sosai ake cin jarrabawa a wannan makarantar ba, kai tsaye ya ce mata bazai yiwu ba, tunda anriga an biya mata kudin jarrabawar ba, ba za a yi asarar su ba, wannan shi ne karon farko da Baffan bai goya mata baya akan wani abu ba. Ganin ba ta sami goyon baya ba, ga kuma ba'kin cikin da za ta kwasa a FGC KANO, sai kawai ta daina zuwa makarantar gaba'daya, wanda hakan bai damu Baffanta ba, sai cewa ya yi to ta fito da miji, ai Sumayya ma ba ta sami hakan ba ya aurar da ita ga shi nan kuma tana zaune lafiya cikin rufin asiri mai yawa, fiye ma da wanda suka yi karatun. Inna kuwa uffan ba tace mata ba saboda yadda take ganin take-taken Sa'adah nan gaba fin 'karfinsu za ta yi, garama a aurar da ita ya fi mata kwanciyar hankali. Tsawon sati tana gida ba ta je makarantar ba, rannan da yamma tana kwance a dakinta, tunda yanzu Inna fushi take da ita sosai, don haka ba ta jin da'din zaman gidan gaba'daya, ta ji murya Baffa na fadin"Iyah" Da sauri ta amsa ta fita tsakar gida inda yake tsaye, ta tsugunna tare da cewa "Gani Baffa" Ya kalle tay ya ga duk ta lalace tsabar fitinar da ta sawa ranta. ya ce, "Da ma yaron nan Mutari ashe a makarantarku ya ke koyarwa?" Shiru ta yi tana nazarin sunan, kafin ta ce, "Wani abu ya sake cewa?" "Dazu ya same ni a inda nake zama shima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157