Chapter 13
Chapter 13
abin da zai kankare wannan son, dole za a sami matsala a cikin zamantakewar aure, muhimmi shine ayi afuwa, a yafe, a kuma manta, amma ba za a iya kaucewa matsalar ba. ko wani sabon auren kipka yi komai jin da'din da za ki riska sai kin tarar da matsala" Ya nisa sannan ya sake fa'din, "Ina tabbatar miki kuma a yanzu ne ya fi dacewa ki koma dakinki, ba a wancan lokacin da ke kadai kike son komawar ba, yanzu da shi ya bukaci hakan da kansa za ki fi 'kima, ki fi daraja" Sunkuyar da kai 'kasa ta yi hawaye na cika idonta, amma ba ta ce komai ba, ganin yadda jikinta ya yi sanyi, hakan ya 'kwarara guiwar 'Karfi. Ya sake kur'bar ruwa ya ce, "Kar ki bari wannan damar ta kubuce miki, ina tabbatar miki, MK bai so wata mace kamar ki ba, kar ki bari rudin 'kawaye da zuciya su sake rudar ki a karo na biyu, wai ya yi aure, ko kaza da kaza, da duk abin da zai sake dagula miki lissafi. Ki sa a ranki cewar ko kuna tare zai auri Farida! tunda an rubuta a cikin littafin 'kaddararshi cewar matarshi ce, mu gode Allah da ya kasance rabuwa ku ka yi, ba mutuwa kika yi ba, kin san akwai rabon da ke kashe mutum". Hawayen da ta ke tattalawa ya zubo akan lallausar fuskarta, ta ce, "Ai ni sai daga baya na gano dama auren ya 'kallafa rai zai yi shi yasa ya yi ta zungurata, komai 'kankantar laifi sai ya juya shi ya zama garma, ashe dama akwai abin da ya 'kudure, to ya aureta hankalinshi ya kwanta, ni ma kuma ai bai jini a gadon asibitin mahaukata ba, bai kuma ji labarin auren nashi ya zama ajalina ba" Kuka ya so kubuce mata saboda haka ta yi shiru sai rishin kukan kawai. Sai da ta nisa sannan ta sake dorawa da cewa, "Ni kuma nan duniya ban ga mai zai mini na ga farin shi ba" Ta fada cikin dakewa da shanye kukan dake son kunyata ta. Jikin Mahmoud ya sake yin sanyi, ya yi shiru cikin rashin abin cewa. Tsawon mintuna biyar kowa ya yi shiru a tsakaninsu sai fama suke da tunanin zuci. Shudewar yan mintuna kafin ya ce, "Ni fa ba tone-tone za mu yi da ke ba, dukkanku, kowa da irin nashi laifin amma kin sani, laifin ki ya fi yawa" Cikin takaici ta ce, "Baban Dadi tunda laifina yafi yawa, ai ya sake ni ya auro wacce ba za ta yi kuskure ba, wacce son da ake mata zai sa ayi ta mata uzirin ri'ke igiyar aurenta da kyau, sai dai a nuna mata kurenta cikin ladaftarwar da shari'a ta tanadar, shi yasa ni ma da na gane ba son nawa ake ba, kuma duk ni ce mai laifin sai na dau hukuncin da macen da ta san ciwon kanta za ta dauka don ta tsira daga ba'kin cikin namiji". Shiru Mahmoud ya yi mata ya lura kishin Farida ne ya ke cinta shi yasa take ta furzar da magana, don haka ya 'kyale ta, at least dai za ta sami sau'kin ciwon dake addabar zuciyarta. Sai da ta yi shiru don kanta, sannan yace"Ki yi ha'kuri, ki bi komai a sannu, ban hana ki nuna bacin ranki ba, amma kar ki wuce gona da iri, saboda kin san kema kin mishi laifin da sai da ya yi jinya bayan rabuwarku, tunda har ya sau'ko, to fa kar ki wuce makadi, ina fada miki wannan maganar ne a matsayin yayanki" Ya dan numfasa, kana ya zarce da fadin, "Lamarin aure yanzu sai ha'kuri ba Perfect Marriage, kowanne aure da irin nashi 'kalubalen, duk abin da aka ce ibada ne, to fa sai an yi hakuri". Ya mi'ke yana cewa, "Zan wuce, ki saurari zuwanmu!" Hannu yasa a aljihunsa ya fito da yan dari biyar guda ashirin ya zuba kan kujerar daya tashi, da sauri ta ce, "Don Allah ka bar su, kullum a cikin hidima kake " Murmushi ya yi yana cewa, "Wannan kudin zance ne, ina fatan dai za a karbe mu da dukkannin raunin mu, kasancewar mu Malaman makaranta masu sadaukarwa, ba ma su satar kudin jama'a ba" Ta san sarai inda maganar shi ta dosa, da Alhaji Mamman ya ke, tunda ya sha ganin ta da shi, wanda 'karara yake taya amininsa kishi. Dariya ta yi tana kuma godiya amma ta ci alwashin bashi ya ci, dole sai an baje maganar nan ai ya san tun farko ta zabe su tabar Alhaji Mamman din da dukkan abin da yake da shi. Tun a mota yake 'kiran lambar MK amma bai dauka ba, har ya gaji ya mayar da wayarshi caji a jikin motar. Mintuna kusan ashirin har ya shiga layin gidansa yaji 'karan wayar shi, ganin sunan MK yasa shi dauka da sauri, tare da cewa, "Wai ina ka shiga ne?" Daga can ya amsa mishi da cewa, "Wallahi ina tare da Farida ne ba zan so ka yi mini maganar Sa'adah a gabanta ba" Shiru Dr Mahmoud ya yi yana jin shi kam bai san wani namiji da ke gudun 'bata wa matarshi da gangan irin MK ba, ya tuna lokaci da dama da yake zaunar dashi yana caccakar shi akan tsoron Sa'adah ya ke yi, ashe ba tsoro ba ne tunda ga Farida ma hakan ya ke mata. Mutum ne mai martaba abin da yake so, ko wadda yake son sa, ya sake tuna ko a abotarsu, MK ke ha'kuri da shi, shi ke masa hidima ba tare da tunanin ai yasan yawan albashinsu 'daya ba, samun irin Mukhtar Kabir Bichi zai yi wuya a wannan lokacin. Amma duk da hakan sai da ya tsokane shi da cewa, "Dadi na da kai mijin ta ce ne kai, ni ban san me ya sa kake jin tsoron mata ba, ai na 'dauka Sa'adah ce kawai dodon taka, ashe wa lnnan alankosar ma murza ka take yi". Shi ma cikin 'kosawa da shakiyancin da ba ya gajiya da mishi ya ce, "Kai ai ba za ka gane karatun ba ne ni kadai na san mai suke jiyar da ni, ka ga kuwa ai dole na yi tattalin farincikinsu, kar ni ma a hana ni nawa farin cikin" Dariya sosai 'Karfi yake yi yana cewa, "Ashe haka karatun yake ganewa ne ban yi ba? amma da dukkan alamu karatun naka na daban ne" "Idan kagama iya shegen naka, ina sauraranka don waje na fito, idan kuma ba ka gama ba, to zan koma, ma hadu gobe" 'Karfi ya gintse dariyarsa hadi da cewa, "Kai MK wallahi da alama 'yar darun taka, ta shiryawa daru kala-kala, amma dai na san kishi ke 'dawainiya da ita, ka san tunda ka yi auren nan bata bude baki ta ce 'kala ba, yana ta cin ranta, na ga soyayyarka mai yawa a idanuwanta duk da bakinta na 'kirarin rashin son" Shiru MK ya yi har Mahmoud ya yi tsammanin ko wayar ce ta katse. Amma da ya ce, "Kana ji na kuwa?" MK ya amsa da cewa "Ina jin ka. Mamakin ta ne ya ke ta kama ni". "Ai ba mamaki a lamarin mace." A cewar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157