Chapter 59
Chapter 59
da ta ke ciki na rashin tsarki. Idonsa sunyi ja, sun kankance saboda fitina, ya zuba mata su,ya ce "Hajiya Babba da Innah ne suka zartar da hukuncin nan, hakuri zamu yi, mu yi yadda suke so". Wani irin farin ciki ya sake kamata, amma a iya zuciyarta ya tsaya, tana jin zumudin sake zama da mahaifanta na taso mata. Haka suka kwana yana jaddada mata irin kewarta da zai yi, tamkar wadda kasar za ta bari. Kwanaki biyu a tsakani ta koma gida tare da dukkan abin da za'a bukata, Hajiya Babba ce kuma ta kaita kamar yadda ta yi al'kawari. Sosai Inna ta ke kula da Sa'adah, wankan rumfu take mata ba tausayi, ga duren kunu, da tuwo, duk ranar da zata mata gardama kuwa cewa take yi " Na lura dakinki kike son komawa, zan 'kira Hajiya ta zo ta mayar da ke, tunda ina tattalinki, kina 'ki! idan kika kufu'de na ga yadda za kiyi rawar jiki akan mijin, ko shi ya yi rawar kai akan ki". Shiru ta ke yi, kan dole kuma sai ta yi yadda Innar take so. Jawad ya sami kyakkawan kulawa, kullum safe aka masa wanka ya sha nono, Inna take goya shi, haka zai yini a baya sai anyi azahar yake tashi, cikin 'kan'kanin lokaci ya bundume, kammaninsa da Mk suka bayyana 'karara. A yini Mk na kiran Sa'adah kamar sau uku koma fiye, koyaushe cikin tambayar lafiyar su, ko yace Babana na kukan dare har yanzu, ko ya tambayi me take so, menene bata da shi, kar fa tace zata dinga 'dorawa Baffa nauyi. Ire iren tambayar kenan a kullum, itakuma cewa take, komai akwai Uncle. Duka-duka ma yaushe muka zo ne? Ranar da suka yi kwana biyar, ya je musu. Ana idar da sallar la'asar ya Isa gidan, a zaure ya tsaya, yana faman kiran wayarta, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, ya jingina da bango, yana ri'ke da wayar. Baffah da yake faman jijjiga Jawad, saboda wankan da Inna ta ke yiwa Sa'adah, kullum ana idar da Sallar la'asar yake dawowa gidan dan ya ri'ke musu shi, su yi wankan, saboda riko da al'adar ba a barin jariri shi ka'dai.😁 Yau sai koke koke yake yi a dalilin cikinsa ya kumburaba a ankara ba, yana sa'be da shi a kafada ya doshi zauren, kwatsam yaga Mukhtar a tsaye. Cike da girmamawa ya tsugunna ya gaida shi, Baffa sai fadin "ya ka tsaya anan? da ga yau ka dinga shiga kanka tsaye". Baffah da kansa ya masa jagora har 'dakin Sa'adah yana cewa "wanka suke yi, zauna ka saurare su kadan". Ya mika masa Jawad tare da fadin "dama so na ke na fita ana jirana za mu je dubiya asibitin Malam". Cike da kunya ya karbe shi, yana masa godiya. Baffah na shirin fita Inna ta fito duk ta hada zufa, ta kalle shi, ta ce "kwantar da abokin naka ka yi?" "A a Babansa ne ya zo, yana gunsa, na shigo da shi, yana dakin Iyah ni fita zanyi, za mu je asibiti mu sake dubo Malam lado". "Adawo lafiya, shikuma Allah ya bashi lafiya". Ya fita, yana fadin "Ameen ameen". Sai da ta sako hijabi sannan ta shiga suka gaisa da Mk, da yake ta fama da Jawad. Ta karbe shi tana fa'din "Bari a masa wanka kar sanyin yamma ya sauka, ko idan ya ji ruwan dumi zai daina wannan koke koken". Murmushi kawai ya yi, kansa a kasa, ya bata shi, a zuciyar sa tana jinjina kunyarsa, ko Idris din Sumayya bai kai shi kunya ba. Yana zaune yana jin kukan wanka da Jawad ya ke tsalawa, jikinsa sai tsuma yake yi, yana jin tamkar ya leko yaronsa ko sabulu ne ya shigar masa ido, amma kawaici ya danne shi. Ana cikin haka Sa'adah ta shigo da daurin kirji, ta yi mayafi da faffadan tawul. Mamakin ganinsa a zaune ya daskarar da ita a tsaye. Da azama tace " Uncle yaushe ka zo?" "Tun dazu, dan Allah hanzarta ki dubo yaron nan , ki ji har shidewa ya ke yi?" Ri'ke baki ta yi tare da cewa"oh oh wato Innah tace mini bani da kunya ko?" "Haka yake da kukan wanka, da angama kuma ya yi ta barci, sai dare zai ishi Inna da kuka". "Oh barinta ki ke da shi?" Eh to, shi sai yace ba zai kwanta ba, sai dai a baya! itace kuma mai jure goyon, tace na kwanta na yi barci na huta". "Amma kuwa dai ba ki da tausayi ko da ya ke, Auta ce ai". Dariya suka yi a tare, ts shirya cikin doguwar rigar atamfa, irin dinkin masu shayarwa. Ta zauna tana shafa mai tare da turare, ta yi cas, ta masa kyau, da gaske ta huce din, duk wani kumburi ya sace, fuskar nan da ta aune, duk ta sabe, ta dawo masa Sa'adatun nan mai burge masu kallon ta. Yace "kin huce din fa Iyah, kin zama so mashallah". Ta tura baki gaba, tace "ai so na yi na zauna kar na huce din, naga yadda zaka yi". "Hmm ke dadina da ke misunderstanding dina kike yi sometimes". "Iyah Iyah" Ta mike da sauri tana amsawa ta fice gurin Innah da take 'Kiran. " Zo ki dauke shi ki bashi ya sha, ashe cikinsa ne ya kumbura shiyasa kukan yau yafi na kullum, yanzu Ina bashi wannan maganin ya hau gyatsa, sai kuma ga tutu, dole sai canja masa Pampers din na yi" Ta karbe shi tana fadin"Ayyah, sannu da kokari Innah". Ta dawo dakin ta zauna ta fara shayar da shi, Mk da ya zuba musu ido yana jin duk wani bugun da zuciyar sa ke yi da kaunar su ta ke bugawa. Sai da ya 'koshi, sannan ta mi'ka masa, ya karba yana mai masa kallon kurillah, yana ganin hoton fuskar sa, akan ta yaron. Ya dago ya kalleta, ya yi kasa da murya sosai, sannan ya furta "Duk yadda kika yi ta makale min, ashe ba wani abin da kike tabukawa? dubi! ba wani abu, na ki a jikinsa". Kunya ta kamata, ta kasa cewa komai sai ta buge da murmushi. Haka suka sha hirarsu, ta na shan yoghurt din L&Z da ya taho mata da shi. Kwana ashirin da haihuwar, Sumayya ta zo ganin Baby, tare da kayan uwa da jariri kala kala,sun zo juma'ah suka juya lahadi saboda makarantar Yara. Ranar da ta cika sati uku ta koma dakinta, rawar jiki ba irin wadda Mk bai mata ba. Sun tabbatar sunyi missing juna, irin wadda ba su taba yi ba! haka suka cigaba da rainon dansu cikin tattali, da kulawa mai yawa. Surayya Dahiru ✍🏼✍🏼✍🏼 19/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 59-60 Irin kulawar da MK yake yi wa Sa'adah da danta, yasa take mamakin da ake cewa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157