Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ba zan saurara wa duk wadda ba shi da gaskiya ba". Ya kalli Sa'adah da take gurfane a lullu'be cikin lafaya, "Sa'adatu duk da ba na fatan matsala, amma duk abin da ya taso na rashin jin dadi, ni ne Babanki, ni za ki fadawa kar ki ji nauyi ko kunya, waya kawai za ki mini, ni kuma zan miki maganin ko mene ne, domin duk girman Mukhtar yaro ne karami a idonmu, na san kuma mun isa da shi". Baffa dai bai ce komai ba, da'di ya cika zuciyarsa, Allah Ya kai Iyarsa cikin ahalin da suka san mutunci suke kuma rama shi da alheri. Bai ce komai ba sai da suka mike, ya kalli Mukhtar ya ce, "Ban baka aure ba sai da na tabbatar kana da nagarta, ina kuma zaton kai din adali ne saboda ka siffantu da kyawawan dabi'u don haka ni ba na shakku a kanka. Sai dai kar ka bari jan kunnen da ake ta faman yi maka na ka kyautata mata, ya yi dalilin da za ka bari ta yi abin da ta ga dama, ka bude kunne ka ji ni sosai. Duk 'kawa ko makwabciyar da ka ga dabi'arta ba ta yi maka ba, ka shata wa matarka layin mu'amala da ita, idan ka bari ta fi karfinka to kai ne za ka sha wahalarta". Su Baba umaru suka hada Baki wurin cewa, "Ba ma za ta bijire masa ba, ai barewa ba za ta yi gudu d'anta ya yi rarrafe ba, In sha Allah, irin halin gidansu na girma za ta yi ba *HALIN YAU* ba". Aka rufe maganar da doguwar addu'ar zaman lafiya da neman tsari daga sharrin shaidan, da shaidanun mutane. Suka tafi MK ya bisu a baya, yana ta musu godiya tare da fadin duk abin da suka fada zai kiyaye, bai juyo ba sai da motarsu ta bace wa ganinsa. Sannan ya bi bayansu zuwa bakin titi ya karbo gasassun kajin da tun yamma Mahmoud ya yi masa booking, ya hado da yougurt din L & Z da kuma lemon 5alive, yana tafe yana ayyana bai taba ganin nisan bakin titi zuwa gidan nasa ba sai yau. yana isa ya rufe gidan. Kamar a guje ya fada falon! ya tarar da ita zaune a inda suka bar ta, tana rufe ruf cikin lafaya. Gefe daya ya ajiye ledojin hannunsa, ya isa kusa da ita ya tsaya, a zuciyarsa yake ta fadin Alhamdulillah! sannan ya sunkuya ya 'dago ta tare da fadin , "Assalamu alaiki! Barka da zuwa gidanki, ina miki murnar wannan rana mai cike da farinciki". Ta yi shiru, ta kasa amsawa saboda yadda zuciyarta, take a cunkushe da alhinin barin gida. Ya ri'ke hannun ta yana janta zuwa cikin 'dakin da shi ne mallakinta, a bakin gadon ya zaunar da ita tare da fadin, "Haka na ga ana yiwa amare." Yana warware mata laffayar zuwa kafadarta, fuskar ta masa kyau duk da ta kode saboda kukan da ta ke yi. Kusa da ita ya zauna sosai har jikinsu na gogayya da juna ya dan ri'ko ta ya ce, "Kukan na mene ne tamkar ba gidanki za a kawo ki ba, ke da kika yi sa'a a gari za ki zauna duk lokacin da kika so zuwa gida, zuwa za ki yi to menene abin kuka sai ka ce ba gidana kika dawo ba". Tissue ya dauko a kan madubi ya shiga goge mata fuska, yana ta fadin maganganu masu taushi. Ya kalli agogo ya ga tara saura,ya mi'ke ya dauko ledar kajin da ya bar su a falo, sai da ya shimfida musu abin zama sannan ya janyo ta ta sau'ko 'kasa, ya bude ledar ya tura mata gabanta yana cewa, "Nasan tun safe ba komai a cikinki. Taimake ni ki ci" Ya zabura ya nufi kicin ya samo 'yar roba ya wanke hannu sannan ya zubo ruwa a ciki ya dawo, da rarrashi da hikima ya sa ta cin kazar nan, har ta manta ita ba'kuwa ce, dama kuma azabar yunwa ce a cikinta. ya sake lallabawa ya tura mata yougurt, sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya kalle ta ya ce, "Ga toilet nan ki shiga ki yo brush ki dauro alwala" Ya mike yana fa'din ni ma bari na yi alwalar. 'Kirjinta ya buga fargaba ta kama ta yau gata a daren farko da ta ke karantawa a cikin littafai ko ya ya nata daren zai kasance? Har ya dawo tana zaune a inda take. "Kin yi alwalar kuwa?" Shiru ta masa ya tabbatar ba ta yi ba sai ya ce, 'Tashi mana!" Ya sa hannu ya 'dago ta, sai da ya raka ta har kofar bayin da ke cikin dakin sannan ya dawo yana tattare kayan da suka yi amfani da su, ya shimfi'da musu sallaya ya koma gefen gadon ya kishingi'da yana jin matsanancin bege na ratsa shi. A bandakin ta tarar da sabon brush da makilin, sai da ta wanke bakin sannan ta 'dora alwalar sai kuma ta tsaya a bakin 'kofar ta kasa fita. Wata irin fargaba ce ke haniniya da ita. MK da ya ga shirun ya yi yawa, sai ya tashi ya tura kofar ganin ta a tsaye, yasa shi yin turus, bai ce komai ba ya ru'ko hannunta yana fadin, "Ba na son ba'kon yanayin nan da nake gani tare da ke a yau". Laffayar ya mi'ka mata ta fara kokarin na'de jikinta, ya kalle ta ya ce, "kin ga ba sai kin yi wannan na'din ba, kawai ninka ki yafa". Ba ta musa ba saboda yadda bakinta da jikinta suka yi mata nauyi ainun. Ya ja su, suka yi sallar da Annabi ya kwa'daitar da sabbin ma'aurata su yi. Bayan sun idar ya ri'ke goshin ya yi addu'a sosai, tana amsawa da amin a cikin zuciyarta. Suna shafa adduar ya mike ya fita! bai jima ba ya dawo bayan ya rufe 'kofar falon tare da kashe fitila da fanka, kasancewar farkon damina ne yanayin zafi ne. Yana shiga ta kalle shi da gefen idonta saboda yadda kamshin sa ya sake cika dakin da hancinta, ta ga ya sauya kayan jikinsa zuwa farar jallabiya sabuwa 'kal. Hannusa ri'ke da wasu kayan, kai tsaye ya isa kusa da ita ya m'ikar da ita ya cire mayafin ya wurgar da shi, ya zame dan'kwalinta!dogon gashinta da ya sha gyara na musamman ya bayyana, ya kasa cigaba da dauriya ya fizgo ta jikinsa ya sa hannunsa biyu ya rungume ta sosai tamkar zai mayar da su halitta guda. Ba ita ba, shi kansa jikinsa 'bari ya ke yi, 'kamshin man gashinta da na jikinta da kuma nasa kamshin suka hadu guri 'daya suka sake rikita shi, hannunsa sai kai komo ya ke yi a bayanta cikin wani irin shau'ki mai rikitarwa. Ta yi luf a 'kirjinsa jikinta sai 'bari ya ke yana sake rikicewa da sa'kon da ya ke kar'ba. A kunne ya ke rada mata "please hold me Sa'adah, sa hannu ki ri'ke ni don Allah!" Cikin wata irin murya da ba ta san shi da ita ba yake ro'kon. Kunya da tsoro suka sa ta kasa koda 'kwak'kwaran motsi balle ta iya masa abin da ya ke ro'ko. Da 'kyar ta samu ta zame

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});