Chapter 67
Chapter 67
kuma ta ganshi yana taimaka wa kanwarta da ta samu admission zata karanta economics fa? Farida ba tasan komai a new side ba, tunda ita a old side take karatunta, shikuma sai ya rakasu a kokarinsa na kyautata mata kamar yadda take girmama shi a matsayin malamin ta. Shi bai san har anzo anfesa mata ba.😄 Da yamma ya dawo, ya ya tarar da ita goye da Jawad, kayan da ya barta da su ya dawo ya same ta da su. kallo daya ya mata, ya gane bata ci komai ba, sannan bata yi wanka ba. Ya rasa gane wannan masifar da ta 'dorawa ranta, da 'kyar ta bude baki ta ce "Sannu" ya amsa da yauwa ya isa bayanta yana duba Jawad da yake ta Nishi, shi dai ta masa wanka fes yake, sai dai jikinsa kamar wuta. "Kin bashi maganin kuwa? na ga jikin, har yanzu bai sauka ba". Ko kala ba ta ce ba, ya isa inda ledar maganin take ya bude ya ga ba wadda aka taba, bare a sha. Ransa ya baci matu'ka da gaske, ya nunata da yatsa ya ce " Wai ke wacce irin yarinya ce marar mutunci?" Ta yi 'kasa da kanta tamkar wadda ta saduda, yaci gaba da fadin "kin fara kaini bango Sa'adatu, kullum a cikin zullumi nake zaune da ke, masifar yau daban, ta gobe daban, haka ta jibi". "Ai kaci moriyar ganga, sai ka kawo karshen zaman zullumi Mk" ta fada kanta tsaye. A razane ya zuba mata ido, yana kallon ta, itama ta kafe shi da idon da suka cika da 'kwalla ba alamun tsoro ko shakka a cikinsu. Ya kasa cewa komai, dan kuwa a yadda yake jin bacin rai zai iya na'da mata dukan tsiya, abin da baya fatan ya aikata kenan, dukan matar aurensa. Ya mika hannun yana fadin "bani yaron, kai tsaye ta ce "idan kai ka haifar min, ba sai ka 'kwata ba". Ya yi kanta yana fadin "Me kika sha ne? Bari na sauke miki iskancin da kike fama da shi". Ga mamakinsa ko motsi ba ta yi ba, sa'banin da, idan ya mata irin haka take kwasa a guje ta 'buya. Ya isa kusa da ita ya kama kafadunta ya girgiza da karfi har sai da Jawad ya motsa, ya ce " fada min me yake faruwa, me na miki har ya shafi wannan yaron da bai san komai ba?". Tsaki ta ja, tare da fizgewa, ta koma gefe tana sake 'daure goyonta sosai. " What! Ni Kika yiwa tsaki Sa'adatu? abin da kinfi kowa sanin na tsani a mini?" Ai kuwa ta sake jan wani fiye da na farko, sannan tace " ka kashe ni! an maka tsaki Mukhtar". Wani irin shock ya kama shi, a farko da tace Mk gatsal mamaki ta bashi, amma a yanzu da ta ambaci cikakken sunan sai ya gane ashe Mk din a mutunce ta fa'da. " Allah ya tsare ni da kisan kai, duk bala'in da kike nufi na da shi, in sha Allah ba zai same ni ba". "Tunda abin har ya kaimu ga haka, to shikenan! ki yi harkar ki na yi tawa, sauko shi na bashi maganin, sai ki mayar da shi". "Baka ji mai nace tun farko ba? ka 'kwata' a shirye nake da mu karya yaron nan! idan har ni na tsugunna na haife shi wallahi ba zai sha wannan maganin ba". "Ya zuba mata ido, yana jin haushin ta na samu gurin zama a zuciyarsa, ya ce "idan na siyo masa wasu zai Sha?" "Idan na tabbatar da sahihancin su ba". Ya dauki ledar maganin ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba". Bai wani jima ba, ya dawo da su, a wata ledar mai tambarin lamco pharmacy. Ya mika mata, tare da cewa "gashi" ya juya ya fice. Ta dudduba ta tarar da su dinne, illah ledar da ya canja, ta yi 'kwafa ta dankwarar da su. Ana idar da Isha ya dawo, ya tarar da maganinsa akan kujera ita kuma ta shige 'daki ta rufe kofar, Jawad sai kuka yake yi. Ya duba maganin ya tabbatar ba'a bashi ba, ya hau dukan kofar, amma banda kukan yaron ba ya jin komai. Ya kirata ya fi sau hamsin amma tamkar bata gidan. Ya hassalo sosai ya ce "wallahi idan yaron nan ya mutu, ke kika kashe shi, da hannuna zan mika ki wurin hukuma". Sai lokacin ta ce "yi sauri kar 'kuda ya riga ka, wato ka maida ni bagidajiya, ka fita da magani kamar gaske, ka sake dawo min dashi, idona tar yake, bazan bashi ba". A fili ya dinga fadin "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un". Ya fice zuwa dakinsa, yana karfafawa kansa guiwar ya rabu da ita, ai ta fishi son yaron. Karfe shadayan dare ya dinga jin kukan yaron, da farko ya yi biris, amma da ya dinga jin 'ka'karinsa baisan yadda akayi ba sai ganin kansa ya yi a jikin kofar dakin Sa'adah yana bugawa, yana cewa "ki dubi girman Allah ki bude min kofar nan, komai na yi miki, na yarda kimin komai, amma banda yaron nan, ki ji tausayinsa, ki ji tsoron hakkinsa". Har ya gama bilayinsa bata tanka ba, tana jin ta shirya faruwar komai ciki har da rabuwarsu. Cikin ikon Allah, sai Jawad ya sami barci adalilin ta bashi tea, ta bashi maganin zazzabin sa da yake da shi. Da asuba kukan Jawad ya sake tayar da hankalin Mk, ya rasa inda zai tsoma ransa, a take ya kira Hajiyar Bichi a waya, bai fa'da mata komai ba, ya ce dai kwana suka yi Jawad bai yi barci ba. Ba bata lokaci, ta taho,har da garin kunun ko zai dinga sha, tare suka shiga falon, ya dinga kiran Sa'adah amma ta 'ki budewa, sai da taji muryar Hajiya tana cewa"Sa'a, menene yake faruwa ne?" Da sauri ta bude 'kofar, ta fito idonta, yayi luhu luhu, yayi ja tsabar kuka. Ta mi'ka mata Jawad ta zauna a gefe tana kuka tamkar wadda aka yi wa mutuwa. Hajiya ta kalleta, taga ta fita a hayyacinta, ta rame farat daya, ta maida kallonta ga Mk taga shima a firgice yake. Tace ciwon Jawad ne ya susuta ku haka, ko kuwa wata matsalar ce?" Ya dauko maganin ya mi'ka ma Hajiya ya ce "Dan Allah ki bashi maganin nan", ta karba, ai kuwa Sa'adah ta saka uban kuka tana cewa "Kar ki bashi Hajiya". Hajiya ta rasa maganar wa zata dauka a tsakanin su, ta dubi Sa'adah tace "Yi shirunki bazan ba shi ba, fada min me ya faru?" Ta kasa magana sai kukan da take yi mai dauke da shesshekar ajiyar zuciya. Ganin hakan yasa Hajiya ta rufe Mk da fa'da, ta inda ta shiga, ba tanan take fita ba, tana jaddadawa laifinsa ne, tunda Sa'a ba me fitina bace. Ya yi shiru ya dauki laifin da bai yi ba. da lallashi, Hajiya ta samu Sa'adah ta fada mata dalilin da bata son maganin alhalin ba expired suka yi ba. Da rawar murya ta ce " Budurwarsa ce ta siyi maganin, akan idona suka yi zance ta siya ta bayar". Ta karasa cikin gunjin kuka. Dariya abin ya bawa Hajiya, amma sai ta dake, ta dinga salati tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157