Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 94

Chapter 94

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Cikin kukan sosai ta ce "ina fatan ciwon ya shige ni da 'karfi irin 'karfin guguwar iska, idan na yi sa'a ya dangana ni da kusheweta, wata'kila na huta da azabar da nake 'dan'dana da raina a cikin wannan duniyar". Kuka sosai take yi, wadda ya matu'kar dukan zuciyarsa sosai. Ya nisa ya ce "Zan tambaye ki, kinsan na san ki tamkar tafin hannu na, kar ki mini 'karya dan kuwa zan gane ki". Ta tsagaita da kukan, kafin ta bashi amsa ya ce "wa ya baki waya da agogo da kayayyaki a Jawad?". Zuciyarta ta buga ta 'barke da kuka tana cewa "Dan Allah ka fahimce ni, ba fa yadda ka ke zato bane". Ya busar da iskar 'bacin rai ya ce " ok to fahimtar da Ni! ina sauraron ki, warware mini". Da rawar murya ta ce "Tsakani na da Allah! Saurayin Safina ya siyo mata, ita kuma already tana da ita, shine ta bani, akan na bata rabin ku'din ". Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Ina jin ki! A ina kika samo ku'din?" "Zobena 'daya na gold na bata, a hankali kuma zan cika mata sauran ku'din da suka rage tunda ba yawa". Ya yi shiru yana nazarin anya Sa'a za ta shiryu, yanzun nan ta tsara labari tamkar a wasan kwaikwayo ko a littafi? A kausashe ya ce "kuma ya aka yi naga ba sunanta bane akan rasit din siyan wayar?". "Malam! baka lura bane domin kuwa SB aka saka ma'ana Safina Bunkure". "Hmmmm" ya furta kawai ya yi shiru. "Gaskiya na fa'da maka Malam". Yace " idan kina ganin na gamsu ba Sa'adatu Bashir ake nufi ba. to ki fa'da mini, ta ina kika mallaki agogo mai daraja haka tunda English gold ne". Duka na Safina ne, kayan da ka gani kuma siyawa Jawad ta yi tunda Alheri ta samu ba ka'dan ba". Ya ce "alheri irin na 'yantattun Mata?" Jikinta ya hau ' bari ita kam tam ta shige su, kalma 'daya tak da ta fa'da ta wanke ta a zuciyar Mk! ta janyo Mata tashin hankali mai yawa, ta yi amanna har da wannan kalamin suka 'kara fusata shi, ya yi irin fushin da bata ta'ba hararowa zai yi ba, hakanan kalaman sun janyo ya kasa gasgata ta. A daren ta gane tuntu'ben harshe yafi zafi fiye da wadda za'a yi da 'kafa ta fashe. Jin ta yi shiru ya ce "Sa'adatu har yanzu ba ki shirya fa'da mini gaskiyar magana ba, bare na auna naga zan iya miki afuwa ko bazan iya yafe miki ba! Abin da nake son ki fahimta shine, ki daina yaudarar kanki cewar wannan laifin zai wanku a gurina da kwaskwarimar 'karya. matu'kar kin san ba zaki fa'da mini gaskiyar lamari ba to ki daina tunanin maganar zata bi ruwa da sau'ki." "Gaskiya na fa'da maka Malam! ka zafafa ne, ya kamata ace kasan abin da zan iya da wadda ba zan iya ba! ko ban tsira da komai ba, ka gaskata ni mana". "Ki mini adalci! wacce maganar zan 'dauka na gasgata ki akanta, alhalin tunda abin nan ya faru, kike ta canja magana, kin ce Sumayya ta baki, kin ce ta Halimace, kin ce ta Safinace shin wacce zan 'dauka na gasgata ki akanta?". Shiru ya ratsa amma zukatansu sai bugawa suke yi tamkar ana lugude, ya nisa ya ce "ki kwantar da hankalin ki, duk sadda kika yi nufin fa'da mini gaskiya, Ni kuma na miki al'kawarin zan saurare ki, nasan kuma zan sami nutsuwa a zuciyata tunda gaskiya a bayyane take bata bu'katar ado". "Malam na kusa kammala iddah fa, dan Allah " sai ta fashe da kuka fiye da na farko. Yace "Na sani! yau kika fara period 'din ki na uku, me kike jin tsoro?" Ta kasa yin magana, ya ce "Ni ya kamata na yi fargaba, Ni ya kamata na koka, domin zan rasa damata, sai dai na shiga sahun zawarawa, ke kuwa ai baki da damuwa idan har kina sona ai za'bin a hannun ki aka dam'ka shi". Cikin kukan ta ce "Ban son muje ga haka, Ni ka zo ka dauke ni mu koma gidan mu, na yarda kar ka ci abinci na, kar ka kula ni har sai ka gamsu kamin abin da ka huce". Ya ce "matu'kar muna tare kin san ba zan iya wannan jarumtar ba". Ya sassauta ya ce "ki dinga addu'a sannan ki bar komai a hannun Ubangiji. Abin da nake so ki fahimta, wallahi na fiki shiga damuwa da tasku, kawai ni jarumta na fiki saboda kasancewata Namiji! Sannan ba zan ta'ba sauya hukuncin da na yi mana ba, har sai kin fa'da mini gaskiya koda hakan na nufin rushewar farin-ciki na gaba'daya, duk lokacin da kika shirya fa'da mini gaskiyar magana, ki mini magana". Da haka ya kashe wayar gaba'daya. Ta yi sororo da waya a kunnen ta, tana kallon agogo da ya nuna uku da rabi da minti biyu. ' Har aka fara 'kiraye 'kirayen sallah barci bai iya surarta ba, tana ta tufka da warwara, ta yaya zata iya fa'da masa Khalil ne ya bata wadannan kayan? To akan wanne dalilin zai mata kyautar su ta karba? zuciyarta ta shiga harbawa, bare da ta tuno waccan kato'barar maganar da ta yi. Ta yi amanna har da wancan laifin ya sake girmama wannan laifin a zuciyar Mk, sai ta yi kamar ta fa'da masa gaskiya sai ta tsorata, a yadda tasan ya tsani Khalil zai iya 'kararsa ko dan ya ci mutuncin gidansu tunda mahaifin Khalil fittacen 'dan siyasa ne, ita kuma ta hadu da zubewar mutunci a idon dangi dama duniya gaba'daya tunda tasan suna chatting da shi, ha'kika Sa'a na cikin hali irin na canka ca kare. A fili ta dinga fa'din "Allah na tuba! na cuci kaina, son zuciya ya janyo mini 'bacin rai da damalmalewar lamura! Na keta alfarmar shari'a shiyasa na ke 'dan'danar 'bacin rai mai azabtarwa". Tamkar mahaukaciya take surutai, tana sake cewa "Na yi al'kawari idan har na koma 'dakina bazan sake yin wani abu na rashin gaskiya ta kowacce fuska ba, sai da nace wa su Halima ina jin tsoron abin da zai biyo baya ta mini ingiza mai kantu, na biyewa 'kawar zuciyata na gasgata su, waiyo waiyo! Lah ilah ha illah anta subhanaka inni kuntu minan zalimin". Duk akan kunnen Inna take wannan koke koken, da suratai duk da bata fahimci me take fa'da ba, da farko tsorata ta yi, ta 'dauka gwaiguna ne, sai daga baya ta fahimci daga 'dakin Iyah ne, a hankali ta fito, kasancewar Baffah yana Gogel. Har ta isa bakin 'kofar dakin, sai kuma ta fasa, ta juya a zuciyar ta kuma tausayin'diyarta ya fara kamata, ta dinga mata addu'ar samun sassauci a zuciya. Haka kwanaki suke ta shudewa, fargabar Sa'a na sake girmama, ba ta sake tuntunbar Mk ba, sai ana gobe za ta kammala iddarta, duk yadda ta kada billenta ta dinga ro'kon kar ya bari ta fita a matarsa bai ji ba, ya nan akan bakansa sai ta fadi gaskiyar lamari. Washagari ta tashi da zazzabi ga kuka ya ki yanke mata. Inna ta kasa jurewa yanayin da ta ganta a ciki, har 'dakinta ta shiga ta zauna kusa da ita,

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});