Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nan ne wajen zamansa ya tambaya an tabbatar masa nan ne gidan ku, ya yi mamakin yadda, bai gane ke yarinyar wajena ba ce sai a kwanakin nan, kuma ya ga ba kya zuwa makaranta shine ya tambaya lafiya kuwa?" Ya nisa sannan ya ci gaba da fadin, "Na fada masa kawai makarantar ne ba kya so, ni kuma ban takura miki sai kin ci gaba da zuwa akan dole ba, amma ba zan zauna na zuba miki ido ba, aure zan miki! Ya ro'ke ni alfarmar yana son ya zo ya ganki ya ji dalilinki na gudun makarantar alhalin aski ya zo gaban goshi, na amince masa ya zo ba dan komai ba, sai don mutuntani da yake yi, katifar ma da kike kwana a kai shi ya kawo miki ita, don haka idan an yi sallama da ke bayan La'asar na miki izinin ku tsaya a zaure" Kai ta 'daga tare da cewa "To" ya juya ya fice ita kuma ta koma daki tana jin faduwar gaba. 'Karfe hudu da rabi 4:30pm yaro ya shigo ya ce, "Wai ana sallama da Sa'adatu" Daidai lokacin ta fito a ban'daki dan haka ta ce, "Je kace tana zuwa". A gurguje ta shirya cikin tsadaddiyar doguwar riga Coffee Colour ta yi roling da mayafin rigar, ta fesa turare bayan ta shafa powder da wet lips, ba ta cikin walwala don haka ba ta sami sukunin yin kwalliya sosai ba, duk da hakan rigar ta karbe ta, ta yi mata kyau. Dakin Inna ta le'ka ta ce mata, za ta fita." Kai ta 'daga mata ita kuma ta dauki 'yar 'karamar tabarmar da take jingine a dakin ta fita. A jingine ta same shi, ya yi shigar 'kananun kaya, wandon jeans ne mai kalar ba'ki, sai T-shirt fara 'kal an rubuta *PYRAMID* da manyan ba'ki a gaban rigar, zanen dutsen pyramid 'din kuma ta bayan rigar, 'kafarsa dauke da boot farare sai zabga 'kamshinsa na dindin yake yi, sumarshi tasha gyara sai she'ki take yi, yau har farin glass ya saka wanda ba kasafai yake amfani da shi ba, ba ta yi mamakin shi ne Mutarin da Baffa yake bayanin sa ba, saboda ai ya taba ce mata yasan Baffan shi ma. Ba 'karamin kyau ya mata ba, amma da yake haushin sa take ji sai bai wani burge ta ba, sai da ta shimfida tabarma ta ce "Bismillah!" Ta juya ta dauko ruwa, a zaune ta same shi a farkon tabarma ita kuma ta sai ta zauna a 'karshen tabarmar. Da 'kyar ta bude baki ta gaishe shi, ya amsa yana nazarin yadda ta zabge lokaci guda. Kai tsaye ya ce, "Mai ya hana ki zuwa makaranta tsawon sati guda?" Shiru ta yi amma a zuciyarta fadi take na bar muku makarantar sai ku tabbata kai da Farida da sauran staff masu shaidar zur, har Mahdi ya bayyana. Sau biyu yana tambayar ta, ba ta 'dago kanta ba, bare ta amsa mishi. A karo na uku ya yi magana a kausashe tare da cewa "I will not repeat myself!" Cikin turo baki ta ce "Ni ban son makarantar ne na gaji" Mamaki ya kama shi wacce irin yarinya ce wannan? Ka zo shekarar 'karshe a karatunka kuma rana daya ka ce wai ka gaji? Ya zuba mata ido yana nazarinta matsakaicin tsayi gare ta, ba'ka ce amma ba sosai ba, irin su ake cewa wankan tarwa'da, zagayayyiyar fuska ce da ita, mai dauke da manyan idanuwa dara-dara, gashin girar ta a cike, sannan hancinta ya dace da fuskar sai dan 'karamin baki irin na Baby Girl🤩, mai dauke da wushiryar da take 'kawata murmushinta, ga ta kuma da dimples a dukkan kumatunta ko motsa bakin ta yi sai sun lotsa, ba siririya ce ba amma kuma bata da jiki na sosai, sai dai a cike take, 'kasanta ne mai fadi, amma ta sama a tsuke take musamman da ta yi sa'a ba ta da tumbi sai hakan ya taimaka wurin fito da cikakkiyar sura mai birgewa. Shi yasa uniform ke mata kyau tunda sai sun mishi shape sannan kuma hijabin su 'dan mitsil ne. Ya nisa yana kokawa da zuciyarshi, ya ce, "Ban gane kin gaji ba"? Shiru ta yi ba ta ce 'kala ba. Ganin yadda ta rame ya san dole akwai wani abu daya sata wannan borin sai ya tausasa murya ya ce, "Sa'adah what's your problem, mai yasa haka? Ba za ki ji tausayin iyayenki ba, duk wahalar da suka yi sai da abu ya zo gaf, kice ke ba za ki yi ba, ko auran kike so wata nawa ya rage ki kammala sai a miki" Wani malolon ba'kin ciki ya tokare mata wuya, tasan Baffa ne ya ce mishi haka, ta kasa magana amma ranta in ya kai dubu to ya baci. Sai shi ne ya gaji da shirun ya ce, "Tunda gajiya ce kawai dalilinki ai yanzu kin huta tunda kin fi sati kina hutawa, kuma gobe Monday lallai ki shirya ki zo makaranta. Kai tsaye ta ce, "Idan har FGC ne sai dai a kai gawata!" Ta fada kuka na kwace mata, ta sunkuyar da kai tana danne kukan. Shiru ya yi tare da tunanin dalilin 'kin makarantar haka farat 'daya, murya ba amo ya ce "Listen, idan aka canja miki wata makarantar za ki je"? Kai ta 'daga mishi. Ya ce "it's ok but let's talk the reality. Fada mini dalilinki na son barin makarantar ni kuma idan na ji kina da hujja da kaina zan nemo miki wata makarantar na kawo wa Baffa" Ta yi shiru sai shesshe'kar kuka take yi, jikinsa ya yi sanyi zuciyarsa sai kisima mishi abubuwa take yi. Ya dade yana lallashinta da kalmomi masu dad'i har ya samu ta bude baki ta ce, "Akan me zata dinga tsokana ta sannan duk a hadu a ba ni rashin gaskiya? Saboda ita Babanta mai kudi ne, ni kuma nawa talaka? Saboda ita mai haza'ka ce, ni kuma ba ita ba ce? Duk staff kowa ita ya gasgata! amma ni da nake yar class 'dinka, ka kasa kare mini hakkina, saboda ita Bebinka ce, ni kuma ka tsane ni? To na bar mata makarantar ta tabbata a ciki kar ta fita" Mamaki ya yi matu'kar kama shi amma ganin ta hau dokin fushi mai yawa, sai ya tattaro dukkan alhini ya ya'ba a fuska da gangar jikinsa. Ya kira ta, ta amsa ba tare da ta 'dago kanta ba, cikin muryar lallashi ya ce, " Have I ever said I hated you?" Ta girgiza kai alamun a'a sai kuma ta ce. "No, but actions speak louder than words!" A thick silence sweeps the atmosphere! Ya zama speechless, bai yi tunanin irin kallon da take masa ba kenan. Cike da ta'ajibi ya ce, "Kar fa ki zama cikin jerin mutanen da idan an musu gyara yake zama gaba, tunda haka ne na miki al'kawarin ba zan sake shiga cikin case 'dinki ba, wannan bai kai dalilin da za ki bar karatu ba, sai dai idan da gaske auran kike so, ko kuma ba gaskiyar maganar kika fada mini ba." Ta yi shiru ya ce, "Yanzu kin ha'kura za ki koma?" "Amma ai cewa ka yi idan na fada maka dalilina za

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});