Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 137

Chapter 137

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jikin Zainab, itama idonta ya ciko ta kasa ce mata komai, tana tuki tana taya Sa'adah kuka. Da kyar Zainab ta shanye kukan ta ce "Ai Halima tana cikin bala'i ke har Safinan ma, domin dai saurayin Halima ya ki aurenta ne adalilin wastewarsu suke yi. Dake akwai alaka tsakanin su da gidan iyayen saurayin shine aka masta masa amma ko kadan babu kwanciyar hankali a tare da ita. "Ita Kuma Safina har yau dai bata karbi result dinta ba, kiga dai a bayansu da shekaru masu yawa kika shiga makarantar amma kin kammala kin barta". Aure kuwa shiru kake ji sai dai ana nan ana addu'a. Komai lokaci ne. Amma su kam hakkin kashe aure ne ya saka suka kasa samun nasu auren". Cikin kuka sosai Sa'a ta ce "Tabbas su Halima sun yi wa rayuwa ta illah, Amma kuma ai da gudunmawata, yarda na yi da su, sannan nima ina da tawa matsalar, bayan wadda suka cusa min, kawai iza mini wutar suke yi, Amma ni na hura abata. Dan haka na yafe musu, amma bana fatan mua'amala ta sake hadamu, rabona da su tun ina gidan Malam, in sha Allah kuma rabuwarmu kenan domin tarayya da su halaka ce, na rufe babinsu har abada, dan haka kema daina yi mini maganar su". Zainab ta dinga lallashin Sa'adah da maganganu masu taushi, tana nuna mata, ta yawaita addu'ar sau'kin kishi, itama zata taya ta, sannan yadda ta yi maganar a fita mata da shi waje suyi magana a gadarance, amma ya tashi duk da baya jin da'di ya isa ta gane har gobe ita ke jan ragamar zuciyar sa, sai dai dole ya yiwa Farida adalci domin matarsa ce, dole kuma zai sota. Zainab ta nisa ta ce "Dan Allah Sa'adah ki 'dore da kyawawan dabi'un ki, kar ki bari kishi ya mayar da ke 'yar gidan jiya, kin san dai yanzu ba ke ka'dai bace, kuma Wallahi duk son da namiji yake yiwa mace indai ta cika kishi da korafi, fita fit take yi a zuciyarsa. Ke ce uwargida tunda baki yi wani auren ba, dole ki 'dauki hakuri mai yawa. Ki koyi hakuri da juriya, duk yadda kike da mutum kar kiyi zancen abokiyar zamanki da ita mussaman dangin miji, domin duk ranar da abu ya ha'do ku da su, sai sun zayyane mata komai, a hada da sharri ma, daga nan girman ki ya zube a idonta, itama kuma ta sami damar da zata dinga fa'din munanan dabi'un ki". "Na gode miki Zainab! Na sani ke din mai sona ce ubangiji ya sanya mu cikin masu zumunci dominsa". Sa'a ta fa'di hakan a sanyaye. Zainab ta ce "gida zan ajiye ki, ko gidan Anty Sumayya?". A tunzure ta ce "gidan ubana zaki ajiye Ni, ai Ni da gidanta sai ta neme Ni". Zainab ta yi shiru! ta san tana tofawa baza su rabu cikin da'din rai ba. Wasu daga cikin halayyar Sa'a a jinita ne ilimi ko shekaru ba zai sa ta sauya ba, rikici na cikin abin da ba zata daina ba. A Daren ranar Baba Isa ya dawo asibitin ya fa'dawa Mk ranar juma'ah mai zuwa za'a mayar da aurensa da Sa'adatu, amma ta nemi abarta ta kintsa kafin ayi maganar tariya tunda titsiye ubanta ya yi mata, ba dan tana so ba. Ya ce " Na kuma yi mata wannan laminin, dan haka ba zata tare ba, sai ta shirya, wannan umarni na ne". Baban ya nisa ya ce "Soyayya da sanin darajar Dan Adam ne kawai ya sanya Malam Basiru zai sake baka aure a Karo na biyu! Ka sani da ni da mahaifinka ra'ayin mu daya, shawarar mu daya, hakanan neman kudinmu daya, abin da Zan fa'da maka yau, na tabbatar da yana raye a gabansa zan fa'da maka domin ka sani idan ina waje baya ta'ba nuna shine ubanku yana dora ni akan komai nasa matu'kar anan Kano ne, da bashi da dan'uwan jini. To ka saurare ni da kyau ni na karba maka amanar yarinyar nan, idan har ka bari ta wulakanta ina rantse maka da Allah ni ka wulakanta, na kuma tabbatar idan har ka wulakanta ni, zaka wulakanta Kabiru, hakkin abotarmu ba zai bari ka ga haske ba, ko bayan ba raina, ina maka wasiyya akan yarinyar Malam Basiru domin ni dai banga mai arziki a wannan zamanin irinsa ba, Ubangiji ya bashi wadatar zuciya, ya bashi alheri mai yawa, wadannan kuma sune kololuwar arziki". Da tsananin farin ciki Mk ya ce "Na ji Baba, in sha Allah ba zan sake kunyata ku ba, komai zata yi zan yi ta ha'kuri, zan kara hakuri akan ha'kuri. Ya sauko ya durkushe a gaban dattijon ya ru'ko hannun sa ya ce " Baba ina maka shaida baka watsar da iyalin amininka ba, har yau din nan da tsufa ya cimma maka sosai, baka huta da yi mana hidima ba. Ina yi maka fatan samun aljannar da Annabi ya yi bishara ga masu kyautatawa iyalan wadda suka rasu". Jin wannan albishir din ya sake 'karfafawa Mk jiki, domin zuciyarsa ta yi haske. Washagari da safe aka sallame shi. Ya isa gida bisa rakiyar Dr 'Karfi, tarba na mussaman ya samu daga Farida. 'Karfi bai jima sosai ba ya tafi. Mk ya dinga biyewa Farida na yadda take ina ka saka da shi. Ya fito wanka ya tarar da ta ajiye masa kaya a bakin gado, gajeran wando ne tiri kwata kalar ruwan 'kasa, sai farar riga ti.shet ya fesa body spray ya sanya kayan da ta riga ta feshe su da turaransa na Versace. Tawul din da ya dauro, ya dauka ya rataye shi a bandakin, yana fitowa ita kuma ta shigo dauke da tiren kayan abinci. Yana zaune bakin gado yana kallon yadda ta yi masa shimfida, ta fara zuba masa abincin da ya kasance dankalin turawa da miyar albasa sai gashashiyar kaza, gefe yankakkiyar kankana ce jawur da ita, an lullubeta da ledar rufe abinci. Sama sama ya ci abincin, ya mayar da hankalinsa wurin shan kankana, ya kalleta ya ce "zanga ranar da zaki daina bani lemo da safe". Ta mike da sauri tana cewa"wallahi na dafa maka shayin ga su cups nan flask din na manta". Cikin kankanin lokaci ta kawo masa, da kanta ta zuba masa, tunda ba ma'abocin shan shayi da madara bane. Bayan ya kammala ta 'ballo masa magungunansa ya sha. Ya mike ya ce " Bari na sauka na dan kewaya, bana jin ciwo a tare da ni, amma sam jikina babu karfi". Ta ce "hakan ma babu laifi, ko na dauko maka lucozade it will help". Ya kalleta ya ce "Bari na kewayo dai, so nake mu yamutsa shimfidar can." Ya yi nuni da gado. Kunya ta kamata ta yi murmushi, ba tare da ta sake cewa komai ba. Ya juya ya fita. Hakan kuwa aka yi, domin bai wani jima ba ya dawo, hakanan duk yadda yake jin rashin kuzari, sai da ya zartar da kudirinsa. Duk yadda take ro'kon ya bari ya warware sosai, amma bai ji ba. Sai fa'di yake "kewar ki na yi sosai, har addu'a nake na samu sauki na dawo gida, ba dan komaai ba, sai dan na kasance tare da ke". Da'di ya

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});