Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 117

Chapter 117

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*SADIK ABUBAKAR* 93-95. Ana idar da Sallar isha Baffa bai tsaya a shagonsa ba, saboda yadda ya ke zumudin tattauna al'amarin da Mk ya zo masa da shi a yammacin yau, dan haka kai-tsaye gida ya dawo. Sai da ya kamallah cin abincin da aka gabatar masa ya wanke hannu da baki. Ya kalli Inna ya ganta duk a takure tun safe haka ya ke ganinta sukuku. Cike da kulawa ya ce "me yake damun ki ne Salamatu?" A sanyaye ta ce "Ba komai jikin ne nake jinsa ba tsanani, amma lafiya ta kalau". Nan kuwa mafarkin da ta yi ne ya saukar mata da rashin walwala. "Allah ya rufa asiri" Baffa ya fa'da yana kallonta, ta amsa da "ameen a takaice. "Ina tafe da albishir mai dadi wadda na tabbatar zai tsananta jikin nan naki saboda tsananin karfin farin-cikin da zai saukar Miki a zuciya da ma gangar jikin ki gaba'daya". Ta gyara zama ta ce " Ai kuwa kana da Babban goro fari kal Baffan Iyah". Da murmushi ya ce "Abin da muka Dade muna addu'a da fatan ya kasance ne zai tabbata bayan mun debe kauna da samunsa". Zuciyar Innah ta sake takura amma sai ta shanye ta ce "Al'amarin ubangiji ya wuce hakan, yana zartar da komai a sadda ya nufa". "Baffa ya ce "kwarai kuwa komai nufin Allah ne, bana dai kukanmu ya kare domin ubangiji ya nufa zaman Iyah yana daf da karewa a gabanmu, dazun nan Mutari ya zo mini da wannan albishir din, tun yamman na so na fa'da miki, ganin ki wani iri yasa na ce wannan maganar mai dadice bari na bari sai mun zauna". Yana rufe baki ta fashe masa da kuka sosai fiye da wadda ta yi akan auren da Mk ya yi. Kuka sosai ta dinga yi, tana ambaton raini ne zaisa Mukhtar ya iya zuwa gabansa ya ce zai mayar da Iyah a yanzu, bayan ya gama wulakanta ta, ya gama cusa musu ba'kin ciki. Ba dan karfin imani ba da yanzu barin jikinta ba ya aiki saboda tsananin tozarcin da Muutar ya yiwa Iyah har da su, shine yanzu da aka samota da kyar zai dawo ya ce zai mayar da ita, saboda yana ganin komai ya ce maka haka zaka yi masa?" Baffa ya yi shiru yana sauraronta, wannan ne karon farko tun aurensu da ta zauna take fa'da masa magana cikin kara'di da daga murya, kullum harshenta a kasa yake dan haka ya mata uzziri domin ba dabi'arta ba ce. Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka sosai tamkar yarinya karama. Ya ce "Yanzu wannan kukan na menene Salamatu?" Kai tsaye ta ce "Na ba'kin ciki ne, saboda wallahi na tsani duk abin da zai hada Iyah da Muutar, Jawad ne a tsakanin su ubangiji ya raya shi, amma ni kam na rufe babin wannan yaron mai kafirin ri'ko, da 'Kullaci da kuma rashin ragayya". "To kuma idan ubangiji bai rufe babinsa da Iyah ba fa? Ya ya zaki yi ne?" Kafin ta yi magana ya sake cewa na bashi dama ya nemi amincewarta, zan kuma ta ya shi neman yardarta". Ta kuwa sake fasa kuka tamkar wata sa'ar Iyah. Ya hassalo ya ce "lallai kin bani Babban goro fari kal Salamatu! na gode miki, amma abin da zan fa'da miki, 'daya ne, Ni ne na haifi Iyah kuma nine wakilinta, ko da shari'a ta bata damar ta zabi wadda ta aminta da shi, a matsayinta na bazawara, Nima kuma shari'ar bata ba ta bata damar yi mini kwangen biyayya ba, dan haka ba zance miki komai a yau ba, sai ta zo gidan nan a gaban ki zan tambayeta ra'ayinta. Da ra'ayin ta zaku ga matsayata". Haka tsofaffin masoyan suka kwana zuciyoyinsu ba da'di amma Inna ta ta nan kan ba'kanta tana fatan ko zaman mota kar Allah ya sake hada su bare zaman aure, shekaru bakwai yarinya na zaune, sai yanzu tana shirin tsayar da miji zai lallabo ya watsa maneman, kai Muutar ya cika tabbataccen marar kunya, kuma marar mutunci, ta tabbatar zai iya aikata abin da ta gani a mafarkinta sai dai da ikon ubangiji ba da Iyanta ba. A bangaren Sa'adah kuwa ta shanye murnar dawowar Mk, domin sai da suka zauna da Suamayyah ta sake gane ba 'karamin wauta ta yi ba da ta bari ta ji da'din dawowarsa cikin rayuwarta, domin washagari da zata fita zuwa kotu hawaye Sumayya ta dinga yi tana cewa "Iyah yanzu dai da kike da shekaru talatin da biyu ai ya kamata ace kin fahimci ba abin da mace zata ri'ke a duniya sama da martabarta da 'kimarta. Domin kyau da arziki duk suna samun tawaya, amma idan mace ta ri'ke darajarta to ko da tsufa ya yi wa kyakkawar surarta tawaye wannan 'kimarta da ta ri'ke zata bata kariya. Kar ki bari matsananciyar soyayyar da kike yiwa Mukhtar tasa ki kasa gane a yanzu kinfi bu'katar ki yi daraja a maimakon samun son zuciyar ki. Sa'adah da take jin magaganun Sumayya har cikin kanta ta dago ta kalleta, sai ta ji a yau tausayin Sumayya ne ya kamata saboda yadda take ganin rauni da wata irin fargaba a kwayar idanuwanta, tana kuma ganin wata irin soyayya da jini kawai ke samar da ita saboda tsananin karfinta da amincinta. Ta matsa ta rungumeta cikin rawar murya ta ce "Na gode Anti! Ko yau Baffah da Inna suka barmu na san Zan yi kukan rashin ganinsu ne, da kuma adduionsu gare ni, Amma ba na rashin gata ko rashin samun wani abu ba, na tabbatar ubangiji ya zaba mini ke ki zame mini Yar uwa kuma garkuwa domin ya san idan ban samu irin wannan katangar ba zuciya ta tana iya tarwatsewa adalilin jarbawar rayuwata mai zafi ce, Ina tabbatar miki Anty ke ka'dai idan na kalle ki na ga tarin kaunar da kike mini fiye da ta ya'yan cikin sai na yi ta godewa ubangiji domin gatan da ya yi mini mai girma ne". Suka dinga kuka tamkar anyi musu Rashi ne. Da kyar suka rabu Sumaayya ta bita har hanyar waje tana fa'din ki rufe dukkan kofofin da kika san Mukhtar zai gan ki, idan kuma kaddara ta sake hada ku, to ki rufe dukkan kofofin da zai ji kayyawan kalmomin bakin ki domin shi din bai cancanta ba, bai dace da ke ba, shekaru bakwai da Kika yi, ba shi kika tsaya jira ya zo ya miki alfarmar mayar da aurenku ba. kin yi wadannan shekarun ne kawai dan gina Goben ki, da samarwa kai nutsuwa. Sa'adah ta kasa bu'de baki ta yi magana domin kuka ne zai kwace mata mai karfi, saboda kalaman Sumayya tausayi su ke baata. Tana tafe tana yiwa Sumayya addu'a da dukkan ahalinta tana fatan shakuwa da soyayyar da Jawad da Khairat suke yiwa juna ta bisu har girmansu dan su sake hada zuri'arsu ta zama dunkulalliya. Tana isa kotun sai ta sake tarar da shari'ar da ta bata mamaki, mahifin Khalil hukumar ya'ki da yiwa kasa zagon kasa da ta'annati wato (E.F.C.C) ta gurfanar domin tuhumarsa da take yi da sama da fa'di da ma'kudan kudaden da ya wawure a lalitar gwamnati a laokcin da yake shugaban maaikatan gwamnati (Head of

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});