Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 105

Chapter 105

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

janta da hira, har ta dan sake da shi. "Na fadawa Dadi ba zaki tare ba, Ni Kinga nan da kwanaki biyar zan wuce, ke kuma da zarar visar ki ta fito, sai ki bini, abar maganar jere tukun yanzu". "Allah ya nuna mana" Ta fada a hankali. Suka yi shiru. Na dan gajeran lokaci, Farida ce ta katse shirun ta hanyar cewa "Dadi ya baka aure ba tare da ka ce kana so ba anya ba'a takura ka ba?". Tausayinta ya sake shiga jikinsa sosai! a hankali ya kira sunanta ta dago suka zubawa juna ido tsawon sakwanni, Farida ce ta yi karfin halin janye idanuwan ta saboda yadda take jin sonsa na sake dafa duk ilahirin jikinta, yadda idanuwansa suke a jirkice da kuma yadda suka yi ja sun sake jefata cikin matsanancin so. Murya ba amo sosai ya ce "Na yi mamakin da kika yi tunanin aurenki zai zamo mini takura! Tun yaushe muke soyayya da zaki ce na takura?" Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "kafin shigowar Gogel cikin rayuwar ka nasan muna soyayya, amma bayan ta shigo sai ta kashe tawa soyayyar". Ta fa'da cike da rauni sosai. Idan gaskiya zai fa'da yasan ba 'karya ta yi ba, amma dan ya faranta mata sai ya ce "Ba mutuwa ta yi ba dogon suma kawai ta yi, saboda ina ganin bani da halin da zan zo neman aure wannan gidan, Amma da yake ubangiji yasan yadda na ke sonki sai ya 'kaddara mini samun ki a lokacin da na cire rai, idan kinsan farin-cikin da nake ciki da baki yi wannan tunanin ba". Ya nisa ya ce "tunda da bakinki kika sako maganar Sa'adah bari na fa'da miki wani Abu, kin san yanzu bama tare, amma idan ubangiji bai karar da zaman mu ba, zan dawo da ita, kar hakan ta faru a gaba ki ji a ranki kin gaza ne, sosai nake sonki Farida, sannan ba zan boye miki ba itama ina sonta, kaddara ce ta rabamu, Ina fatan wannan ya zama na karshe da za ki sako mini maganarta mussaman akan ina sonta ko saboda ita na rabu da ke a farko, an 'kadddara mini sai na fara aurenta ne kawai". Sosai ta fahimice shi ta kuma gasgata shi, duk da ta ji fargabar da ya ce zai dawo da ita, ba dan ba ta so ba, sai dan kishin da kowacce mace ke da shi akan abin da take so, dan ma ta yi sa'ar na ta kishin mai sauki ne saosai. Ta katse maganar da cewa "Ya Hajiya da Jawad?" My 11 amsa mata suna lafiya. Ta sake fa'din"kun je anyi masa passport din?" "Anyi masa sai dai da alamu visar ki zata riga tasa samuwa, kawai idan ta ki ta zaama ready, zaki taho ne, shikuma Mahmoud zai taho da shi nan da wattanni uku". Yana rufewa ta ce "wallahi ba zan iya ba, kafata, kafarsa, sai dai nima na jira shi, ka riga kasa masa rai, sai kuma ya ga shiru, Ni bama zan iya zama da kai babu shi a tsakanin mu ba, ni ka'dai nasan yadda nake jin yaron nan a zuciyata". Dadin kalaman ta suka kama Mk ya ce "wato saboda Jawad sai ki barni ni ka'dai, baki damu da halin da zan shiga adalilin rashin ki kusa ba?" "To idan hakane sai ka yi kokari mu samu visa tare da shi". Sosai suka sha hira mai cike da 'doki. A ranar ta nuna masa yatsun kafarta guda biyu da suke a tankware , dan kar sai daga baya ya gano ya ji an yaudare shi, sosai ya sake jin tausayin ta, bai san me yasa yake jin tausayin ta ba tun fil'azal, ya yi ammana wannan tausayin ba zai barshi ya zalunce ta ba. Har wajen harabar Adana motoci ta rako shi, anan ma sun sake bata lokaci suna hira. Sai da ya koma gida ya kwanta tunanin ciwon Farida ya zo masa menene (Arthritis?). Da tunanin ciwon barci ya yi awon gaba da shi, yana karyawa kuwa bai zame ko ina ba sai asibitin kwararru na Murtala, ya samu Dr Babangida Bojuwa abokin kaninsa ne Akil, suka gaisa sannan ya nemi alfarmar ya masa bayanin menene ainihin ciwon Arthritics da hanyar da za'a bi a kula da mai fama da wannan ciwon. Dr Bojuwa ya yi murmushi sannan ya cire gilashin idonsa wadda yake taimaka masa wurin gani sosai sabanin da mutane suke kallon tamkar na ado ne. Cike da girmama yayan abokinsa Dr Bojuwa ya ce "Zan maka bayanin da harshen Hausa tunda kai Baban turanci ne, gara na adana turancina da bai fi cikin cokali ba". Da murmushi a fuskar Mk ya ce " kowa a fanninsa gwani ne 'kanina, baka ga takakkiya na yi domin ka sanar da ni abin da ban sani ba?" "Hakane yayan mu". Dr Bojuwa ya ce "A likitance an fassara Arthritics (Ga'ba) da mahadar kasusuwa biyu zuwa sama. Ba iya 'Kashi ke bada abin da ake kira ga'ba ba! Muna da ga'bo'bi da yawa a jikin 'Dan Adam amma anraba su zuwa manya biyu mafi shara wato masu motsi da marasa motsi". Dai-dai lokacin Dr ya nisa sannan ya zarce da fadin "(osteoarthritis) wannan nau'in shine yafi yawa yana farawa adalilin kokewar shimfidar kawunan kasusuwan(articular cartilage) wacce take hana kasusuwa gogar juna yayin motsi, daga karshe hakan na janyo sidewar kawunan kasusuwan da kuma curewar su zuwa 'Kashi guda daya. Wannan nau'in na faruwa adalilin jin rauni a ga'ba ko shigar kwayoyin cututtuka". "Na'aam" Mk ya furta cike da gamsuwa. Dr ya cigaba da cewa "sai kuma na biyun (Rhematoid arthritis) mai farawa da kumburin shingen gabobi, wannan nau'in yana farawa da kumburin da ya zagaye gabobi wanda ya ke samar da ruwan gabobi. Daga baya kuma ya cigaba har ga kokewar shimfidar kawunan kasusuwan. Wannan nau'in na faruwa ne sammakon rikicewar Garkuwan jiki har ta kai suna yaki tare da lalata shingen da ya zagaye gabobi wato(synovial membrane). Cikin nutsuwa Mk ya fahimci Farida na fama da ciwon Arthritics nau'i na biyu wato (Rhematoid arthritis). Dan haka ya ce "Na gode sosai Dr! Na gamsu da bayanin ka, amma me yake kawo wannan ciwon?" Cikin rashin gazawa Babangida ya ce "zuwa yanzu dai an tabbatar tasirin wannan ciwon ya hada da GADO- ana iya gadar wannan ciwon idan an samu wani a ciki dangi yana da wannan ciwon ma'ana yana bin jini. SHEKARU- yawan shekaru na tasiri sosai wurin samuwar wannan ciwo. MATA-Jinsin mata sunfi kamuwa da ciwon Rhematoid arthritis yayin da jinsin maza suka fi kamuwa da (Gouty arthritis). NAUYI- nauyi fiye da kima na jagorantar kamuwa da wannan ciwon, da kuma buguwa a gabobi". Kafin Mk ya yi magana Dr Babangida ya sake cewa "kalubalen da masu wannan ciwon suke fuskanta bayana rad'ad'in azabar ciwon, sun hada da Tankwarewar yatsu, hannu ko kafa, ciwo yayin motsa gaba, kumburi sosai a gabobi, dama daina aikin gabobin gaba'daya". Mk ya ce "Madallah da hazikin Dr! shin wanne shawarwari zaka bani don kulawa da mai fama da irin wannan ciwon?". "To shawarar da zan baka kasancewar wannan lalura kusan ta dindince, ma'ana za'a tabbata ne ana s!han magani. Mafi soyuwa a inganta abincin marar lafiya, a

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});