Chapter 56
Chapter 56
kunnensa". Da haka suka yi sallama ta kashe wayar, da kyar ta samu ta tashi saboda yadda cikin ya mata nauyi sosai tamkar ba cikin fari ba. Watansa bakwai, amma sai a yi zaton a watan nan za ta haihu, duk da cewar watansu takwas da aure. A fili ta ce "Gara ki zo ki gan ni, ki ga yadda na zama". Washegari kuwa bayan azahar sai ga Inna da yar rakiyarta Zainab Ma'aji. Mamaki ya yi matu'kar kama Inna ko kadan ba ta san cikin har ya tsufa haka ba, ta san dai tana zargin ko da cikin tunda rabon da ta sa Iyah a idonta an kai wata biyar koma ya zarce hakan. Ta zauna tana mamakin yadda ta aune ta zama babbar mace komai nata ya bude, da kyar take zama da tashi. Kallon Zainab Inna ta yi ta ce 'Ashe kin kusa zama uwa amma ba labari?" Dariya sosai Zainab ta yi tare da fadin "Inna Ina zan iya hirar haihuwarmu ta fari". Yayin da Sa'adah ta sunkuyar da kai kasa alamun kunya. Zainab ce ta shiga kicin ta hado ruwa da lemo ta kawowa Inna, ta sake komawa ta dauko tiren da ta gani an shirya kayan abinci a kai. Hira suka yi, cikin walwala har Inna ta fahimci sauyin da Iyah ta yi, ta fara yin hankali. Sai da suka zo tafiya, ta fashe da kuka, kamar wata sokuwa. Cike da tarin kauna Inna ta sata a jikinta, tana fadin "Kukan na menene kuma Iyah? so kike ki tayar mini da hankali bayan cike nake da murnar ganin ki cikin nutsuwa da walwala, ko wani abin na damun ki ne?" Cikin kukan ta ce "Ni so nake ki dinga zuwa". Cikin rarrashi ta ce "Wani satin zan dawo, ai yanzu kam dole Baffanku ya bari na dinga zuwa akai akai". Da haka ta lallaba ta suka rabu lafiya, ta raka su har gate bayan Inna ta shiga dakunan ta gani tare da sanya albarka. Suna tafe Inna ta ce da Zainab "Ina murna Iyah ta yi hankali ashe dai da saura, indai ba so take na zama uwar zamani ba, ina ni ina zarya a gidanta?" Dariya sosai Zainab ta dinga yi tana fadin "Mene ne a ciki Inna? Kin san Baffa ne ya hana mijinta barin ta zuwa gida, ke ba sai ki dinga zuwa ba". "Ba ku da hankali" Har gida Zainab ta raka Inna sannan ta tafi gidansu. Allah- Allah Inna take yi Baffa ya dawo ta ba shi labarin Iyarsa ta kusa zama uwa. Tunda su Inna suka tafi, ta debo kayansu da ya wanke jiya, ta zauna ta fara guga. Ta kammala nasa tsab ta-ci karfin nata, ya dawo. Ta fara kokarin tashi ta karbe shi, ya tsaya daga inda yake ya bude murya ya ce "Yi zamanki ki ji da kanki". Ta koma ta zauna tare da cewa "Sannu da dawowa" Bai amsa ba ya shiga kicin ya ajie ledar hannunsa, ya zubo abinci a plate, tare da cokula biyu. Gefe kuma ya wanko guiba ya zubo a bowl. Yana zama tun kafin ya yi magana ta sa hannu ta dauki gwaibar ta fara ci. Ya kalleta ya ce "Sau nawa zan ce miki ki daina gugar nan idan na sami dama zan yi?" "To ina zaune haka ai bai fi motsa jiki ba, ni fa har wankin ma zan iya mana, kawai dai na bari ne saboda ka ce ba ka so. Ya zuba musu abincin, yana fadin mun yi Ba'ki ne yau, ko kuma wani abin za mu yi da daddare?" Tana murmushi ta ce "Yau babbar bakuwa muka yi baka nan" Ya zuba mata ido cike da neman karin bayani. "Inna yau dai Allah ya nufa ta zo" Da sauri ya ce shine baki fada mini za ta zo ba?" "Ni ma fa ban sani ba kawai ganin su na yi ita da Zainab". "Ba ni labarin yadda ta kaya, kin saka hijabi kin boye cikin?" Tana dariya ta ce "Ban saka ba, amma dai na ji kunya ba kadan ba, ita fa ba ta san ya girma haka ba". Shi ma cikin dariyar ya ce "To me kika ba su da za su tafi?" "Ban basu komai ba". Ya rage fara'a ya ce "Kai Iyah don rowa?" "To ai na ga farkon zuwa na na kai mata atamfa da sabulai, zuwan da na yi na karshe ma ka ba da kayayyaki na kai mata, yanzu ni kuma ba kudi ne da ni ba". "Kudin da yake cikin durowa a dakina fa?" Ya tambayeta yana kallon ta. "Uncle ai ban fada maka zan taba ba, sannan kuma cewa ka yi na sayayyar kayan Baby ne". "Daga yau ban miki iyaka da komai nawa ba, akan su Hajiya da Inna, komai kika ba su ba zance don me ba?". "Tom shike nan na gode zan gyara". "Ina ta cin abinci baki sa hannu ba?". "Ci abinka ni kunu zan sha, dazu Zainab ta taya ni muka yi". "Kwana biyun nan ban san me yasa ba na son shinkafa ba". Sai da ya kammala cin abincin ya tashi ya zubo mata kunun a katon mug, sannan ya jona gugar ya ci gaba da yi. Suna zaune aka fara kiran Magariba, daidai lokacin kuma ya kammala musu gugar gabadaya. Ya yi alwallah ya nufi Masallaci, ita ma ta tashi da kyar ta yi alwalar. Kafin ya dawo ta shirya kayan su cikin durowa, ta tattare falon, ta kunna turaren tsinke na Touch Me. Haka kwanaki suke ta shudewa har watan haihuwa ya kama, komai na Sa'adah ya sake canjawa, fuskarta, ta yi wani iri, hanci ya bude sosai, baki ya zama kato tamkar ba Sa'adah yar kwalisa ba.🤣 Ita da kanta ba ta son ganin fuskarta a madubi, MK idan ya kalle ta dariya take bashi, amma ba ya iya dariyar a gabanta, tun kwanaki da ya kalle ta ya fashe da dariya, ita kuma ta saka masa kuka mai tayar da hankali, da kyar ya shawo kanta, shike nan bai kara ba, sai idan ya fita ko ya shiga dakinsa ya yi mai isarsa. Ranar Alhamis da yamma ya isa gidansu, bayan sun gaisa da Hajiya Babba, ya tambaye ta yadda za a yi akan sayayyar kayan haihuwa. Ta kalle shi da kulawa ta ce "Haihuwar ta matso ne?" Ya ki tankawa. Ta yi murmushi ta ce yanzu fa an daina wannan ala'adar, a yi sayayya amma wai sai ranar suna da a ba da kaya, kawai ku je ku sayo kayanku, ku ajiye Allah ya raba su lafiya". A zuciyarsa kawai ya amsa, ya mata sallama ya yi dakin uwarsa!ya mata bayanin yadda suka yi da Hajiya Babba. Ta ce "Shike nan a yi yadda ta ce din, ko ka hada su da Samira ta raka ta, tunda ku ba ku san mai aka fi bukata ba". A gidan ya ci abinci kasancewar daga makaranta ya zarto, sannan ya musu sallama ya tafi. Haka kuwa aka yi tare da Samira suka je kasuwar kayan jarirai ta asibitin Nassarawa suka zabo kayayyaki daidai misali, wadda za a fi bu'katar su. Ganin kayayyakin nan ya karawa Sa'adah kaguwar ta haihu, da MK ya dawo ya ga yawan kayan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157