Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 153

Chapter 153

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Baffah ya ce "Mayar da wukar ki Salamatu! Bata hanyar banza suka same shi ba, ni dama ina da kyakkawan Ya'kini a ziciyata baza suyi hakan ba". Takaici ya kama Inna ta shige daki ta barshi da Iyah, tana Jin irin rarrashinta da yake yi, tamkar ba abin ayi mata kashedi ta yi ba. Ranar juma'ah Mk da kansa ya zo ya dauki Sa'adah! A mota sai kuka take yi. Sai da suka zo kofar famfo ya ce "Fisabidillahi kukan nan na menene? Na ro'ki karki bata mini Rai". Tara saura suka isa, taga irin daular da aka shirya mata, ta rungumo shi tana ta fa'din thank you Malam"!. Ya ce "ki yi hakuri ban samu damar yi miki lefe ba wannan karon ma, ki bini bashi, idan komai ya dai-daita zan yi Miki" Kwana suka yi cikin farin-ciki mai yawa ha'din kai da soyayyar da Sa'a ta nunawa Mk yasa ya dinga hawaye ba tare da ya san yana yi ba. Da sassafe ta tashi ta shirya masa irin kunun gyadan da tasan yana so tare da wainar rogo mai dadin gaske. Ya tashi ya ganta ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar shaddar da ta karbeta, cikin jikinta ya' kara mata kyau da yarinta. Ya dinga kallonta, a zuciyarsa sai faman godiya ga ubangiji yake yi. Ta ce "wannan kallon fa? Ka tashi ka yi wanka ka zo mu karya ni wallahi yunwa nake ji". Ya diro daga gadon yana cewa "zo muje ki tayani wankan". "Ni na riga dana shirya dan Allah ka yi sauri ka fito". Ya wuce toilet din yana cewa to 'Ranki ya da'de". Cikin kwanaki ukun da ya yi a gidanta wadda shari'a ta bashi, ba karamin soyayya ya nuna mata ba, ba irin rawar jikin da bai mata, shekarun bakwai din da suka shafe cikin tashin hankali da ba'kin ciki sai da ya wanke musu a cikin kwanakin, har Sa'adah take mamakin maganar Innah da tace idan ta yarda da shi kafin ta tare, ba zai yi 'dokinta ba. Ga mamakin Mk ranar da zai koma wurin Farida yini ya yi cikin zullumin kada Sa'a ta botsare, amma har 'karfe shida na yammaci ta biye shi suna ta harkar arziki. Da zai tafi, ya rungumeta ya ce" idan na yi sallah zan wuce gidan Hajiya, zan kaita unguwa wata'kila kafin na dawo kin yi barci". Ta ce "ba damuwa ma hadu da safe". Da'di ya kama shi, ya dinga kissing 'dinta. Suka rabu 'kalau, yana murnar addu'ar da yake yi mata na samun sau'kin kishi ya fara ganin tasirinta. Yayin da ita kuma tana sallah tana kuka, tana ro'kon ubangiji ya sassauta mata kishi, ya bata jarumta da ha'kurin danne shi. Kwananta hudu wata babbar motar daukan kaya ta zo shake da kayyaki, yini guda aka yi a bagaren Farida har washagari suna fama. Ranar da juma'a kuwa wadda yayi dai-dai da satin Sa'a daya a gidan Mk ya dauko Farida da kansa. Kai tsaye bangaren Sa'adah suka yada zango, cikin 'karfin hali ta karbe su, ta gabatar musu da ruwa da lemo har da abinci. Cikin son K'ulla alaka a tsakanin su, Mk ya ce " kin zuba mana abinci tare, ke kuma kin koma gefe, dauko cokali kawai muci tare". Ta daure ta ce "Na riga da na ci tun 'dazu". Kallonta kawaya yi ya gane bata ci ba, sannan kokawa kawai take yi da zuciyarta. Dan haka sai ya mike ya dauko mata spoon din da kansa. Ta karba suka ci dukkansu uku a plate 'daya. Ba magana sai karo a tsakanin cokula da plate. Sai da suka kammala ya yi musu addu'a! Sannan ya roke su arzikin su zauna lafiya da juna, bayan ya tabbatar musu zai yi iyayinsa ya yi adalci a tsakaninsu, ya tabbatar musu dukkansu yana sonsu dan haka ba wadda zai musgunawa da gangan, ranar da aka samu akasi ya 'batawa wata, to ta yi masa uzziri yau da gobe ne, sannan dole idan ana tare dole a fuskanci matsaloli, sai dai kar a bari matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba. Ya nisa ya kalli Sa'adah da kanta yake 'kasa ya sassauta murya ya ce" Sa'adah ta dago ta kalle shi sannan ta ce "Na'am"! "Ku fa'da mini tsarin da ya muku wurin rabon kwana" A sanyaye ta ce "Farida fa'di yadda zai yi". Cikin nutsuwa Farida ta ce "Majority anfi yin kwana biyu, mu barshi a hakan mu ma". Ya sake kallon Sa'a ya ce "Hakan ya yi miki?" Ta amsa da "eh" a hankali. Ya sake yi musu nasiha tare da shawartarsu su sanyawa ransu zaman ibada zasu yi, yin ibada tsabtatacciya kuwa sai mai hakuri mai kuma Imani na gaske. Ya mi'ke yana cewa Sa'aadah "muje ki yi mata rakiya". Ta bisu ba dan tana so ba, sai dan kar ya ga gardarmarta. Da gaske ta dauki aniyar canji. Suka isa bangaren Farida da ya 'kawatu da kaya na garari. Duk yadda Sa'adah ta yaba haduwar bangarenta, da ta ga yadda aka narka dukiya a wurin Farida sai da ta girgiza matu'ka da gaske. Jikinta ya sake mutuwa, bata fi mintina biyar ba ta mike tare da cewa"Allah ya sanya alkhairi". Itama Faridan ta mike tana cewa "zo mu shiga mu ga gidan sosai mana". Akan dole Sa'a ta bita, ta ga 'dakunan da suke falon wanda 'daya tsarinsa ya tabbatar mata Jawad aka shiryawa dakin. Akwatuna da ta gani guda uku set, masu tsadar gaske, ya tabbatar mata kayan fa'dar kishiya Mk ya yi mata, Amma ita ko akwati 'daya bata samu ba. Sai dai take ta tuno milyoyin da ya kashe mata, sai ta yarda ta kuma gane ba laifi ya yi ba. Ta riga ta gamsu Mk bai kai 'karfin da zai zuba irin wannan kayan ba, ta kuma yarda idan har yana da ku'din yin hakan to ita zai fara siyawa. Suka gama da dakunan suka yi kicin da yake shake da na'urorin zamanin da ba zasu lissafu ba. Sa'a taki yarda da shiga dakunan su na cikin corridor wadda ta tabbatar sai ya ninka na falon 'kawatuwa. Tunda dakunan Farida da Mk ne. Har bakin kofar Farida ta rakota sannan ta juya ganin Mk na waje, ta sani rakiya zai yi mata, tunda wurinta yake ma'ana Faridan ce mai girki. Sa'adah tana ganin Mk ta wuce shi fuu tamkar bata ganshi ba, ganin haka ya bita yana 'kiranta amma bata tsaya ba. Har suka isa bangarenta, ta zauna a falo ta fashe da kuka, jikinsa na rawa ya ru'kota, ai kuwa ta dinga dukansa ta ko ina, ganin dukan ba mai illah bane, sai ya sunkuya mata sosai ta yadda zata ji da'din dukan nasa. Sai data gaji dan kanta sannan ta barshi, shikuma ya janyota ya rungume. Ya dinga karfafa mata guiwa, tare da zugata, har ya samu ya zagwanyar da rikicin da ya taso mata. Sai da ya kaita har 'dakin barcinta, ya jira ta yi wanka, ta kwanta ya lulluba mata bargo. Sai a lokacin ta ce "Malam" ! Ya amsa Mata da cewa "Na'am my dear Iyah"! Cikin rauni ta ce "Amana dai itace amana! Haka cika alakawari sai mai Amana, kar ka bari a kwace mini kai,

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});