Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 92

Chapter 92

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dauko hijabin ta da ke rataye a bakin 'kofa ta saka tana tambayar Jawad wa ya kawoka? Yace "Malam ne", ba ta zauna ba ta dauko tabarma ta shimfida a inda ta saba shimfida masa, tana ayyana tasan zai shigo, aikuwa kafin ta dago ta ji sallamarsa. Ganin Sumayya lullube ta ke da mayafi, Sa'adah ce kawai a zaune ba mayafi daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda wuyan ya mata yawa tsabar rama, kanta ba dankwali asalima tsifa take yi, ga tulin gashinta a gefen ta wadda ya ke zuba tamkar wutar daji. Inna ta amsa masa tare da bashi iznin shigowa, Sa'adah da tun jin sallamarsa ta daskare a zaune, ta rasa me za ta yi duk kuwa da yadda Jawad ya saki Ayman ya zo ya haye cinyarta yana taba wuyanta, alamun ramar da ta yi shima ta bashi mamaki. A hakan Mk ya shigo, idonsa ya fada cikin na Sa'adah, gabansu ya buga a tare da azama ya dauke idanuwan sa, ya isa ga tabarmar da yasan dan shi aka shimfida, a ransa ya dinga godewa ubangiji da 'kaddare shi ya shigo, da ya kunyata Inna. Suka gaisa cike da kunya da girmamawa tamkar komai bai faru ba, haka suka gaisa da Sumayya. Da Sa'a ta gaishe shi ya amsa mata ba yabo ba fallasa, amma yanayin da ya ganta ya matu'kar bashi mamaki da tausayi, mussaman da ya ga Jawad ya lafe a jikinta. Ba ta ji kunyar Inna ba, bare Sumayya, ta ajiye Jawad ta mike ta dauki hijab ta bi Mk hanyar waje, a zaure suka tsaya, ya zuba mata ido, bai ji so ko tausayin yadda ta lalace ba, domin tare suke shan bakin cikin, kawai dai shi Namiji ne, namiji kuwa da juriya aka san shi. Ya daure ya ce "har yau ba ki fara cin abinci bane? kin ga irin ramar da ki ka yi kuwa?" Hawaye ya 'balle mata ta ce " Ka yi hakuri , na 'kira Jawad ka tafi da mu, ka mayar da ni gidanka, ba sai ka kulani ba, zama tare da kai 'karkashin inuwar aure ya gamsar da Ni". Ya yi murmushin da babu nisha'di ko kadan yace " ba kya yawan addu'a, ki nemi zabin Allah a tsakanin mu, ba son rai ba, sau da yawa mukan so abu 'kololuwar so, sai abin ya zama sharri ne a garemu, hakan nan muna 'kin abu iyakacin 'ki, sai ya zama alheri a garemu". "Kar ka kwatanta ni da sharri Malam, ina hadaka da girman Allah ka yi hakuri ka yafe mini". Ta tsugunna guiwa biyu a 'kasa Ta cigaba da cewa "saura 'kiris na kammala idda, ka taimake ni, ka ji 'kaina." Daidai lokacin Baffa ya shigo zauren ya kewaye su ya wuce ba tare da yace uffan ba. Jikin Mk ya yi mugun sanyi, bai so Baffa ya gansu a haka ba, ya dubeta ya ce " ki koyi karban rayuwa a yadda ta zo miki, ki kuma daina wasa da damar da rayuwar za ta baki, na so ki, iyakacin so, amma menene amfanin son da babu kwanciyar hankali ko aminci a cikinsa?" Da haka ya juya da sauri yana fadin "ki yi murna kin zama 'yantacciyar macen da ki ke fata". Ta jima tana kukan zuci da na fili, sannan ta shiga gidan, ba ta tsaya a tsakar gidan ba ta shige daki ta kwanta tana cigaba da rizgar kukan da ba ya amfana mata komai. Ganin wulgawar Jawad ya dan rage mata kewa, ga Sumayya da take tausarta. Ranar lahadi suna zaune, Sumayya na mata kitso bayan Ahamad 'kanin Mk ya zo ya tafi da Jawad, kawai suka ga ana ta shigo da kaya, kallon su kawai Sa'adah ta yi ta fahimci kayan ta ne Mk ya Aiko musu, tunda ya ga an'ki zuwa a debo. Abin mamaki sai ba ta ji kuka ya zo mata ba, ko dan ta yi kukan har ta gaji ne? Tsakar gidan sai da ya cika da kaya, domin duka gadajen nan uku ya Aiko mata haka nan kujerun falo da tv plasma hatta freezer da bai 'dade da siya ba, ya ha'da ankawo mata. Ga wasu bakko guda uku sha'ke da kaya, Sumayya ta bude biyu duka kayan Sa'adah ne, ya yin da 'dayar labulaye ne da zannuwan gado a wanke a goge, sai lokacin 'kwallah ta zowa Sa'a, wato ya da'de yana shirya mata kaya, tunda ga labulayen da suke dakunanta ma ya cire su anwanke su. Haka akwatunanta duka kayanta ne a ciki, ba kayan da ba' a wanke an goge ba, a cikin fishi ma Mk ya iya alheri, ta ayyana a ranta. Gwala gwalan ta ne kawai ba ta gani ba, indai ba a tsakiyar kayan ya 'boye su ba. Ilai kuwa cikin katon akwatin ta ya saka mat su a tsakanin kaya. Dukkansu jikin su ya yi sanyi da ganin kayan, hatta Baffa da yake nuna mata bai damu ba, ganin wannan kayan ya tayar da hankalinsa, balle Inna da take ta faman goge hawaye a fuskarta. Ganin hakan Sumayya ta roki Baffan su, za ta tafi da Sa'adah Gombe, ta kwana biyu, idan ta 'dan warware sai ta dawo. Ya kalli Sumayya, a sanyaye ya ce "kin manta ba ta kammala iddarta ba? har yanzu a matsayin matar Mutari ta ke, bani da ikon da zan turata wani guri alhalin ba hakki na bane yin hakan". "Baffa dan Allah ka bari mu tafi, mutumin nan, ba mayar da ita zai yi ba, gaba'daya ya fita a kaina wallahi". Murmushi ya yi ya ce " Ban sanki da son zuciya ba, Sumayya! Kar son 'kanwar ki ya mayar da ke mai son kai, kinsan me ta shuka masa ne? Ruwa ba ya tsami banza, har yau ya 'ki fadan me ta yi masa, maimakon haka sai ya 'dorawa kansa laifi, Ina rantse miki da Allah! Iyah ce ta yi wani abu marar 'dadi, ko shekaranjiya na ganta durkushe a gabansa, Ni na fara tsoro da wasiwasi akan lamarin ta, Allah dai ya sa ba wani mugun abu ta yi ba" Sumayya ta kasa magana, tausayin Iyah na ratsa ta. Ko da shiga dakin a zaune ta sameta, ta tsurawa gefe 'daya ido, idonta a soye, sai da Sumayya ta kirata sau uku sannan ta amsa a firgice. "Ki fa rage dogon tunani Iyah Ina jiye miki ciwon farat 'daya. Ta dago ta dubi 'yar'uwarta ta ce "Dama na mutu Aunti". Da sauri Sumayya ta ajiye Anis ta 'karasa kusa da ita ta rungumeta ta ce " idan ki ka mutu, ki barni da wa Iyah? ke ka'dai gare ni bayan Innah, ko da na haifi mace ba zata cike min gurbin ki ba, bare ban haifa ba, me yasa ba za ki duba wadda farin cikinsu na 'damfare da ke ba? Yanzu Mukhtar din da ba ki san shi ba sai da kika mallaki hankalin ki ne, zai sa ki yi fatan mutuwa ki bar Baffah, ki bar Inna, ki bar Jawad, ki bar Ni?" Sai lokacin kuka mai ciwo ya gocewa Sa'a. Sumayya ta cigaba da cewa ki fauwalawa Allah lamarin ki, ina tabbatar miki zai kawo miki mafita, ki ha'kura da Mukhtar yadda ya ha'kura da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});