Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ance da Safina 'daga kai, sai ta hango Farida Torondi, da Uncle Mk na Sa'adah, da wata da bata ganeta ba. A hanzarce ta zunguri Halima da hankalinta ke kan waya ta mata nuni da abin da ta gani. "Munafiki dama ai nasan cin amanar Gogel yake yi, marar mutunci, ba dama aje gidansa ya dinga 'dacin rai da muzurai kenan, banda rashin gaskiya, menene na zargin mutane suna zuga maka matarka, ai dan yasan yana rashin gaskiya a waje ne". Kafin su kammala, har su Farida sun gama sun fice tare da Mk. Halima so take su wuce gidan Sa'adah, yayin da Safina tace ita ba zata iya zuwa ko'ina ba tare da taci abinci ba, dan haka suka zarce capteria. Anan ma suka sake yin tozali da Mk da su Farida suna cin abinci suna hirar su cikin nisha'di. Suka kewaye su, suka tafi can baya suka zauna, ta inda su Farida baza su gansu ba, yayin da sukuma idonsu na kan duk motsin su, suna daukarwa Sa'adah rahoto. Halima fadi take "wannan mutumin mugune, ya rufe yar mutane ya hanata fahimtar komai. ashe shi yana nan yana sheke ayarsa" Safina ta furzar da hucin takaici tace saboda Allah kiga ya hanata karatu, shima daf yake da ya kammala Masters dinsa, (Jami'ar ce ta dauki nauyin karatun nasa). Sannan yana tarayya da mai yin degree a fannin hada magunguna (pharmacy), above all daga rich family ta fito, oh Allah sarki! na tausayawa poor Sa'adah". "Ka'dan kenan a sharrin namiji" inji Halima da take jin tamkar taje ta rufe su da duka. Suna zaune suka ga su Mk sun mike, sun fita, a motarsa ya 'debi su, kuma Farida ce ta shiga gaban motar. Ba'kin ciki ya kamasu da gaske suka ji, suna taya kawarsu kishi, Safina tace "takaici na daya, da bamu samu damar yiwa Gogel bidiyon su ba". Halima ta amsa da cewa "wlh kuwa basirar yin hakan ba ta zo mana ba" Daga capteria, basu zame ko ina ba, sai gidan Sa'adah, suka kwashe komai suka fa'da mata, a kokarinsu na tserar da ita daga cin amanar namiji, ita kuma bata gane duk mai zuwa ya fa'da maka abin da zai ruguza farin cikin ka, ba masoyi na hakika bane, mai sonka idan yaga abin da zai tayar maka da hankali! 'Boye maka yake yi mussaman a fannin auratayya tunda dai kowa yasan namiji is entitled to 4 wives, dan angan shi da budurwa matu'kar ba ba'dala suke yi ba Ina ruwan ki? Kuka ta dinga yi, tana fa'da musu kwanaki biyun nan wulakanci ya ke tata mata, ya tsiri ya yi wanka da magariba ya she'ka kwalliya ya ce mata ya tafi shago, ba zai dawo ba sai after 11. Suka hada baki wurin cewa "karya yake miki ba wani shago, wurin Farida yake zuwa, yau munga zahiri". Safina da ta fi Halima kishi tace duk ranar da ya wuce goma na dare bai shigo ba, ki rufe gidanki, ya koma can su kwana tare, ai dan ya ganki sanyi kalau ne ya samu damar yin wani abin" "Wallahi kisan me kike ciki akan makaranta, baya son ki dinga ganin mai yake yi, shiyasa yake ta miki yawo da hankali akan karatunki, oh mai za'a yi da irin su Mk". Ita dai banda kuka ba abin da take yi, tana jin wani irin kullutu ya tokare mata wuya da zuciyar ta, ya sababa mata nauyin kirji, da kyar take zuko numfashi. Haka suka tafi suka barta da kunan rai, suna jaddada mata tasan matakin dauka akan mijinta🤔 Wawiyar kuma ta cika fam! tana jin yau ko yafi gyatumarsa kokari, ba zai yaudare ta da kalamansa na yaudara ba, ya maida ta wata nympho, da sun fara rigima sai yasan yadda ya yi suka kusanci juna shikenan sai ya kashe fa'dan, da zarar ya hau samanta bata sake tuna komai na bacin rai a tsakaninsu. Ta ci kukanta ta 'koshi bayan tafiyar su, sai ta yi dabarar fara karatun kura'ani dan ta sami sau'kin 'kullutun dake neman fasa mata zuciya da makoshi. A haka ya dawo ya tarar da ita, ta sami sau'kin bacin ran da ta ke ji. Kusa da ita ya zauna yana sauraron kira'arta mai dadi, sai da ta kai Aya. sannan ta ajiye kura'anin ta mike tace "sannu da dawowa". Ya amsa da "yauwa! Na gaji yau dinan sosai, na sha zirga zirga, ba tare da kalle shi ba, tace " wata'kila har wanka ya hau kanka". Zuciyarsa daya ya ce "gaskiya kam idan na yi zanfi wartsake wa", ya kalli agogo ya ce bari na yi sauri na watsa ruwan kafin a kira sallah". Ya mike ya yi dakinsa, ita kuma ta bishi da kallon tuhuma, da takaici mai yawa. Da ya dawo bai nemi abinci ba, ta kara gasgata su Halima, ya taba jikin Jawad da yake kwance yana fama da zazzabin hakorin fi'ka, ya kalleta yace a kwance ya yini ne?" Kai kawai ta daga masa, ya riga da ya saba da halinta na rashin bashi amsa da baki wani lokacin, dan haka bai damu ba. Wani ikon Allah yau da wuri ya dawo, kamar yasan anshirya masa ya kwana a waje, haka suka kwana bai gane kan gimbiyar ba, ya daure, shima ya 'kyale ta. Washagari suka tashi Jawad yana ta suma! ga wasu irin abu sun feso masa kamar borin jini, asibiti suka kai shi, aka bashi magaunguna bayan anmasa allurai, sunje siyan magani, suka tarar da Farida a pharmacy din, da azama ta zo gunsu ta karbi Jawad da yake hannun sa ta dudduba jikinsa tana fadin "Abban Jawad wannan ai 'kyanda ce(measles)". Da kanta ta hado maganin da aka rubuta musu, har ta kara musu da wani sabulu da zai taimaka wurin baje fatar. Lokacin da take yiwa Mk bayanin maganin da yadda za'ayi amfani da su, Allah kadai yasan yadda zuciyar Sa'adah ta ke tafasa, ko da Farida ta karaso fuskar Sa'adah a daure ta gaisa da ita, har Mk yaji kunyar yadda ta mata a gaban jama'a. Ya mika kudin Farida ta ce "A a Uncle ka barshi, da dai na Gogel ne sai na barka ka biya! Amma ai Jawad 'dana ne nima", ta fa'da da sigar tsokana da wasa. Ya yi godiya ta rakasu har mota, ya karbi Jawad a hannun ta, ya mika ma Sa'adah ta hakince a gaban mota, suka tafi. Suna Isa gida bata jira ya gama daidaita parking ba, ta dauki ledar maganin da Jawad ta fice. Tana kwantar da Jawad da yake ta barci tunda aka masa allura, ta samo biro, ta yiwa magaungunan nan shaida ta yadda ita kadai zata gane, ta daure ta ajiye su. Ya shigo ya zauna, yana son yi mata magana amma ganin yadda ta 'daure fuska tamkar wadda ya zagi iyayenta, yasa ya mi'ke yana cewa " na tafi! Dan Allah kar kiyi wasa da bashi magani". Ci kanka ba ta ce ba, ya gaji da tsayuwursa ya fita, yunwar da yake ji dole ya fita da abarsa, dan yasan tunda take wannan fishin ba yi zata yi ba, yasan ganin Farida ne ya sake tunzuro ta, tunda tun jiya take ta faman 'kunci, a ransa yana ayyana da jiya

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});