Chapter 133
Chapter 133
Ya dinga yi masa addu'a yana tofa masa. Har ya gama zamansa Mk bai farka ba, ya isa gida ya tarar da Innah a tsakar gida tana yanke farce, ta masa sannu, ya amsa, ya samu gefe ya zauna. Ya nisa ya ce "Mutari ne bai da lafiya rabona da shi yau kwanaki uku kenan, dazu na je shagonsa jin ba'asi sai ake fa'da mini bai ji da'di ba, na je na gano shi, Amma ban ji da'din ganin sa ba, domin gaba'daya yana kwance tamkar gawa. A sanyaye Inna ta ce "Assha Ubangiji yasa zakkar jiki ce". "Ameen dai! Amm an tabbatar mini jininsa ne ya hau fiye da 'kima, na san baya rasa nasaba da bijirewar ku, Ayyah Salamatu ba zaku yiwa yaron nan sassauci ba, ko bai ci arzikin kowa ba, ya ci na tilon 'dansa mana". A sanyaye ta ce "Àllah zai bashi lafiya, Iyah har karamin hauka ta yi, amma da aka yi hakuri ai gashi nan ta mike, har ya zama tamkar ba a yi ba, shima zai tashi ne". Ran Baffa ya fara 'baci da lamarin ta sosai, Amma sai ya mike ya fice domin ya san cigaba da zamansa a cikin gidan yana nufin rikici mai tsanani a tsakanin su, abin da ba zai iya tuna ko sau nawa suka yi a tsayin rayuwar aurensu ba. Sa'a da ke daki take jiyo su, hankalin ta yayi tashin gauron zabi, ta da'de tana wasi-wasin fishi su Dr 'Karfi suka yi, ko kuwa jikin Mk ne har yanzu domin yadda ta ganshi kwance a gaban mota da irin gudun da Mahmoud ya yi ta tsorata. Gashi kwana biyu bata sake jin su ko a waya ba. Hawaye ya 'balle mata, ta tuno sadda yake ce mata, yana jiye mata fargar jaji, yana jiye mata kar 'danta ya zama maraya. Ta kasa fitowa waje dan idan Inna ta ga tana kuka akan Mk to kuwa ta kade har ganyen ta. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Washagarin ranar sai ga Baba Isa sun zo har da su Baba umaru, daga asibiti suke, ganin Halin da Mk ya ke ciki, yasa suka ji tausayi, suka saka Mahmoud ya kawo su, su zo ko Allah zai sa a samu yarinya ta huce . Amma wani abu da Sa'adah ta kasa gane menene ya daure mata baki da zuciyarta, ba abin da take hange sai Mk da Farida cikin mayafi guda, duk tambayar da suke yi mata ta kasa amsawa sai kuka take yi, tana satar kallon mahaifiyarsu. Hade ran da Inna ta yi, yasa ta ce "Na yafe masa, amma ni bana sonsa da aure". Jikin su Baba Isa ya mutu kwarai da gaske, dan haka suka ha'kura domin dai sun san yarinyar ta hadiyi ba'kin ciki kala kala. Ran Baffah bai ta'ba baci irin na yau ba, gaba'daya ya ji Sa'adah da mahaifiyarta sun kunyata shi, sun tozarta shi. A daddafe ya sallame su, ya dawo gida, ya dinga surfawa Inna sababi, yana fa'din "Ban san ladabin karya kika yi mini ba, a tsawon shekarun da muka kwashe ba sai yanzu". Ya nisa ya ce "wallahi Salamatu kin yi 'karko irin na kifi ace wai ke kika raba mini gida zuwa jami'iya biyu, kin hana yarinya zabin zuciyarta, saboda son rai irin naki. Yanzu haka yaro yana gadon asibiti rai a hannun Allah! Tabbas idan ya mutu, ke ce sila, kin bada muhimmiyar gudunmawa wurin kisan rai" Ta fara kuka ta na cewa "Eh ai da yake shi ka damu da lafiyarsa, shiyasa kake akilon samo masa mafita, amma sadda ta dinga zabura tana surutai ai duk ka manta. Ina nan akan bakana bana son Muutar da Iyah". Ya hassalo ya ce "to kuwa ba zan iya zama da ke da wannan bakar zuciyar ta ki ba, har kina iya buda baki kina ce wa wanii mai ru'ko da 'Kullaci, to ke ai zuciyar ki tafi ta kafiran farko ma tauri". Da kuka sosai ta shige 'daki ta fara tattara kayanta tana fa'din "akan Iyah ta komawa Muutar gara na ha'kura da zaman tunda ka ce ba zaka iya zama da ni ba". Sa'adah da take tsaye tana kukan bacin ran yau akanta iyayenta da bata ta'ba ganin sunyi ko da musu ba, suke wannan tashin hankalin. Ta bi Inna daki tana bata hakuri amma ko kallonta ba ta yi ba, sai hawaye take yi, tana cigaba da hada kayanta. Baffa ya shigo ya ce "daina ha'da kayan ki, yau shekaru arbain har da uku da auren mu, kike tunanin dan na rabu da ke zan tura ki gidanku? Ai ni ba azzalumi bane, ba zan karar miki da karfinki da kuruciyarki sannan na sallama ki ba". Ya nisa sosai ya ce "mahaifiyata ita ta sha nono ta barwa mahaifin ki, kenan a ko ina ni mai tsaya miki ne, ba me tozarta ki ba. Ni ne zan fita na barki miki gida, ki yi yadda kike so da yaranki, tunda ni ban isa na yi iko da su ba, kin riga kin zama 'Yar birni, son ya'ya kawai shine a gabanki ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba". Ya sake cewa "ki yi zamanki, ko ban aure ki ba, aike kanwata ce da zan baki 'daki a gidana, bare kuma nine na karar miki da komai". Ya juya ya fice zuwa dakinsa ya dinga ha'da kayansa. Sa'a ce ta ankara da yadda yake ta fito da kayayyakinsa tsakar gida. Ta fito da sauri, cikin kuka sosai ta zube tana cewa "Na ro'ke ka Baffah ka yi hakuri, kar ka bar mu ina zaka tafi ka barmu? Muryarsa na rawa ya ce "ko ina ma zan shiga menene matsalar ku, ina ce yanzu kun yi wayewar da zaku iya rike kanku, ku zartar da hukuncin da ni ne zan yi muku biyayya, ba kune zaku mini ba, saboda kuna gamsar da kanku da uwarku, kyale-kyalen duniya fiye da yadda zan yi muku. Dan haka gara na nesanta kaina da ku, tunda ban isa na ce ga yadda za'ayi a gidana ace mini to ba". Inna da take bakin kofar daki hawayenta ya kasa tsayawa, da sauri ta tsugunna tana cewa "Ka mini hakuri, na yarda na yi kuskure, na yi laifi, ka gafarce Ni, na amince Muutar kaddarar Iya ne, ina fatan ubangiji ya sa karshen bacin ran mu kenan. Ka yi hakuri na ce to, na amince, ka yi yadda kake so da 'yarka". Dadi ya mamaye zuciyar Baffa ya ce "Na gode miki Salamatu! Ubangiji ya kore shaidanun da suke son tarwatsa mana kyakkawan zaman mu". Ya kalli Iyah ya ce "A lokacin da na barki ki yi karatun ki, na tabbatar miki bana so, amma na amince miki dan na yarda alfanu ne a gare mu baki'daya. A lokacin na ro'ke ki duk sadda nima zan zo miki da wata bukata ki daure ki mini biyayya ko da ba kya so, sai dan kin san ba zan dora ki akan abu marar alfanu ko cutarwa a gare ki ba". Kafin ta amsa masa, ya sake zarcewa da fa'din "To yau ina son na roke ki, ki koma dakin ki, burina a duniya bai wuce ace kina dakin mijinki a zaune
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157