Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 150

Chapter 150

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wadda na tsana, Dan Allah baka ji a zuciyarka ka tozartani ba?" Da sauri ya ce " Ni ban tozarta ki ba, domin 'auren da na yi 'kaddarata ne, wadda ko muna tare ba zan iya tsallakewa ba. Ta ture shi ta ce "Ai kuwa zamu rayu a haka cikin damuwa, domin zuciyata ba zata huce ba, har sai ka yarda ka wulakantani, ka mini hukuncin da ya wuce laifina". Ya sake rungumeta tsantsan tamkar zai mayar da ita cikinsa ya ce "Anya mutum yana tozarta zuciyarsa da rayuwarsa? Amma tunda shine abin da zaisa ki yafe mini, shine abinda zanyi ki dawo mini da nutsuwata, to na yarda na wulakanta ki, amma wallahi ba intentionally na yi hakan ba, ki yafewa masoyinki, kamar yadda na yafe miki, ko na tuna abubuwan da kika yi mini, a take nake jaddada cewar Ubangiji ya zama shaidar na yafe miki, ya kuma hane ni tunowa". Da rawar murya ta ce "Ai ni ko ina son na manta din ba zai yiwu ba, a da kai din nawane ni ka'dai, kome zan yi maka na san ba inda zaka je ka kwana zaka dawo gare ni ne, amma yanzu fa? Zan dinga rabaka ne da wata muddin rai". Ta karasa cikin kuka na sosai. Shi kansa da ya tuna bala'in da ya shiga da ya ganta da Khalil ya gamsu ita din jarumace, domin shi akanta ba zai iya shanye abin da ita ta shanye ba, ya dinga ji har zuciyarsa yana taya ta Jin ciwon kaddarar nan da ta kutso musu. Ya Dora bakinsa daidai kunnenta ya ce "Daga yau din nan ba zan sake maimata miki wannan kalmar ba! Ki ri'keta ta zame miki jagora a zaman da ubangiji ya kaddara zamu yi". Ya nisa ya ce "Wallahi ban taba son wata halitta a doron 'kasa irin ki ba, Hajiya ce kawai ta fiki darajah a duniyata. Ke nake yiwa so na 'kauna, so na sha'awa, so na burgewa, wani irin so nake miki da a kullum ina tuna ki sama da sau sabain a rana, ke kadaice nake tuna abin takaicin ki, amma sai na tsinci kaina da yin murmushi. Ke kadaice kike mini iyashege ya burge ni. Ke kadaice macen da idan na kalla sai na tsinci kaina da yawan ambaton Alhamdulillah! Ke ka'daice macen da idan na ta'ba ki, ba ki mayar mini da marta ni ba, nake Jin bacin rai da tashin hankali. Haka nan ke ce macen da nake fatan idan na tsinci kaina a aljannah na fara tozali da ita cikin jerin matayen da ubangiji zai bani. Wallahi idan kika cire Hajiya ba wadda nake jin sonsu a raina da zuciyata irin ke da d'anki." Ya nisa ya cigaba da cewa "Ba zan miki karyar bana son Farida ba, ba zan miki karyar bata da wata daraja a idona ba, hakanan ba zance miki bana jin da'din zama da ita ba. Sai dai idan har gaskiya zan fa'da miki! Ina jiye miki a wayi gari Farida ta yi kunnen doki da ke a zuciyata, koma ta zarta ki, domin ita din mai hakuri ce, mai kawaici ce, ta sani na fi sonki, amma bata ta'ba tayar mini da hankali akan hakan ba. Zuciya a kirjina take kawai, amma bani nake sarrafa ta ba, ubangiji ne, Annabi kuma ya ce an gina zuciya da kaunar wadda yake kyautata masa". Jikinta ya laushi irin tubus din nan, tana gasgata dukkan furucinsa, ta kuma gasgata tana da kafiya da kaifin harshe. Tun ranar da ya auri Farida bata sake jin nutsuwa a zuciyarta akansa ba, sai yanzu. Ta nisa ta ce "Shikenan! Ka yi ha'kuri zan gyara, zan kuma kiyaye, amma dai ka dinga mini uzziri, ni akan ka, bana iya sarrafa kishina, ka taya ni addu'a, ka kuma kara ha'kuri da ni, kar kuma ka bu'de kofar da wata macen zata kamo ni a zuciyarka". Ta fa'da hawaye na zubowa. Da sauri ya matsa ya rungumeta, yana jin tamkar an yaye masa wata katuwar masifa a rayuwarsa, yana jin wata irin salama tana mamaye dukkan zuciyarsa. Ashe wannan 'daaurin da 'kirjinsa ya yi, ashe wannan fargabar da yake tsintar kansa a ciki, duk saboda rashin samun aminci ne daga wajen Sa'a? A yanzu da ta yarda zasu zauna lafiya sai ya ji tamkar anyi masa bushara da gidan aljannah ne. A fili ya dinga fa'din "Alhamdulillah! Allah kasa karshen tashin hankalin da zamu fuskanta kenan, Allah ka sanya wannan shine karshen jarrabawar mu". Sau uku tana yun'kurin yin magana sai ta kasa, da ya lura da hakan sai ya ce "fill free, fa'da mini abin da ke ranki". Ta tura baki gaba ta ce "Amma dai ka yi mini al'kawarin ba zaka ha'da ni zama da wata matarka ba, kuma yanzu na tabbatar waccan part din na Amaryarka ne". Ya sake ru'ko ta sosai ya ce "Ban manta al'kawarin ba, amma sai nake ganin a waccan gidan da kika tsara yadda za'a gina shi, na miki wannan al'kawarin, yanzu kuma ai bashi bane". Da rawar murya ta ce"kar ka hadani zama da ita, kar ka bari na dinga ganin mua'amalarku, zaka iya rasa ni a dalilin ciwon zuciya ko hawan jinin farat 'daya". "Ina son ki koyi jarumta Sa'adah! Ina son hankali na ya tsaya a wuri daya, a yanzu da nake matu'kar mararinki, idan na rabaku zan halaka ne, Ina tabbatar miki zan tare ne a inda zuciyata tafi so, shi kuma adalci wajibi ne ka yiwa kowa. Addinin musulunci! Addinin adalci ne, ubangiji ya sani namiji ba zai iya raba soyayyar matansa ta zama daidai a zuciyarsa ba, sai akace an masa uzziri anan, ma'ana bai yi laifi ba dan ya so wata sama da wata ba. Har ilah yau Sharia bata ce dole abin da ka yi da wannan, idan ka koma wajen wannan ma sai ka yi mata irin wannan ba, domin ansan ba zamu iya ba. Amma duk da hakan sai da Annabi ya yi ta wasiyyar kar mu jingine mace, mu ratayeta ita ba sakakkiyar mace ba, ita ba matar aure ba, dole a rabon kwana, muhalli, abinci da sutura ya zama daidai (eqaul). Shari'ar musulunci ta yiwa mata gata da adalci, ta yadda ko ba ke aka fi so ba, to kuwa indai ana kan tsarin sharia din ba za'a ki wulakanta ba". Ya numfasa sannan ya ce "ki min hakuri zaki koma wanccan gidan amma ba yanzu ba, ki bari nima na koyi jarumtar da zan kiyaye ka'idojin shari'a". A hankali ta ce"To" ba dan tana so ba, sai dan kar ta cigaba da yi masa gardama yana ganin Farida ce mai biyayya kawai. Ya tsura mata ido yana kallonta, sonta sai huda dukkan sassan jikinsa yake yi, cikin kasalalliyar murya ya ce "har yanzu baki huce da ni ba, har yau baki yafe mini ba?" Murya ba amo ta ce "me yasa ka ce haka?" "Har yanzu ban ji kin kira suna na ba, Na sani kuwa idan kina fishi ne kike gatsa sunana dan ki nuna mini iyakata. Idan kuma ba kya son shiga shirgina sai ki yi maganar ki ba tare da kin kama sunan ba" Ta zuba masa wani irin kallon da yake kidima shi,

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});