Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Abin kuma da ke ba ta mamaki yadda har yau bai ta ba bude baki ya ce ga sanadin rabuwar tasu ba, ita ma Sa'adah ba yadda ba a yi ba ta'ki fada, lamarin da kowa ya kyale su aka bi su da addu'ar alheri. Duk irin sha'kuwa da aminci da ke tsakanin Sa'adah da Baffanta, ko shi ta'ki fada masa dalili. Haka ma Mk duk yadda yake jin nauyin surukin nasa bai iya fada masa dalilin rabuwar tasu ba, illa ya ro'ke shi, akan kar ya yi fushi ko ya ga laifinsa, ko rashin kirkinsa akan sun rabu da Sa'adah. 'Kadarrar su ce haka, shi ma kuma Baffan bai zafafa ba, bai kuma takura sai ya ji dalilin ba, ya yi ammana tunda suke boye sirrinsu da alamun za su iya yi wa junansu afuwa a gaba, duk kuwa da a farkon mutuwar auren hana Sa'adah zaman gidansa yayi. **** Bayan yaron ya kawo mata littafin, ta dauko al'kalami ta fara, ta yi layi kamar uku ta goge tana ganin bai tsaru ba, ta ina za ta fara ne? Daga haihuwarta har zuwa girmanta, ko kuwa daga rayuwar makaranta inda nan ne mafari tsakaninta da MK Bichi, ko kuwa ta rayuwar aurensu za ta fara? Ashe rubuta labari da tsarawa ma iyawa ne? Lalle a gaida marubutanmu. Sau uku tana yi tana sokewa, ta tabbatar dai ba za ta iya ba, tunda ba ta taba ba, ai ko za ta ne mi wata cikin fasihan marubuta, ta bata labarin ita kuma ta fasashi ya zama littafi. Ta tabbatar ba za a rasa darasi da jan kunne cikin rayuwarta ba. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍️✍️ [5/14, 15:55] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.} https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR*. 11-12 A cikin wannan yanayin Zainab ta yi sallama a tsakar gidansu, sai da ta fara shiga gurin Inna ta gaishe ta, ta bar mata Khalifa, ta yi dakin Sa'adah. Zaune ta same ta kan katifarta hannunta ri'ke da littafi da biro. Gefenta ta zauna tana fadin "Nazari kike ne haka?" "A sanyaye tace "Wai nan littafi zan rubuta amma na rasa ta inda zan fara." Dariya Zainab ta yi tare da cewa, "Sa'adah manya, to wanne irin labari za ki rubuta?" Kai tsaye ta ce "Akan rayuwata, wata'kila ba za a rasa matan da suke cikin rayuwar da na yi a baya ba!" Ina fatan su ji labarina don su farka daga barcin makantar da suke, kafin su bude ido su gan su a *HALIN YAU* da nake fuskanta! Hawaye ya zubo mata ta sa gefen dan'kwalinta ta dauke a 'ko'karinta na kar Zainab ta gani. Cikin sanyin murya da tausayawa Zainab ta ce, "Amma kuma Sa'adah na dauka zuwa yanzu kin gane rayuwar nan bata da tabbas, bamu muke tsarawa kanmu rayuwa ba, da ace kowa shike sarrafa rayuwarsa da baku rabu da Uncle ba, da baki yi kukan rabuwar ba, Ni kaina ba irin kukan da ban taya ki ba, ba irin walankeluwar da ba mu yi ba a waccan lokacin, amma da yake a lokacin ubangiji bai nufa zamu samu cikar burinmu ba mun hakura kan dole. yanzu kuma Allah ya karkato da hankalinsa, maimakon ki yi wa Allah godiya, ki bishi sannu a hankali,har Allah ya taimake ki, ki koma dakinki, ki ri'ke 'danki, amma sai ki 'bullo da iya shege? Ni sai yanzu na gane ashe duk kuka da damuwar da kika yi ba har zuciya bane! Wallahi Sa'adah iskancinki ya fara damuna yanzu abin da kika mishi, da ya tsaya don ya taimake mu ya yi dai dai?" Sai a lokacin ta bude baki ta ce "Idan dai taimakon daga gareshi ne ba na so, ya je ya rike dukkan taimakonsa, ke duk wani abu da ya shafe shi bana bu'kata. ya yi harkar shi na yi tawa, idan Allah ya so ma ba zan sake kuskuren bari mu hadu ba, ai wannan visiting 'din ma dole ne yasa na je, Inna bata nan, Anty Sumayya kuma tana da uzirin mijinta ba lafiya, dama su ne suke zuwa masa. Jawad ne yace, Malam ya ce masa baya gari ba zai sami zuwa masa ba, kin ji 'karfin zuwana." Ta ja majina ta ci gaba da cewa, "Amma ban da haka ba zan je a ranar ba, balle mu hadu! Zainab da ne na yi haukan banza na son na koma masa, amma a yanzu ko zan mutu ban yi aure ba, zan yi iyakar 'ko'kari na ga ko zaman mota bamu sake yi ba, balle zaman aure" Muryarta ta karye alamun kukan da take ma'kalewa gaf yake da ya kubuce mata, ta ci gaba da cewa, "Ban taba dauka Mukhtar zai jefe ni, da abin da ya jefe ni da shi ba, in da tun farkon rabuwar mu na san kallon da yake mini ke nan da ko zan mutu ba zan bi shi ba, bare na ba shi ha'kuri, tunda na san shi ban huta ba. Ban ga kuma da me na tsira a cikin zamana da shi ba, sai ko rabon Jawad da ya ratsa shi ma Ubangiji ne Ya 'kaddara ni ce uwarshi, amma a zuciyar MK, Farida yaso ta zamo uwarshi" Sai lokacin Zainab ta katse ta da cewa, "Wallahi karya kike yi, ina ce ba dole aka mishi ya zabe ki a farko ya barta ba? kin dai san namiji ba a mishi dole, kuma ke da kanki kin tabbatar ke ce kike da alhakin mutuwar aurenki?" "Tabbas ina da laifi amma ai shi ma ba za a rasa nashi ba, sannan kuma bi-ta-da-'kullin da ya bi ni da shi a idonshi da zuciyarsa ya sa na ji ko son shi ne ajalina sai dai na mutu da na koma masa, balle ma ba abin da hakuri ya bari" "Ko za ki kwana kina rantsuwar ba kya son sa, ko ba kya son ki koma, ba yarda zan yi ba don kuwa 'karya ne tsagwaronta, don kuturun munafunci kun 'ki fa'dan mussababin rabuwar taku ai wannan ka'dai ya isa a san kuna son junanku tunda ba ku yarda aji sirrinku ba. Amma ban sani ba ko kin fa'da wa Halima tunda 'kanwar Inna ce ko kuma madadin Anty Sumayya" 'Kin tanka mata Sa'adah ta yi dan ta san magana ta fada mata a fakaice. Ganin haka yasa Zainab canja magana don tasan idan ta ci gaba da zungurarta yanzun nan Inna za ta shigo ta raba su don ba 'karamin aikin Sa'adah ba ne ta rufe ta da sababin da duk wanda ke gidan sai ya san an ta'ba ta. Sai ta bige da lallashi, "Haba Maman Jawad na san ki da fa'da amma ba ki da ri'ko sam, na ro'keki kar fishi yasa ki yanke hukuncin da za ki yi kukan da ya zarce wanda kika yi a baya". Ta nisa ta kalli Sa'adah, ta sake cewa "Idan ma wani Abu ya ce miki da ya miki ciwo wata'kila ya fada ne a lokacin da yake cikin fishi, ko kuma ya fada ne don ya 'kuntata miki, ki ji yadda shi ma yake ji. Amma shi ba abin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});