Chapter 16
Chapter 16
mu'az Matazu, Safina Usman Bunkure, da Humaira Suraj wadda dukkan su iyayen su masu 'kumbar susa ne, itace kadai yar talaka, ko Halima da ba wani kudi ke gare suba, sun wuce matsayin su Sa'adatu, tunda Baban ta ma, aikaci ne a ma'aikatar Revenue yayin da mahaifiyar ta take principal a wata makarantar 'yan mata ta gwamnatin jaha(GGC). Ita Sa'adatu kawai kwalliya da gayu ne ya janyo mata 'kawaye tunda tana samun abubuwa masu tsada daga yar uwar ta Sumayya. Tunda suka hada group basu cika mai da hankali kan karatun su ba, illa kwalliya da kuma soyayya tunda kowa ya san FGC KANO co-education ake yi, ma'ana makarantar maza da mata ne a ha'de. Dukkan su suna da samari a ajin, inka dauke Halima da ta ce ta fi 'karfin soyayya da yara 'kananu, kasancewar tana da saurayi na gaske a gida, wadda ya kasance 'Dan 'kawar maman ta ne. Khalil Ibrahim na cikin wadda su ke son Sa'adatu Bashir, mahaifinsa ne kwamishinan ilimi na Kano a wanccan lokacin, ita ma kuma ya fi kwanta ma ta a rai, dan haka tana kula shi, dukkan kudaden shi na kashewa a makaranta a kanta ya ke 'karewa. Wani lokacin ma har fakar idon mahaifiyar shi ya ke ya debo mata kudi kasancewar ta shahararriyar yar kasuwa domin Dubai take fita ta shigo da kayayyakin mata na alfarma, wani lokacin har da Abaya da lace yake daukowa dan ya bawa Sa'a🤔 Suna da 'kokari amma da yake basu mai da hankali kan karatun ba sai suka sha mugun kaye. Halima da ta kasance ogar su saboda duk tafi su 'kokari ta kuma fi su izza da buri, ita ce kawai ta yi ta shida, amma kowacce a cikinsu ta wuce ta ashirin. Sa'adatu ita ce kashin baya ta kai ta talatin tunda duk sun fita background din makaranta mai kyau. Dukkan su jikin su yayi sanyi da ganin sakamakon su, amma Sa'adatu ba ta wani damu ba, tunda dai ta san daga Inna har Baffa sun san tana da 'ko'kari a makarantar da ta baro. zai yi wahalar gaske ma a wani tuhume ta in dai ba Sumayya ce ta zo garin ba. A cikin wannan yanayin suka kammala SS1, suka shiga aji biyar, budurci sosai, ya bayyana a jikinsu, duk wadda ke FGC KANO ya san da zaman 4stars. Barin Sa'adatu Gogel, ba wai kyau ta fi su ba, a a kawai ita ma'abociyar kwalliya ce kusan kowanne term sai tasan yadda ta yi, tsakanin 'karya da gaskiya an sabun ta mata uniform, sannan ko mai na ta mai tsada ne tunda ga kan sandal, da school bag, Sumayya ta tsaya ma ta a wannan bangaren, duk kuwa da tana mamakin yadda kowanne hutu sai ta canja komai. Hakan yasa ta saje cikin Ya'yan ma su wadata har ma ta fi su daukar ido, mussaman saboda 'kirar jikin ta. Zangon karatu na biyu, a aji biyar din su, a ka turo sabbin 'yan hidimar 'kasa (COPPERS) Cikin su har da Mukhtar Kabir Bichi (MK Bichi). [5/19, 18:52] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 21_22. Ranar da ya fara shiga ajin su a matsayin malamin harshen turanci(English language), ba abin da ya musu illah introduction, wato gabatar da kai, ya sanar musu zai koyar dasu harshen turanci. Bayan sun masa barka da zuwa, sai ya bu'kaci da kowannen su zai tashi ya gabatar da kan shi, as he did. Sa'adatu da hankalin ta ya yi nisa wurin rubutawa Khalil Ibrahim reply din wasi'kar da ya mata na zai je School shop mai ta ke son ci?. Ba ta san har anzo kan ta ba, sai da Halima tace "Gogel"! Sannan ta yi firgit ta mi'ke, ba tare da ta rufe takardar da ta ke rubuta reply din ba, cike da yanga da iyayyi tace ,"I am Sa'adatu Bashir Gogel" daidai lokacin ya 'karaso jikin desk din na ta, Yasa hannu ya na nazarin rubutun da ya 'dauke mata hankali, baice uffan ba ya dauki takarda ya zira a aljihun sa. Wucewa ya yi yana fadin "next" har aka kammala ya cinye period dinshi ya fice tare da takardar. Takaici ya kama ta, ta fara tunanin mai ta rubuta ne? _Nagode da kulawa Khalil komai ka ga ni indai ya burgeka, ni ma zai burgeni, Sa'a luvs you_. Abin da ta rubuta kenan, haka kawai ta ji takaicin wannan Malamin da ya kira kanshi Mukhtar ya kama ta, Ina ruwan shi da ita daga zuwan shi? Washa gari da ya shiga, karatu sosai ya zazzaga musu cikin turancin da ya kama bakin shi tamkar a 'kasar ingila ya girma. Ya yi tambayar an fahimta ko da akwai mai tambaya? Serious student din cikin su ne, su ka shiga tambayar abin da basu fahimta ba, shi kuma ya sake bayani a hankali dalla dalla, har kowa ya ce ya fahimta, sai yace zai yi tambaya. Ba zato yayi pointing Sa'adatu Bashir ta tashi ta yi masa bayanin yadda ta fahimci topic din da ya gama bayanin sa. Nan da nan taji ta muzan ta, saboda ba wani fahimta ta yi sosai ba, ta mi'ke ta na rarraba ido ta kasa furta kalma ko guda cikin tambayoyin da ya ke mata, da 'kyar tace "ban gane explanation din ba dama" Ido ya zuba ma ta yace "We're not talking in Hausa but we're in English" kunya ta kama ta, wato har ya gane ba ta iya mayar da magana da turanci? ya sake cewa "I ask all of you who didn't understand, but you mutter"! Ita dai ba baki, sai ido tana jin wata kunya na kama ta. ya dade yana nazarin ta, sannan yace ta zauna ya sake bayani sosai, a lokacin kuma ta mai da hankali ta na sauraro tunda tana jin maganar, wurin mayar wa ne ke mata tasga'do. Cikin 'kankanin lokaci ya fahimci ita da 'yan group din su, ba abin da suka sa gaba irin kwalliya da soyayya, mussaman idan class ba teacher to hirar kenan. Transfer ta baza ta ce ta sami malaman makarantar, ciki har da class master din B class, na ss2 ajin su Sa'adatu, nan take kuma akasa Mukhtar Kabir Bichi a mastayin Class master din nasu. Wannan damar da yasa mu ne ya 'kudure a ran shi sai ya canja wa'dannan daliban, abu na farko da ya yi musu ya rarraba musu gurin zama ya cillasu ta yadda sai dai hange a tsakanin su. Haka kawai ya ji duk yafi jin haushin Sa'adatu saboda yadda ya lura wadda ta hada kai dasu din sun fita dama, kullum sai ya ga an kawo su a motoci masu kyau, an kuma zo an dauke su, sa'banin ita da ta ke zuwa da kanta cikin adaidaita sahu ko mashin,'kawarta da ya ke ganin suna zuwa tare Zainab Ma'aji sam ba halinsu 'daya ba, ba ta da hayaniya ta na kuma maida hankali wurin karatu duk da ita tana c class, ajin commercial. Amma yayi nazarin sa ya gane buri da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157