Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

maganar aure za ki yi tsalle ki ce bai miki ba, amma kina son abin hannunsu saboda kawai kin 'dorawa kanki sai kin daura abin da kike gani a jikin yaran da 'karfin iyayenku ba 'daya ba" Ta nisa tana jiran ko Sa'adah za ta yi magana sai taji sabanin hakan, duk da dai ta lura jikinta ya sake yin laushi fiye da 'dazu, don haka sai ta sake cewa, "Ki ajiye wannan dabi'ar, sannu a hankali idan kina da rabon yin arzikin za ki yi shi ne. Yanzu dai babban misalin da zan miki da yayarki ne, duk da cewa lokacin da aka aurar da ita ba ki da wayon da za ki gane komai, mijinta ko mashin din da kika raina mai hawansa ba shi da shi, amma a yau mene ne bai mallaka ba? A saninki 'kasashe nawa ya debi iyalinsa suka fita? Wace irin hidima da karamci ne ba ya mana ke ma shaida ce tunda dai ko wannan makarantar da kike yi ba don shi ba, da ba ki yi ta ba, da ace farko ta raina matsayinsa da yanzu ta cim ma wannan jin dadin da kowa ke mata kallon tana ciki? Tsakanin ki da Allah ba don ta sau'ka'ka buri ba ta kai wannan matsayin?" Kai Sa'adah ta girgiza wa mahaifiyarta don kuwa harshenta ya mata nauyi, amma a ranta tana raya in dai akan zaben miji ne an wuce wannan babin, zuciyarta ta riga da ta aminta da MK Bichi kuma shi ma ai talaka ne tunda ko mota ba shi da ita. Jin da'di da son kayan 'kawa kuwa ba mahalukin da ba ya so sai idan bai samu ba, ita a jininta ne son gayu ba wai fariya ko 'karya ta sa a ranta ba. 😀 Don haka ba ta dauki maganar ajiye dogon buri da aka mata nasiha da wani muhimmanci ba. "Kullum addu'a ta Allah ya ba ki miji nagari wanda zai kula da ke da amana, ke ma irin adduar da za ki rike ke nan. Dauki abinci maza ki ci kar ya gama hucewa, Allah ya miki albarka." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amin na gode?" Sannan ta ja abincin ta hau ci, danwaken fulawa ne da yaji mai da'din gaske, tana ci tana yaba yadda Innarsu ta iya sarrafa abincin gargajiya masu da'di, kawai dai abincin zamani ne ba ta yin su ko kuma don za su ja kudi ne? Sai ta tsinci kanta da cewa "Allah Inna na kusa daina cin abinci mai nauyi." Cike da mamaki ta ce "Me za ki dinga ci to?" Murmushi ta yi, ta ce "Chips, chicken, sai dangin su pizza, da indomie da kwai, sai na bi bayansu da ababen ruwa irin su juices da yougurt ko hadadden shayi hadin kauri." Salatin da Inna ta 'dauka ne ya sa ta dakatawa tare da tunanin ta yi subutar baki. "Ashe duk togaciyar da na gama yi miki bai shiga kunnenki ba? A gidan uwarki kika san wadannan kayan, wadda ba ta alfahari da abin da ta bude ido ta gani a gidansu, sai hangen kayan wani da ba ya rufa maka asiri! Nasan kina nufin idan kin je gidan miji ne kike tunanin wannan rayuwar za ki yi" Ta kafe ta da ido tana mata kallo mai tsanani sannan ta ci gaba da cewa, "To saurare ni da kyau aure ya wuce wasa tun wuri ki cire wannan tunanin a ranki, gabadaya aure ibada ne, duk abin da akace ibada ne, to ba son ranka za ka yi ko zaka gani ba, sannan ba abin da ke ri'ke da aure gabadaya sai ha'kuri don haka ki cire wannan tunanin a ranki. ki yi fatan Allah ya ba ki miji nagari, da hankalinki zai kwanta, domin komai za ki samu idan ba kwanciyar hankali ina tabbatar miki ba za ki ji dadinsa ba Allah ya shirye ki, adduar da zan dinga miki ke nan." Ta fada da iyakacin gaskiyarta, domin ta lura addu'a ce kawai za ta canja mata Iyah ba hantara ko nuna fishi ba. *** MK yana isa gida ya tarar da Hajiyar Bichi ta zo, a falo ya tarar da su ita da Hajiya Babba suna cin makani wanda ba ya tantamar daga Bichi ta taho da shi, da murna ya hau fadin, "Hajiya ashe da gaske kike da wuri za ki dawo?" Dariya ta yi ta ce "Allah Ya yarda ban dade ba". Suka ci gaba da hirarsu har su Abbas da Ahamad suka dawo aka ci gaba da hirar da su, Maghriba ce ta dakatar da su. Bayan sallar Isha MK ya tarar da Hajiya Babba a dakinta, ya gama kame-kame da soshe-soshen 'keya, sannan ya ce "Hajiya so nake aje a tambayar mini izinin magana da wata yarinya a wajen mahaifinta." Dadi ya kama ta, ta shiga fadin "Alhamdulillah! Allah Ya sa abokiyar arziki ce, ina ne gidan nasu?" Sake kasa ya yi da kansa da kyar ya ce "A babban layin Unguwa Uku suke mahaifinta mai karamin karfi ne amma mutumin kirki ne, na san shi tun kafin nasan yarinyar." Farin ciki ya bayyana a fuskar Hajiiya Babba ta ce, "Yanzun nan za mu tattauna da Hajiyar Bichi tunda Allah ya sa ta zo garin, gobe In Sha Allah zan je har gidan Babanku Alhaji Isa (Aminin mahaifinsu ne) na shaida masa. Sai ya je ya tambayar maka, tunda ka kammala karatun kuma ka iya harkar kasuwanci ba za mu ji tsoron aurenka ba, bare da ikon Allah da wuri za ka sami aikin yi ka ci gaba da rike mu gabadaya." Koda ta sami Hajiyar Bichi da maganar fatan alheri kawai ta yi tare da cewa, "Hajiya Babba ai ke ce uwarsa, ni 'yar addua ce!" Wannan biyayyar da tun fil'azal Hajiyar Bichi ke yi wa Hajiya Babba ta taimaka kwarai wurin samun zaman lafiya a tsakaninsu, tare da saukaka kishin junansu matu'ka da gaske. A satin aka tambayo masa izinin magana da Sa'adah, a take kuma Baffa ya ce ya bashi damar ya nemi yardarta ba don yana jin tsoron halin dan yau ba, da a take zai ce ya ba shi ita, to tsoron kar ta ce ba ta sonsa ta kunya ta shi yasa ya ce idan har sun daidai ta kansu to ya ba shi, aka yi murna aka rabu ana addu'ar Allah Ya sa hadin Allah ne. A ranar Baffa ya zaunar da Sa'adah tare da mahaifiyarta ya ce, "Bakin da suka bakunce ni a yammacin yau, zuwan Iyah ne. Yaron nan Mutari ne ya turo a ba shi iznin neman amincewarki, ni kuma na ba shi dama ya nemi yardarki ba don Ina jin tsoron kada ki yi mini *HALIN YAU* ba, da kai tsaye zan ce na ba shi su zo ayi maganar aure. Saboda yaron nutsatstse ne , ya san mutuncin manya mai kokarin neman na kansa ne, kullum ya zo shagon askinsa sai ya zo ya gaishe ni, ban kuma taba jin hayaniyarsa da wani ba, kiga dai yadda shagon yake cika dam da matasa amma ban taba jin an ce ana fada da shi ba. Da shi muke sallar Magariba da Isha kullum yana sahun gaba, ba zan miki dole ba

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});