Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 112

Chapter 112

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jikinta, tare da sake cewa "kina addu'ar na samu kudin ya kai na siyan jirgin naki kuwa?" Inna da take gurin ta ji Hawaye na neman kwace mata, ta mike ta shige dakinta, tana jin dadi da tausayin yadda Jawad yake girmama lamarin uwarsa. Dawowarsu Nigeria ya sake wayo sosai, aka saka shi a makarantar Intercontinental college tsananin hazakarsa yasa suka dauke shi J s 3, maimakon aji biyu da zai shiga. Iya turanci gangariya da Jawad ya yi ya janyo masa farin jini ainun a gurin malamai hatta student son abota suke da shi. A haka ya Saba da wani dan ajinsu Muhsin Sani Yar-gaya, a hirar su da Muhsin Jawad ya fahimci Malam da Mami sun rabu ne, wato divorce ne a tsakanin su. Kusan Muhsin ne ya cusa masa dabi'ar kin Farida a dalilin shi Muhsin din mahaifiyarsa ta rasu shekaru biyu, sannan amaryar Baban su azabtar da su take yi, shi da yayarsa makaranta nan da suke zuwa ne kawai bata yi nasarar rabasu da ita ba, hatta magana da mahaifinsu sai a sace suke yi da shi domin shima tsoronta yake ji. A hankali Jawad ya fara janyewa Farida idan ana son aga damuwar sa to weekend ne ace zai tafi gadon kaya. Ba irin rarrashin da Farida bata yi masa amma ya kame daga yawan yi mata hira, idan kuwa yaje gidan a takure zai zauna tamkar bai santa ba, abin ya damu Farida sosai hatta Mk ya damu, ya tabbatar kuma ba zaluntarsa take yi ba tsiya ce kawai irin ta 'Dan Yau. Har aka kai jallin da kuka yake zuwa gidan, idan Hajiyar Bichi ta ce da Mk ya barshi tunda baya son zuwa, ya kafe sai yaje. Rannan dai da abin ya ishe Mk a gaban Hajiya ya dinga fa'din "ko zai shide sai ya je gidan, da suka rayu shekaru biyu tana masa wahala bai 'ki ta ba, sai yanzu saboda ya samu shashar uwa tana kitsa masa maganganun iyashege to kanta zata cuta ta kuma cuci 'danta. Ya kalli Jawad da yake bayan Hajiya yana kuka da hawaye ya zare masa ido ya ce "idan na kuma jin kace mini zaka unguwa uku sai jikinka ya fa'da maka ai can ba gidanku bane, kana kin gidan ubanka kana kwadayin gidan wasu, zo ka shige girma da arziki tun ban tashi ba, kuma nan din ma ba zaka dawo ba can din da baka so a can zaka zauna". Jawad ya rushe da kuka yana cewa "Hajiya ki ce ya dawo da Ni dan Allah". Aikuwa haka ya tafi da shi yana kuka , sai dai kaya kala biyu Hajiyan ta bashi tabbacin zai dawo kenan. Shiyasa ya rage sautin kukan nasa. Wannan matsalar gaba'daya Mk Sa'adah ya jinginawa ita ya dinga tunanin hanyar da zai magance ta. Ana haka Jawad ya dinga wani irin zazzabi, karshe farankama(chicken fox) ta feso masa a jiki. Hajiyar Bichi da kanta ta bugawa Inna waya ta sanar musu, Inna bata yi kasa a guiwa ba ta zo ta duba shi har da tsarabar kayan dubiya, ba yadda bata yi da Sa'adah akan su tafi tare su dubo Jawad amma ta ki. Da kyar Inna ta shawo kanta bayan taje da kwana biyu, Suka shirya Suka je da Zainab Ma'aji wacce a lokacin wattannin ta biyar da aure, da kuma cikin wata hudu a jikinta. Ma'aikaciya ce a hukumar kidaya ta kasa reshen jahar Kano. Cikin kwalliya sosai Sa'adah take, ta dawo wata irin mace da gayu da ilimi suka ratsata mussaman da Alhaji Mamman ya sake dawowa cikin rayuwar ta, ba karamin kudi yake sakar Mata ba, ita kuma bata kwangen yin sutura ta daukar hankali. Komai nata daukar ido yake yi, ado take a yanzu irin wadda bata yi zaton zata yi irinsa ba, amma kuma cike da hankali da nutsuwa. A wannan lokacin ta kammala karatunta tana makarantar horar da lauyoyi ta Bagauda(call to Bar). A motar mijin Zainab Suka je bayan sun tsaya a hanya sun masa siyayya ta sosai, kai tsaye suka shiga gidan ba wani nauyi domin dai Sa'a ta kan zo gaida Hajiyar duk da ba kasafai ba. A falon Hajiyar suka tarar da Mk yana shafawa Jawad calamine lotion a jikinsa ko ina jikin Jawad din maganin ne adalilin duka jikinsa ta feso masa har fuska, farin maganin ya maida Jawad wani iri. Suka gaisa da Hajiya cike da girmamawa, suka tambayi mai jiki. Zainab ce ta gaida Mk cikin mutunci, har tana cewa "Uncle rabon da na ganka har na mance". Ya yi murmushi yana cewa "kina cikin daliban da nake cikiyarsu Zainab! Ya mijinki da Yara?" Ta 'kasa kuma kallon Sa'a kawai ya ke yi zuciyarsa na wani irin tsalle, yayin da ita ta yi tamkar bata ganshi ba, ko arzikin gaisuwa bai samu ba, ko Jawad da yake kusa da shi, sau daya ta masa sannu ta maida hankalinta wurin Hajiya. Rashin gaisawar da basu yi ba, ya ta'ba Hajiya kwarai da gaske, yayin da Mk ya dinga fargabar wayewar da cigaban da ya gani a tare da ita, kwarai da gaske ta banbanta da Waccan Sa'adan da ya rayu da ita. Zainab sai zungurar ta take yi akan ta gaishe shi, amma ta yi mirsisi. Suna zaune Ahamad ya shigo ya ganta yana cewa "yau wa nake gani kamar Antina" Da murmushi sosai ta ce "Nice me zan Samu?" Ya mi'ka mata 'datar da yake ci, aikuwa ta karba ta hau ci, hakan kawai sai da Mk ya ji haushi dan me zata ci ragowan yawun Ahamad? Ta mi'ka masa mukallin mota tana cewa "daure ka debowa 'danka kayan dubiya da mamarsa Zainab ta kawo masa". Da azama ya karba, ya dinga shigo da kayayyaki har Hajiya ta ce " wanne irin hidima kuka yi haka Sa'a? Sai kace wadda zai bude shago?". Ran Mk ya baci saboda yadda yaga uban kayayyakin ciye ciye masu tsada sai kawaia zuciyarsa ta kisima masa Bazawarinta ne ya yi wannan siyayyar. Ya dinga huci karshe ya fice bai ko sake kallon kayan ba, da kyar ya ce da Zainab ta gaida gida. Jawad ya warware ya koma zuwa School amma rashin son zuwa gidan Farida na sake ruruwa a ransa kullum da kuka yake isa gidan, sannan har yaje ya dawo sai ta 'kure da ya yi mata magana har zane shi Mk ya yi amma bai canja ba. Kan dole Mk ya samo masa makarantar kwana ba tare da ya yi shawara da kowa ba, da kyar aka samo makarantar saboda anci karfin zangon karatu na biyu. Sai da komai ya kammala na makaranta ya fa'dawa Hajiya dan kar ta hana, Kan dole ya dauki Jawad ya kai shi makarantar gwamnatin tarayya ta Kiyawa, a kokarinsa na nisanta shi da masu hure masa kunne da masu son cusa masa muguwar dabi'a. A dai dai wannan lokacin aka dawo da Mijin Sumayya aiki Kano, da Karin girma sosai. Tuni dama sunyi gininsu a gandun albasa layin kwankwaso, da farin ciki Suka tattaro Suka dawo kano cikin gidansu na alfarma. Zainab ta haihu ta sami Musa sunan uban mijinta ne, Sa'adah ce ta yi masa inkiya da Walid. Farida ce dai shiru har yanzu da suke

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});