Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

san mijinta irin mijin JIYA ne ba na YAU ba, ki yi fatan dacewa kawai, duk auran da aka ƙaranta wahala da bidi'a ya fi karko ya fi albarka". Cike da rashin gamsuwa ta ce, "A'a Inna gara dai a yi maka din, mijin ma ai sai ya raina ka, danginsa su isheka da gorin sadakar ka aka ba shi." Shiru Inna ta yi ta kyale ta, tana tunanin ashe akwai kallo ranar da tasan irin auran da za'a mata. Baffa da ya ga kayan da Alh Mamman ya kawo bai yi fada ba, kamar yadda yake yi a baya, ya farke envelope din sai ga rafar dari biyar wato dubu hamsin wanda ta zarce darajar dubu darin yanzu. Ya ajiye kudin, kayan kuma ya ce su dauka ta yi amfani da su, tunda dai sai da aka fada masa gaskiya sannan ya ba ta. shikenan rabuwar su da Alhaji Mamman. Tunda aka tsayar da maganar aure Sa'adah ba ta sake tsayawa da saurayi a fili ba, sai ta waya wanda suke cika mata waya da kudi, sai kuma Khalil da ta kasa rabuwa da shi duk da ba ta yarda ya zo gidansu sai dai idan ta je gidan su Halima ko kuma idan ta je gidan su Zainab Ma'aji sai ya zo. Soyayyarta da MK a gurinta za ta ce ba laifi, idan ya kira ta a waya yana dan jimawa su yi hira, haka nan yanzu sau biyu ya ke zuwa zance a sati, wani zubin ma har sau uku. Amma dai ita ba sosai ta gamsu da kulawarsa ba, kawai dai tana bin sa da yadda yake yi, da fatan Allah Ya sa ba soyayyar ne bai iya ba ta bakin Halima da Safina, da suke kushe shi duk da sai yanzu da aka tsayar da maganar aure, suka san da gaske soyayya suke yi. Kiri-kiri suka nuna mata me zai sa ta yi gangancin barin Alhaji Mamman inda za ta huta, ta bige da auran mai fama da alli da hidimar gidan su? Ita dai Sa'adah sai dai ta ji su, ta yi shiru. Musamman da ta ta'ba ce musu ba son sa take yi ba Baffa ne ya mata dole, ai nan ma suka mata ca tare da cewa, "A wannan karnin na 21st century za a miki dole?" Ta yi shiru tana jin yadda suke ta sakin maganganun rashin 'da'a tare da ingiza mai kantu, suna jaddada mata da dai ta auri mugun Malamin da ya gama tozarta ta a bainar nasi, gara ma ta auri Khalil Ibrahim sa'anta. Shiru take yi, wani lokacin zuciyarta ta shiga wasiwasi akan MK Bichi, musamman yadda bai kai su Khalil nuna mata soyayya ba. Amma dai ta san ba ta isa ta koma ta ce wa Baffan ta ta fasa ba. Alkalamin *Surayya Dee* ✍🏼✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 43-44 A kwana a tashi ba wuya wurin Ubangiji. Watanni biyu suka zo suka shude tamkar walkiya, mai ya'ki da zuciyarsa kadai ke ribatar lokacin sa a cikin wannan zamanin da ababen shagala suka kewaye shi. A wannan lokacin manhajar 2go ta bullo, matasanmu samari da yanmata suka yi tururuwar karban wannan sabuwar manhajar wanda hakan ya taimaka wurin sake ruguza tarbiya matasa da yawa, saboda yadda ake hira da musayen hotuna na rashin da'a ba tare da jin shakku ko nauyi ba. Sa'adah na cikin jerin yan matan da suka yi tashen 2go da taimakon su Safina da Halima, yini take yi da waya a hannu har sai da Inna ta fahimci sabuwar rayuwar da ta shiga na yadda ta fi bawa waya muhimmanci fiye da komai. Ada kafin Inna ta fito da safe Sa'adah ta kammala komai na gyaran gida, wani lokacin har abin karin kumallo za ta yi, musamman idan Baffa ba ya gari, amma a yanzu sai ta kai rana ba ta share gidan ba, ga wanke-wanke a gefe kudaje na bin su, ko karyawar ma sai Inna ta yi ta faman kiran ta sannan za ta fito, Nan ma tana cin abincin amma wayar na hannunta, tana ta latse-laste tana murmushi. Wannan abin ya yi matu'kar damun Inna musamman yadda ta lura wanka ma Sa'adah sai ta kai la'asar ba ta yi ba, sabanin lokutan baya da sanyin safiya take wankanta da zarar ta kammala ayyukan gida, amma yanzu sai yamma likis ko ma dare. Ranar wata Litinin aka tashi da rashin wuta a unguwar gabadaya, cikin rashin sa'a ta kwana da rashin caji a wayarta, don haka sai ta tashi sukuku da rashin karsashi. Tana kwance lamo a kan katifarta, ta kalli agogon bango dake jikin dakin, ta ga karfe 7 na safiya, sai ta ga lokacin ma baya gudu don haka sai ta yun'kura ta gyara dakinta, ta gangara tsakar gida. Kafin wani lokaci da ba shi da yawa ta gama komai har wanke-wanke, gefe kuma ta dora musu abin da za su ci. Koda Inna ta fito ta gan ta, a tsakar gida sai mamaki ya kamata, musamman yadda ta gan ta ba waya a hannunta, ta gaishe ta ita ma ta amsa da walwala, sai da suka karya, ta yi wanka ta shirya ta yi fes da ita, ta fito tsakar gida ta sa tabarma ta zauna saboda lokacin zafi ne. Sai lokacin Inna ta dube ta ta ce "Wannan ita ce Iyah da na rayu da ita, wannan ita ce Iyarmu, ta jiya da ragowar kwanakin da suka shude ba Iyar mu ba ce ma'abociyar aikin gida da kuma ado"!. Kunya ta kama Sa'adah ta sa hannunwanta biyu ta rufe fuskarta, ita kanta ta san ta shagala, tana son ta tashi ta yi ayyukanta, amma sai ta kasa ajiye wayar tana ganin bari a dan jima, a haka har sai lokaci mai yawa ya tafi ba tare da ta an kara ba. Cikin hikima Inna ta sake fadin, "Ko a mafarki idan aka

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});