Chapter 141
Chapter 141
jin da'din yadda ya fara samun lagonta dan haka ya sake lankwashe murya ya cigaba da 'kiran ba kakkautawa. Zuciyarta ta yi laushi tubus, ta sami sau'kin nauyin da ta yi adilin kishi, domin ta gasgata shi da ya ce har yanzu shine bai canja ba, ba kuma abin da ya ragu na soyayyarta a zuciyarsa. Cikin muryar tabarah ta zallan shagwaba ta ce "Haba Mana, Inna ta na cikin gidan nan fa! Ni dai ka daina, na amsa Na'am, Na'am Na'am". Ya zuba mata idanuwansa da suka kada tamkar ya tashi daga barci ne. Murya ba amo ya ce "Ba zan boye miki ba, sha'awar ki nake ji sosai, tunda muka rabu nake fama da matsanancin ciwon kai da mara, sosai na sha wahala a farkon shekaru uku da rabuwarmu, a lokacin da nake Uk, na sha zarya a gaban manyan likitoci, suka tabbatar mini rashin mace a kusa da ni ne dalili. Da na yi aure na samu sassauci, baya tashi sosai, ko ya tashin ma baya takura ni sosai, amma wallahi Sa'adah, tun ranar da muka kai ki gidan Anty Sumayya nake Jin alamun ciwon na neman takura ni, jiya ko runtsawa ban yi ba, adalilin yadda nake jin ciwon da marata take yi, ga gangar jikina taki sarrafuwa domin ba abin da take so ya rabeta sai ke". Ya bu'de dukkan hannuwansa yadda yakee mata tun fil azal, da rawar murya ya ke fadin "come closer to me my dear"! Kishin yadda ya tabbatar mata, bayan ya yi aure ya samu sau'kin ciwonsa, ya sake sawa ta hargitse. A tunzure ta ce "ka gaggauta tafiya ka rungumi wadda ta kwantar maka da ciwon rashin mace da ka yi fama da shi a baya! Wai kwana ka yi baka yi barci ba, kwana ka yi dai kana rarrashinta, kana kasheta da soyayya amma saboda ka mayar da ni bitacan shine ka karkace baki kana fa'din min tatsuniyar da ko Jawad yasan 'karya ne tsagwaronta, 'karya kawai". Jikinsa ya yi sanyi, tabbas gaskiyar Baffah ne akwai abubuwa da yawa da Sa'a ba zata canja ba, domin a jininta ne, gashi dai a zahiri hankali ya shigeta, ilimi ya ratsata, Amma kishi yasa agabansa ta karyata shi, ba shayi ko shakka. Wanda shi kuma ba zai ta'ba yarda ya sake daukan kaifin harshenta ba, a yanzu da take shekaru talatin da biyu. Ya mike ya ce "Ni ne mai fa'dar tatsuniyar karya? Ni Kika karyata, nine makaryaci?" Ta saci kallonsa, ta ga yadda ya bata rai sosai, ta yi shiru tana jin guiltiness na kamata, amma ta kasa bu'de baki ta ce masa sorry. Ya kada kai ya ce "Tabdi jam ashe kuwa da sauran ki". Dai dai lokacin Inna ta fito tsakar gida taga zogalen da ta ajiye wa Mk, yana gurin dan haka ta bude baki ta ce "Iyah zo ki daukar masa zogalen nan mana, nasan shi da son zogale". Farin ciki ya mamaye Mk! Ba dan komai ba, sai dan sassaucin da yake gani tare da Innah. Da azama ta amsa, ta kuma mike ta fita duk a kokarinta na kar Inna ta zargi wani abu. Ta dauko ta ajiye masa a inda yake tsaye, kamshinta ya cika masa hanci, da ta sunkuya ajiye masa zogalen, ya ga yadda siket din jikinta ya matu'kar fito da taswirar mazaunanta, sai ya matu'kar kidima, ya dinga kokawa da zuciyarsa domin kuwa, ba zai sake kulata ba, har sai ta bashi ha'kuri. A kausashe ya ce "juye mini a leda sai naje gida zan ci". Ta sake juyawa ta fita! Tana jin tamkar ta bashi ha'kuri ya fasa tafiyar, ta sani badan maganar da ta fa'da ba, da sai anyi kiran sallar azahar da ya tafi, haka Kuma zai ta zama yana rarrashinta da son ya jagwalgwalata. Amma yanzu zai tafi gurin matarsa, ya barta da kewa da bacin ran zuciya. Ta hango shi ya zaunar da Farida a cinyarsa yana bata zogalen a baki, tunda ta san shi da son dora mace a kan cinyarsa. Tana juye masa a ledar ta ri'ke, ta kasa bashi, kawai ta saka masa kuka. Ya yi sakare yana kallonta, yana ayyana ko sai yaushe zata daina kukan banza marar dalili, ya sani tafiya gida da ya ce zai yi ne ya mata ciwo. Tabbas kishinta ba zai bari su yi amarci mai da'di ba, ba zai bari su rayu cikin farin-ciki ba. Shikuma ya riga ya kudire duk runtsi ba zai rabu da FARIDA ba, zai yi kuma dukkan kokarinsa ya ga bai tashi a sahun masu shanyewar barin jiki ranar gobe ba. Wahala ne dai zasu dandana shi da ita tunda idan ranta ya baci, ko idan ya ganta cikin rashin nutsuwa shima hakan zai zama marar nutsuwar. Domin ya tabbatar itace jagorar farin-cikinsa. Ya daure ya kore raunin da yake neman sawa ya fasa tafiyar, ya kalleta sosai ya ce "Zaki san kin ce mini makaryaci, na rantse miki sai na miki abin da gaba idan zaki mini magana, sai kin tauna harshen ki sosai. Godài godài da ke amma lafazinki na yara 'kananu, ko Farida ai ba ta mini irin wannan iyashegen". Ai kuwa ta fàdi kan shimfidarta ta fashe da kuka, tana cewa "Na gode da cin fuska, kullum sai ka mini gorin na tsufa, saboda kawai na haifar maka Jawad! to wadda kake yiwa kallon 'kuruciya saboda Ubangiji ya jinkirta mata haihuwar ta girme ni da shekara guda, domin ina Sha bakwai na kammala sakandire, ita kuwa Sha takwas cif. Amma saboda son sai ka nuna itace mai daraja shiyasa kake bata kuruciya, ni ka maida ni tsohuwar mace, to koma menene dai, kai ka zuke mini komai, sannan daga kai har ita dukkanku kun girme mini". Ya Galla mata harara tare da cewa "Sokuwa marar wayo kawai, wacce ba abin da ta iya sai kaifin harshe da kukan banza". Ya juya ya fice, bayan ya dauki wayarsa a inda ya tashi, ya barta tana kukan banza nata. Sai da ya yiwa Innah sallamah, sannan ya fita. Ya fito ya bu'de but din, ya samu almajirai biyu, ya dinga basu kayan suna shiga da shi. Sai da suka kammala ya basu dari biyar ya ja motar sa ya yi gidan Hajiyar Bichi. Ya isa ya tarar da Hajiya cikin Shirin fita unguwa, ya zauna ya gaisheta, ta amsa da murmushin da ya jima bai ga ta yi masa irinsa ba. Ya murtsike kunya ya ce "Hajiya ki yiwa 'yarki magana, tana nemana da jidali, ta fa'dawa Baban Na'ibawa ba yanzu, zata tare ba, saboda Allah wanne shiri zata yi? Tunda tana jin maganar ki, ki mata magana, wannan ai tsokanar shari'a ne, an daura aure mace ta cigaba da zaman a gidansu". Hajiya ta daure fuska sosai! Ta zuba masa ido na tsawon lokaci, shikuma ya sunkuyar da kansa kasa, ba dan ya yarda ya yi laifin da take masa kallon tuhuma akansa ba. Ta nisa ta Nuna kanta ta ce " Ni ka zo kana fa'dawa wannan maganar? Shi Babanku kana jin nauyinsa, kana ganin mutuncinsa shiyasa ka kasa cewa komai a gabansa, sai ni da ka raina zaka zo ka yiwa rashin ta ido?" Ya kuwa maze ya ce "To ni ya zanyi ne?
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157