Chapter 75
Chapter 75
yi karatu, to baza kiyi ba, idan kuma ya zama dole sai kin yi, sai dai kije a matsayin single amma ba matata ba". Hawaye ya balle mata, ta ru'ko hannuwansa cikin rawar murya tace "Na roke ka kar min haka! dan Allah kar bari na gasgata masu fadin ba zaka taba barina na yi ilimi ba". Ido cikin ido yace "gara ki gasgata su Sa'adatu, ada kam na kudiri aniyar ilimi sai kince ya isheki! amma Billahillazi yanzu na fasa, ba ki fara karatun ba, kina iya zagina, bare kuma na baki damar da kullum sai kin fita, kin yi cudanya da mutane daban daban, tunda na gane kawaye zasu iya rinjayar ki, zasu iya canja miki dabi'a, zasu iya ruguza mana kyakkawan zaman mu, daga lokacin na gane barinki karatu mai zurfi ha'dari ne, ilimin sakandiren da kika samu, yasa kina jin kina da yanci, Ina kuma ga kin shiga babbar makaranta, ki zauna ki yi rainon Jawad kawai, tunda nace ki cire loop din nan, amma sun zuga ki, kar ki bari ki tara yara mu tsufar da ke, to ki zauna ki tabbata da kuruciya". Kuka take yi, tana bashi ha'kuri, yace "na gama maganata, zabi na gareki, dan kuwa wallahi ba za kije ki koyo mini karatun raini da rashin da'a ba, a haka kina iya zagina,nan gaba kuma sai dai na ji mari." Kuka take yi tun daga kasan zuciyar ta, a duk tsayin rayuwarta a duniya a ranar ta fara sanin Ashe kuka ma kala kala ne, duk wadda tayi a baya na nisha'di da shagwaba ne, na yau ne take yin na zunzuruntun bacin rai. Ya kalleta yace "Ba abin damuwa bane Wannan fa, domin na riga da na baki damar ki, dan hakama nake ta dan jah baya, dan mu dan saba da rashin tarayyarmu, Ina tabbatar miki idan kin zabi makaranta akan aure! Wallahi zan dauki nauyin karatunki, kuma zan wanke ki a gun su Baffa, zan dauki laifin rabuwarmu Ni ka'dai." Murya na rawa tsabar kuka tace, "Dan girman Allah yaushe na zage ka?" "Kina nufin na miki sharri ba ki zage ni ba?" Ta sake ru'ko hannuwansa da kyau tana harhado kalmomi tace " Ni bance haka ba Malam! amma dan Allah ka yi hakuri, na canja Wallahi, ba zan sake ba" "A ranar da kika zage ni dama na tabbatar miki u will pay for it! zaki yi karatu da yardata ka'dai, idan na gamsu kin canja din da gaske, idan na tabbatar ba mahalukin da zai canja ni a zuciyar ki". Ya zare hannuwansa daga nata ya mike, itama ta mike ta tsugunna ta ru'ko kafafuwansa, tana fadin "Malam bazan iya barinka ba, dan Allah, ba dan halina ba, ka janye wannan kudirin ina son karatun amma da yardar ka nake so". Yace "idan kuwa kina son karatu da izinina, wallahi ba bana ba, to be frank Sa'adatu! ban san time din ba, har sai na gamsu ba third party a tsakanin mu, sai na gamsu na wuce zagi da diban albarka ta kowacce fuska daga gareki". Ta sake shi! sanin halinsa idan ya rantse shikenan ya gama magana, ta ha'kura tana jin bakin ciki tamkar ta mutu! ta huta. Kuka ba irin wadda ba tayi ba, Mk da kansa mamakin kansa ya ringa ji, bai taba zaton zai iya mata haka ba, sai dai wata'kila yadda take gasa masa duk maganar da ta zo bakinta yasa ya iya jarumta haka. Sa'adah tana ji, tana gani, ya hanata makaranta, duk ta zama wani iri, zaman nasu dai gashi nan, ta koma shiru, ba walwala sosai, kullum cikin kunci take amma bakinta dif, sai kuma yanayin data koma ya dame shi, fata yake su koma kamar da, rayuwar farin ciki, amma abin na neman cin tura, a zahiri dai suna zaune lafiya amma kuma babu nisha'di a cikin zaman. Saboda su Halima da suke fadin "dama ai sun san pooling dinta yake yi, ba wata makarantar da zai barta, duk dan'iskan namiji zai yi iya yinsa ya kulle matarsa a gida saboda sun San Annabi baya tuntuben harshe, duk abin da ka yi da matar wani, sai anyi da taka. Wattanni kusan biyu zamansu ba armashi, bata masa komai na laifi, amma kuma ta dadare ranta, suna cikin haka, aka fara babban zabe na kasa, kowa yasan Malaman jami'oi ne baturen zabe, Dan haka wata guda aka dauka ana yiwa su Mk horo na mussaman kan yadda zasu kare muradan yan kasa, kar su yarda ayi amfani da su, ayi wa dimokaradiya kafar ungulu, Malaman addini suka dinga musu wa'azi na suji tsoron Allah su yi gaskiya a cikin aikin da za su yi, karshe suka rufe bayanin da cewa duk wadda aka bashi kudi dan ya yi magudi, to ya karbe kudin ya adana, sannan ya yi adalci, ma'ana ya fadi sakamako na gaskiya. A yanzu da suke shiga shekaru biyar da aure shi da kansa ya tabbatar tsoron ta yake yi, idan akwai abin da ya tsana to ta share shi, ko ta tsiri fushi, ko ya fita sai ya dawo, yasan yadda ya yi ya shawo kanta, yayin da ita kuma take jin kanta a sama komai take so sai ta same shi, SUMAYYA kanta mamakin yadda Sa'adah ta dawo take yi, kullum cikin tsadaddun sutura take , hatta salooon din da Sa'adah take zuwa one in town ne, kullum suka yi waya sai ta mata nasiha ta saukaka buri, ta rage dorawa mijinta hidimar da bai kai ya yi ba. Itakuwa sai tace da ba zai iya ba, ai da bai yi ba, ya hanani karatu ai kuwa dole yamin yadda nake so, tunda idan ban ci ba ma, na waje ne zasu ci, har Sumayya ta gaji ta zuba mata ido tana mata addu'a. Rannan da yamma Zainab Ma'aji ta ziyarce ta, kasancewar ana daukan lokaci kafin su hadu a dalilin Zainab din tana karatu ne a Jami'ar jahar kaduna(K.a s.u). ba kowanne hutun ma take zuwa Kano ba, sai take barin hoste ta tafi gidan kanwar mahaifiyarta ta yi hutunta indai ba mai tsayi bane. Mamamki ta tsaya yi ganin yadda Sa'adah ta koma, ta goge sosai, fatarta ta yi fresh tabbacin tana samun tsadadden mai, tasan Sa'adah Yar gaye ce, amma ko kusa ba kamar yanzu ba, da ta ke samun dukkan wants dinta. Sauyi sosai ta gani tunda ga jikinta, da abubawan more rayuwa na gidan, da cima ta mussaman, ga wata irin ginshira da ta gani a tare da ita. A sanyaye Zainab tace "Kin zama wata Hajiya ko big madam zance? lallai Uncle a gaishe shi, ina Jawad? hatta maganar Sa'adah ta canja sai anfitar mata da wani salo na daban. lamarin da Zainab ta dinga dariya tana fadin ko za ki yiwa kowa wannan iyashegen ban da ni. Suka yi dariya gaba daya sannan suka shiga hira, a gidan Mk ya tarar da ita, ta gaishe shi da girmamawa, shikuma ya dinga mata barka da zuwa cikin karamci, a dan dawowarsa da ya yi , Zainab ta fahimci abubuwa biyu, Uncle Mk ya gama lalacewa akan soyayyar kawarta, yayin da ita kuma Sa'adah take amfani da hakan take yin duk abin da take so. Zainab ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157