Chapter 31
Chapter 31
yadda Inna ta kwantar da murya tana lallaba ta, tana cewa a ranta Inna ta koma lallashi. A fili kuma ta ce "To shikenan ki cigaba da addu'a Allah ya sa na ji ina son sa tunda na lura duk ya kwanta muku a rai" "Ai ni tunda na ji Baffanku ya yabe shi na ji ya kwanta mini a rai, kinsan mijin yayarki ma shi ne ya zaba mata, halayensa da nagartarsa kawai ya auna, shi yasa kema nake so ki masa biyayya kar ki yarda ya kubuce miki". Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA DADDAN LABARIN NAN*! *⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️* NA *Jameey yar'mutan kankia*. *Promo* *Promo* *Promo* _Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_. *#300-sau biyu a rana* *#500 -sau ukku a rana* *#700 -sau hudu a rana* _Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316_. *MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU KOFA A BUDE TAKE* _TUNTUBI_ 08032773332. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 36-37. Sannu a hankali cikin nutsuwa MK ke tafiyar da Sa'adah, a sati sau daya yake zuwa zance. Duk da ya karbi lambar wayar Inna tun da yanzu koyaushe wayar na hannunta amma ba kasafai yake kiran ba, duk a kokarinsa na ganin bai raba mata hankali ba, musamman da kullum jarrabawarsu kara kusantowa take yi. A bangarenta kuma sai ta ke ganin kawai rashin daukar ta da muhimmamanci ne yasa yake nuna mata rashin kulawa, musamman yadda Khalil ke kiranta safe da yamma sannan su raba dare ana musayar kalamai, shi yasa ya daina damuwa da rashin saurarar shi da ba ta yi a makaranta. A haka har aka rubuta jarrabawar JAMB, duk kokarin da MK ya yi na ganin Sa'adah ta samu rubuta jarrabawar abin ya ci tura! Saboda yadda Baffa ya ce masa "Ni sakandiren nan ma a dole na bar ta ta kammala ,yar uwarta aji uku kawai ta yi na aurar da ita, don haka ni ba zan barta ta tafi wata babbar makaranta ba, ta zo tafi karfina". Ya dan tsahirta sannan ya rufe maganar da cewa, "Idan Allah ya sa ta zo hannunka komai ma sai ta yi, amma ni a yanzu babban burina shi ne na sauke nauyinta da ya yi saura a kaina, na aurar da ita a hannun da ko ba na numfashi ba za ta koka ba". Kan dole MK ya ha'kura da maganar amma ya kudire a ransa Sa'adah za ta yi karatu har sai ta ce ya ishe ta. Gab da za su fara rubata WAEC wa'adin da MK zai yi a makarantar FGC ya cika, amma saboda yajin aikin da jami'o'i suke yi, yasa hukumar makarantar ta roke shi ya ci gaba da zuwa kafin lokacin da ASUU za ta janye yajin aikin. Kasancewar MK da sakamako mai daraja ta daya (First Class) ya fita, yana cikin wadanda Jami'ar Bayero za ta dauka don yin koyarwa. A haka suka ci gaba da tafiya a baibai tsakanin MK da Sa'adah, shi yana ganin ya ba ta lokacin da za ta yi karatu sosai, ita kuma tana masa kallon wanda bai girmama lamarinta ba, hakan ya sa take saurarar duk wanda ya nuna yana son ta ba tare da tunanin ai tana da wanda take so ba! Musamman da a lokacin damina Baffa ya fi zaman Gogel saboda kula da noman da yake yi, ita kuma Inna zuciyarta daya ta dauka MK ne yake zuwa. A haka har ta kammala makaranta gaba'daya, cikin wannan yanayin ta hadu da Alhaji Mamman! Asibitin (Arewa Surgery) suka je duba Mahaifiyar Safina ita da Halima, sun fito harabar asibitin suka hadu da shi, ya nemi su shigo mota ya kai su, Sa'adah ta'ki amincewa amma da yake tare suke da Halima sai da ta rinjaye ta suka shiga motar, a hanya ya nuna ra'ayinsa akan Sa'adah, wanda sam-sam bai kwanta mata ba, musamman da yake ta gan shi dattijo da alamun yana da iyalai masu yawa a karkashinsa. A lokacin wayar hannun ba ta da yawa sosai kamar yanzu, sannan mai madannai ce komai tsadar wayar. Ya tambayi lambar wayarta, Sa'adah ba ta ce komai ba sai da ya sake tambayar a karo na biyu sannan ta ce "Ba ni da waya." Bai yi mamaki ba tunda a lokacin ba ta zama ruwan dare irin yanzu ba, ko iyayenta ma Sumayya ce ta sayo musu don ta ri'ka gaisawa da su tun da ita ba mazauniyar gari ba ce. Ita kuma ta gaje ta Inna. Halima ta ce "Ba Inna na da waya ba?" Shiru ta yi da alamun dai ba ta son ba da lambar ne, shi kuma sai ya ce "Yawwa 'kawarmu a taimaka a ba ni lambar Innarmu!" Haka Halima ta bude wayarta ta karanto masa lambar Inna saboda ta ga alamun za su sami kudi a tare da mutumin. Duk kokarinsa na son sai ya kai Sa'adah har kofar gidansu, amma hakan bai samu ba, saboda ta kafe akan idan aka gan ta cikin motar da ba a san mutumin ba, za ta fuskanci tashin hankali, wannan kalaman ya sake jin son ta sosai, ya san daga dukkan alamu da ga Babban gida ta fito ma'ana gidan tarbiyya. Kan dole ya kai su gidan su Halima wanda ita ko dar ba ta ji ba, hakan ya sa yake ganin anya iyayen Sa'adah ba tufka suke wannan 'kawar tana musu warwarba? A dan haduwar nan tasu ya lura da kamewar Sa'adah, ya kuma gane rawar kan Halima, a ransa yana rayawa da zarar ya sami Sa'adah zai raba ta da wannan kawar da idan kawancesu ya ci gaba da wanzuwa, zai ta ba tarbiyar Sa'adatu. Halima ta shige gida ta bar su, bai wani jima ba shi ma ya ce zai tafi don ya lura da Sa'adah kamar a tsorace take, kudi ya dauko har kimanin dubu talatin ya ba ta ya ce ta bawa kawarta goma a ciki. Ta tattaro dukkan kunya ta yaba a fuskarta tare da cewa, "Ka bar su ba zan karba ba!" Shi kuma ya na ta fadin "Idan ba ki karba ba, ba zan ji dadi ba Sa'adatu." Da kyar tasa hannu ta karba ta yi godiya bayan ya karbi address din gidansu, wanda kai tsaye address din gidansu Zainab Ma'aji ta bayar. Jiki na rawa ta shige gidan su Halima ta tarar da ita a falo da kaninta suna kallo kasancewar mamansu tana wurin aikinta, haka suka shige dakinta, kudin ta ciro ta nuna mata suka hau ihun murna! Halima na cewa "Ai tunda na gan shi na san akwai rodina tare da shi sannan ba matsolo ba ne." Dariya Sa'adah ta yi tare da cewa, "Kin ga kuwa takanas ya ba da naki sakon." Dadi ya cika zuciyar Halima da ta ji yawan kudaden da ya ba ta, haka ta sake jan Sa'adah zuwa Country
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157