Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 74

Chapter 74

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duniya bani da kamar ki, mu kenan iyayen mu suka haifa, ki daina duk abubuwan da mijinki baya so, ki kara hakuri, idan ma ke yake zalunta ki yafe masa, ki yawaita addu'a sai kiga Ubangiji ya warware miki komai, fiye da yadda kike zato! Yanzu abin da nake so da ke, ki bashi ha'kuri, kar kuma a sake tada maganar koma wacce iri ce". Sai da Sa'adah ta ja majina murya na rawa tace "Anty shine fa yake fishi da ni, yake ta share ni, ba abin da banyi dan mu shirya ba, ya ki bani fuska, kuma sai ya kawo karata?" Cikin rarrashi Sumayya ta ce "bafa kararki ya kawo mini ba, nasan dai kuna zaune kalau ba zai barki ba waya ba, nice dai na tambaye shi Kuna lafiya kuwa, yace na miki magana baya son ya shigo da Baffa cikin matsalar, iya haka ya fada min wallahi". "To Anti na ji fa'danki, amma shima ki fa'da masa idan ina kuka, ya daina cemin na dame shi da kukan banza, ko na iyashege, ya bar komai ya rarrashe ni". Sumayya ta 'kunshe dariyarta tace "Zan fada masa, amma ki bashi ha'kuri first, nasan kafin ki yi tuba sai tura ta kai bango, kullum ina fada miki hakan sifface ta girman kai. "Anty sanin da, kika mini, wlh na bashi hakuri, ta hanyoyi da dama, ai ba sai na fada da baki ba, shi da kansa yasan na bashi hakuri, kawai dai ya runtse idanuwansa ne". "To yanzu ki fada da bakin ki yasan Ina da mutunci a gurinki, idan na fada miki zaki ji! Idan kuma kin ki, shikenan, kin wula'kanta Ni, kin wula'kanta kanki". Da haka Sumayya ta risinar da Sa'adah, sun dade suna magana har sai da kudin wayoyin ya kare tas, sannan suka ha'kura. Da kanta ta kai masa wayar, duk da Jawad na cewa ta bashi ya kaiwa Malam! ta bashi wayar ta zauna gefen gadon Sannan tace " Malam ka yi hakuri dan Allah". Idonsa a rufe, bai bude su ba yace "Ni dama barcin da kike hanani yi da daddare ne, bana so, hakuri na zai iya :kwacewa, idan zaki yi kukan ki ban hana ki ba, amma pls stay away from me, na riga na gane ban da mutunci ko ka'dan a gurinki, zaki iya zagina kan ki tsaye, zaki iya fada min duk maganar da ta zo bakin ki, na zuba miki ido ki yi duk abin da kika ga dama, amma ki jira sakamakon zagin da kika min, na rantse miki! ba zai tafi a banza ba". Ya karasa da rawar murya saboda 'bacin rai. Hankali Sa'adah ya yi mugun tashi, mussaman yadda ya yi maganar da dukkan zuciyarsa, ta zuba masa ido tana ganin yadda yake numfarfashi tamkar wadda ya yi gudun fanfalaki, dan tsananin bacin rai. Ta zame ta durkusa a jikin gadon ta ru'ko hannunsa "ka yi hakuri, ba zan sake ba". Ya bude ido da suka yi jah yace "wallahi za ki sake, ba dai kin bada kofar da wasu suka shigo cikin rayuwar aurenmu ba? ba kin fi gaskata maganganunsu, sama da nawa ba, nace ban son su zo min gida, kin nuna ban isa ba, saboda kina jin isar gidan na ki ne, na sha jan kunnen ki akan kaifin harshen ki, amma kullum sake koyon dabarun ba'kaken magana kike yi, ki rubuta ki ajiye wañnan *HALIN YAU* din da suke cusa miki, kina dauka babu nazari bare tsinkaye, ba inda zai kai ki sai nadama, na fara gajiya da halin ki, hakuri na ya fara kaiwa geji gaskiya, Menene bana miki da kike wulakanta ni haka?" Jikin Sa'adah ya yi wani irin nauyi, zufa sai karyo mata take yi ta ko Ina, ta kasa bude baki ta yi magana, dan hatta harshen ya mata nauyi ainun, hawaye kuma tamkar an bude famfo, Jawad da yake tsaye yana kallon su, ya karaso ya fara goge mata hawayen, Yana cewa "biskit za ki ci? ko Malam ne ya doke ki?" Ta kasa magana kamar yadda hawayen ya ki yankewa,ya zuba musu ido yana ganin yadda Jawad ke goge mata hawayen,yana kuma fa'din ta yi shiru, zai goyeta a kekensa, wani irin abu mai kama da tausayi ya tsirga masa yana ayyana karfin soyayyar da ke tsakanin uwa da 'da. Murya a dashe Mk yace "ki ci gaba da kukan, so kike ya 'kullace ni, ya zaci kamar Ina gallaza miki ne, idan girma ya cimmmani ya'ki jin 'kaina" Da sauri ta dago manyan idanuwanta ta zuba masa, a fili akan idonsa tace " Malam plz ba kai bane, ka dawo wancan Malamin nawa! mai yawan yi min afuwa, mai tausasa mini". Ya mayar da idonsa ya rufe yace "shikenan ya wuce, dauki "danki ku tafi gurinki barci zan yi". "Ka yafe mini?" "Nace ya wuce" ya fada a gajarce. Taja hannun Jawad! amma yaron ya coge alamun ba zai bita ba, ta tsaya tana kallon sa ya hau gadon ya kwanta jikin Babansa, Mk ya rungume shi yana ji a ransa shima fa Jawad na sonsa sosai😀Mk manya. Kwana biyu, Sa'adah ta sauko, tana komai yadda ya kamata, ta bangaren Mk shima yana iyakar kokarinsa na bai sake yin wata maganar ba, zai ci abincinta, idan ta masa magana, yana amsawa kadaran kadahan, kawai a shimfida ne ba ya kulata, ta gama shure shurenta, ya yi biris, duk da shima fama yake da shan lemon tsami. Tana zaune tana tunanin mai zata masa ya ta'ba ta, hawaye na siraro mata, saboda yadda abin ya dagula mata lissafi, mussaman yadda ta san shi da rashin ha'kuri a wannan harkar, idan ta hasaso ko a waje yake samu sai ta ji tamkar ta sume, ta sake ramewa ta yi zuruzuru, kamar ance kunna radio, aikuwa nan ta ji sanarwa a gobe litinin hukumar zartarwa ta kwalejin tarayya ta kano (F.C.E.) zata rufe yin registration.dan haka duk dalibin da bai yi ba ya hanzarta kafin a rufe. Ta yi shiru, ta tabbatar Malam yasan ranar da aka bude dan farawa, dan kuwa yana da aboki da yake aiki a gurin, duk da ba lakcara bane.(Non academic staff)ne.wani sashi na zuciyar ta yace kika sani ko ya biya miki ne? Da haka ta samu sukuni kadan. A ranar bai dawo da wuri ba, dan haka ta danne komai ta barshi ya gama komai cikin nutsuwa, sai da suka kwanta ta bijiro da maganar da ta ji a radio. Tsawon lokaci ya mata shiru, zuciyarta ta sosu da wulakancin nan da ya tsira, ashe haka yake jin rashin dadi idan ya mata magana ta share? ta daure tace "kana tare da ni kuwa?". "Ina jin ki, na sani, har na biya miki, yasa hannun ya ja drowar gefen gadon ya fiddo da teller ya nuna mata, farin ciki ya mamayeta, kafin ta yi magana sai taji yana maganar da ta kasa gane manufarsa. "Na gama miki komai illah wurin da yake bu'katar signed dinki!amma a yanzu na fasa, matu'kar da aurena akan ki! wallahi ba za kije makarantar nan ba". Cikin rudu tace "Ban gane ba fa?" Ya tashi ya kunna fitila, sannan ya zauna! ya zuba mata ido yace "Ina nufin idan har sai da yardata zaki

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});