Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ana yi musu gadar zare, daga gefen su Sa'adatu, wasu matan ke hirar da ta ja hankalinsu, duk da seniors din sune sosai, 'daya cikin matan ta ce "Ni da aure kuma mun yi hannun Riga, ba komai a cikinsa sai jidali, da hawan jini, baka da ikon yin komai na ra'din kanka, sai ka jira namiji, sannan baka da 'yanci ko kadan a aure". 'Dayar wadda da alamun ra'ayin su daya da wadda ta kammala bayani itama ta cafe da cewa "ai kuwa dai lubna da gaskiyar ki, dare, asuba, tsakar rana kowanne lokaci miji saka'dar ka yake yi tamkar jaka, amma da za ka bijiro da bu'katar ka, ba za'a maka ba, ko za'a maka din kuwa sai ka gama wulakanta". Lubna tace da Asiya "Ashe kin gane karatun! dan haka tsakanin mu da namiji a hadu ayi ar'kallah kowa ya kama gabansa, yanzu kiga da ka ke cin gashin kanka cikin kankanin lokaci ka mallaki abubuwa masu daraja, wadda macen aure sai ta shekara fiye da ashirin ba ta mallake su ba". Wata cikin su, tana bude Baki ta ce "Amma kuma matan aure sun muku zarra da mutunci da kuma 'kima, macen aure tana tsufa tana sake daraja, adalilin gatan da musulunci ya mata". Dukkan su suka sa mata dariya, suna ganin wautarta, Lubna ta ce "kai ku rabu da Hajara kunsan tunda ta gama wannan makarantar ba ta sake shiga aji da nufin zurfafa ilimin ta ba, kenan kanta a duhu yake bata san komai ba, tana cikin jerin matan da maza suka rufe a gidaje suke gallaza musu, suka kuma hana su fahimtar cigaban da duniya ta samu" Su Halima da suke jin tattaunawar suka kwashe da dariya suna fadin "ai yanzu duk wadda ta zauna namiji na mata mulkin kama karya mata ta rako duniya, a wannan karnin da ilimi shine komai yaushe zaka yarda a barka da jahilci, barin ma idan mijin naka mai ilimi ne? Da zarar muguntar namiji ta motsa sai dai ki ji ya amarce da mai ilimi, ko kiga yana jin kunyar ya saka ka a al'amuransa". Jikin Sa'adah ya yi sanyi ganin itama cikin rukuninsu ita kadai ce mai sakandiren, haka akayi ta kutsiri tsoma, ba a gama da wannan maganar ba, a saketa a kamo wata, da za su tafi, a motar Safina suka dunguma har kofar gidansu suka kaita, a hanya suka yi hirar Humaira Suraj da a yanzu take aure a sokoto, dama can ne garinsu aiki ne kawai ya kawo mahaifin ta Kano. Tun wannan lokacin Sa'adah ta fara canjawa, ita da kanta tasan ba abin da ta nema ta rasa illah motar kanta ba wai ta Mijin ta ba, amma zuciyar ta sai tsalle take mata tana ganin kamar ita ta wuce komai sai ta jira iznin miji kafin ta zartar, tana bu'katar ta zama yantacciyar mace mai yin komai babu 'dar balle fargaba. Kullum a WhatsApp su Halima na sake kuranta kyakkawar siffarta, har suna cewa ba wadda zai ganta yace ita ta haifi Jawad, ko su da suke 'Yan mata basu fita komai ba. Suna cikin wannan zaman na ba yabo, ba fallasa, Su Halima suka zo mata da kaya cike da katuwar leda, kana ganin ledar kasan tafiyayyace, sai da aka bude kaya, suka ga kayan Jawad ya kai set biyar, sai agogo na English gold, da kuma waya blackberry bold 4, da tarin alawowi da biscuit duk tsaraba ne inji Khalil abawa Jawad waya da agogo kuma nata ne. A kidime Sa'adah ta ce "Na shiga uku Safina idan Malam ya gani fa, da me zan kare kaina? Gaskiya bazan karba ba tsoro nake ji. Harara Suka galla mata, Halima tace "to kuma barinsa zaki yi ya gane daga inda suka fito, sai an kwana biyu kice Anty Sumayya ce ta aiko muku, waya kuma ki boye abarki sai ba ya gida, ko idan zaki je taron fitar kunya, na gaji da ganin ki da karamar android shiyasa na fa'da masa baki da wayar shiga taro". Safina ta dora da cewa "Da yake ya damu da farin cikin ki kasa da awa ashirin da hudu da fa'da masa ya siyo, ya bayar akawo miki, gaskiya Gogel kin tafka asarar masoya, na tabbatar ko yanzu da kika zama uwa, Khalil zai aure ki a matsayinsa na saurayi". Suka hada baki wurin cewa "duk da ke 'din ma kinfi 'yanmata da yawa nagarta". Tun lokacin hankalin Sa'adah yafi karkata kan wayar nan, kullum Mk ya fita za ta fito da wayar ta, ta yi komai, mussaman take da layi na daban a ciki, amma da layinta ta bude komai. Tun Mk na tambayar ba'asin canjinta har ya gaji, yana ganin ya kyaleta ya huta shima, dan taga yana damuwa ne shiyasa take masa wulakanci, dan haka ya rungumi sabuwar rayuwar da ta bude musu, hatta a shimfida ta canja, ba wai gudunsa take yi ba, kawai zama take yi tamkar gunki, sai dai ya yi kidansa ya yi rawarsa shi ka'dai. Haka nan abu kadan Jawad zai yi ta rufe shi da duka tamkar wadda take dukan babba. Wadannan dabi'u suna matu'kar ciwa Mk tuwo a 'kwarya mussaman dukan yaron da ta tsira, ko abu ne ya hadasu sai ta huce akan 'dansa. Rannan suna kwance sun gama mu'amalar da ba gishiri a cikinta balle Maggie, ran Mk a bace yake sosai, ya rasa mai zai mata kuma, ya riga ya kai gejin rarrashinta, ya gane gaba'daya kwakwalwar kifi ne da ita. Ya yi gyaran murya ya ce "tsakanin ki da Allah ki fada min me kike nufi da ni, rokon ki nake yi, yanzu na tabbatar ba kya sona Sa'adatu". Yana rufe baki ta ce "Kaine dai baka sona, komai zan yi a laifi na ke, 'dazu ba ka ga irin 'barnar da Jawad ya mini ba, dan na dake shi, ka hayayya'ko mini, salon kasa ya raina Ni". "Amma tun ba yau ba ki ke wannan fizgewar, yaushe rabon da ki saurare ni cikin da'din rai, kullum da bacin rai kike yarda da ni, ko kin yarda kai tsaye to sai dai ki zame mini tamkar gawa, anya kuwa dama kina sona? anya kina jin tsoron hakki na akan ki, amma na yafe miki, na kuma dauki laifin ko menene ki yi hakuri ki yafe mini". Ta tura baki ta ce"Tun yaushe nake ce maka zan dubo mahaifiyar Halima da ta yi hatsarin mota, duk yan ajin mu sun je banda ni". Murya ba amo ya ce " Hana ki dubo uwar Halima yasa ki ka na'de kafar wandon yin min wula'kanci haka?" Ta yi shiru ta kasa cewa komai saboda ta ga ya hassalo sosai, ya furzar da iskar bacin rai ya ce "Shikenan ko da wani laifin bayan wannan?" Kamar shasha ta ce "yauwa ni fa yanzu nake son motar nan, na ga kai kuma kana nufin kamar sai anja lokaci, kawai ka dakatar da ginin ka siya mini". Ya kalleta ido cikin ido ya ce "yin hakan shine sharadin samun zaman lafiya a tsakanin mu?" Ta kasa amsawa tsawon lokaci, dan haka ya ce "Ba wadda zan miki ko 'daya, idan ya so zaman namu yafi haka muni". Ta tashi ta fita tana 'kun'kuni, akan

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});