Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 124

Chapter 124

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da ni, ka daina zuwa wurin ubana, kai ba 'dan-uwanmu bane, bamu da alakar komai da kai, akan me zaka zo ka dinga yi mini katsalandan a tsakanina da ubana, alhalin lokacin da ya kamata na shiga rigar uban nawa nuna mini ka yi bai isa ba, amma yanzu kana mini karfa karfar dole ka shiga rigarsa". Jikin Mk ya yi sanyi kwarai da gaske ya ce "Allah dai ya so ba daga sama na fado ba Sa'adatu, kina yawan yi mini gorin bamu hada komai ba, na yarda bamu hada komai ba, amma Jawad ya hadamu, Baffa ai kakansa ne wannan hadin ai ya wuce ace na zama bare". Ta kufulo ta ce "oh saboda Jawad kake mini wannan bibiyar, kake neman hada ni ya'ki da tsohona, to albishirinka, duk duniya uwace kawai ta san ainihin uban danta". Wannan karon bai kai hannu jikinta da niyyar duka ba, amma ya yi matu'kar kidima, wani irin tashin hankali ya bayyana a fuskarsa da jikinsa, sai ta ganshi tamkar ranar da ya saketa. Ya jingina da bango yana fa'din"Ya Hayyu ya QAYYUM bi Rahamatika astagisu". Abin mamaki tausayinsa ya shigeta soasai, amma ta daure ta hadiye shi. Ido jawur ya kalleta ya ce "Ki yiwa Allah da Ma'aiki ki fa'da mini mai zan yi ki daina jifana da irin wadannan kazaman kalaman da suke nufin tarwatsewata". Yana rufe baki ta ce "ka daina shiga tsakanina da ubana saboda kai Baffa ya mini abin da har na mutu ba zan daina takaici ba, ba zan daina zubar da hawaye ba, ba dan darajar sa ta zarta komai a gurina ba, wallahi da ba zan yafe ba domin iyakacin cin fuska anyi mini, ba kuma dan komai ba sai dan ya faranta maka". Ya tausasa murya ya ce " Fada mini abin da ya miki saboda ni, na miki al'kawarin idan na ji kina da hujja ba zan sake zuwa wajensa akan maganar ki ba, ke kawai zan tunkara, ke kuma ai sai kin amince". Murya na rawa ta ce "kasan dai ai kusan sadakata Baffah ya baka, Nima nasan haka aka kai ni ba wata hidima, amma dai naje da gadona da kayayyakin amafanin da suka fi zama Dole. Na so a mini kayan daki da lefe kamar yadda ake yi a al'ada amma na yi hakuri na bi ra'ayinsa, dan samun albarka. Bayan mun rabu na tattara komai da nake ganin kamaar lefe na ne, har da gold dina sai da ya nutse na sayi filaye da zummar idan hidimar iyayena ko aure ya zo mini a siyar ayi hidima, kawai Baffa ya je ya siyar mini ya baka kudin ka yi aure kana jin dadinka ni kuma ko na mutu ko na yi rai ko oho". Wani irin kuka ya kwace mata, fiye da wadda ta yi a ranar rabuwarsu a mota, sosai take yinsa saboda yadda abin yake dafata. Kukan da take yi ya wanke bacin ran da ta jefa shi a farko. Tausayinta ya maye gurbin takaicin maganar da ta caba masa ya ce "Tabbas ba a miki adalci ba Sa'adatu, amma ki yi hakuri, na yarda kuma Baffah ya na sona, amma ko daya cikin goman son da yake miki ban samu ba. Da ciwo sosai, da gaske kuma na taya ki jin takaici, amma bari na tuna miki wasu abubuwa, Ni dai na da'de ban ga mai sa'a irinki ba, tabbas kin ci sunan ki na Sa'a". Ya nisa ya ce da" kin san irin soyayyar da Baffah yake Miki da kin ji kunyar takaicin ya siyar da abinki ya bani na yi aure." "Da kin san yadda Jawad yake son ki, yake fatana ya girma ya yi ku'di dan ya jiyar da ke da'di, da ba abin da sai sake damun ki na dai wani abu da ku'di zai iya siyansa." "Da kin san yadda nake son ki, nake kwana nake tashi da ke, nake jin kin fi duniya da abin da yake cikinta da baki yi kishin auren Farida ba". "Bari yau na fa'da miki gaskiyar magana ba dan ki yarda ki karbi soyayyata ba, sai dan ki gamsu iyakacin gaskiyar kenan, ina da yakinin ban ta'ba yi miki karyar da ban cancanci ki 'ki gasgata ni ba". "Farida na cikin jerin matan da ubangiji ya kaddara mini zan aura. Rabuwarmu ta zama tilas Sa'adah domin itama kaddarata ce. Kin sani idan ina tare da ke wallahi duk yadda nake zage 'kwanjina akan ki, zai yi wahalar gaske na iya aure, bani da wannan 'kwarin guiwar saboda tsananin son da nake miki. To fa'da mini ta yaya zan auri Farida alhalin hakan ya zama dole, na farko mutuwa na iya kauda ke, na biyu kaddara ta rabamu, kinga da ki mutu ki barmu, ai gwara kadarar rabuwar tunda idan da rai ai da rabo". Sannan Dan Allah bai isheki daraja ba ace ke ce kika biya sadakin kishiyarki, ke kuwa ni zan biya na ki, na tabbatar abin da Jawad yake yi miki a shekarunsa ya isa ki gane ubangiji yana tare da ke". Jikinta ya yi sanyi ta san kalamansa duka ba karya, illah wadda ya ce ta fi duniya, da hakane ai da sai ya bari kaddarar ta kasheta in yaso shima ya zauna jiran wa'adinsa babu aure har ya mutu, su hadu a aljannah su sake rayuwar da babu bacin rai, amma yanzu ya gama curarta ya bari wannan makirar da take boye ainihin kalarta, ta san komai nasa, ta mallake shi, shine zai zo ya mata da'din bakin wai ta zarce duniya? kai namiji Hankaka ne tabbas. Ganin ta yi lakwas sai ya ce "kin gamsu kin yarda?" Ai kuwa tamkar wadda ya mareta har huci take yi ta ce "Wallahi ko shiga kunnuwana wai kana sona fiye da duniya bata yi ba, na dai yarda Baffah da Jawad na zarce komai a gunsu". Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "shikenan ba sai kin yarda ba. Ko ba kya sona mu komawa aurenmu, son da nake Miki, da wadda Jawad yake miki ya isa yasa ki rayu cikin farin-ciki". Ta goge kwalla ta ce "har abada ba zan yi farin ciki a hannun ka ba, ka rufe idonka ka ce mini ina ha'intarka, ka rufe ido ka ce mini ana maka sharing dina" Muryarta ta fara rawa tabbacin tsumin bacin rai ya taso, ta nisa ta ce "ka rufe idonka ka barni ka dauki wadda kasan na tsaneta saboda munafuncinta, ta faki idon mutane ta tsokane ni, amma sai ta layance a kuma bata gaskiya. Allah ne ya rufawa al'umma asiri ba karatun lauyanci ta yi ba, dan anga kwarewa wurin bada kariya ga karya". Da 'kyar ya ce na janye kalamina, wallahi tashin hankali ne da kishinki, Amma nasan ha'inta dai babbar ha'inta ba zaki yi ba, na san ni ka'dai ne na muaamalance ki, na tabbatar da hakan har zuciyata". Wani abu mai nauyi da ya danne kirjin Sa'adah shekaru uku ya fa'da mata sai dan saura. Ta ce "to shikenan na yafe maka. Amma ka sani gaskiya ban da buri ko sha'awar auren mai mata kishi kashe ni zai yi, kawai ka barni na auri wadda zan sami nutsuwa, ka bar ni nima na dandana

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});