Chapter 93
Chapter 93
ke, ba sai da shi za ki rayu ba, ba sai da shi za ki yi farin ciki ba, ki dube mu, ruwa da iska ba zamu canja ki ba, shi kuwa ko gobe kina iya jin ya auri madadin ki, ya shayar da ita soyayya irin ko ma ta zarta wadda ya miki, fatana dai ki 'dauki darasi, kar ki sake maimata irin kuskuren da ki ka yi idan kin samu wata damar". Ganin maganganun na shigar Sa'adah sosai, Sumayya ta zarce da fadin "gaba'daya aure ha'kuri ne da kawar da kai, duk macen duniya da ki ka ga ta tsufa a 'dakinta ta shiga 'kalubale kala kala, amma idan aka yi ha'kuri aka danne sai a cimmma babban matsayi, ki cire buri, da son 'kyale 'kyale ki rabu da 'kawayen banza na tabbatar wadannan abubuwan sun taka muhimmiyar rawa wurin mutuwar aurenki". Sosai ta ke kuka a 'kirjin Sumayya karon farko tun bayan rabuwar su da ta samu ake rarrashinta cikin tausayawa. Haka suka shafa lokaci mai yawa Sumayya na lallashinta, tare da 'karfafa guiwarta. Kwanaki goma Sumayya za ta yi tare da yaranta, adalilin Yaran suna hutun zangon karatu na uku, sannan kuma mijinta na cikin tawagar da aka zaba zuwa New York din 'kasar Amurka akan sanin dabarun inganta bankunan 'kasashen Africa. Zaman Sumayya ya taimaka wa Sa'a sosai, tare suke cin abinci, sannan sai da ta sa Inna ta sauko da ga fushin da take yi da ita, Baffa kuwa cewa ta yi tasan duk dauriya yake yi, amma ai shi da Iyah sai Allah. Ya yi dariya ya ce "wato ta tabbata kema zargina kike akan na fi sonta, kamar yadda itama ta ke 'kalubalantar gyatumarku ta fi son ki". Sumayya ta yi dariya ta ce "Ni bana kalubalantar ka Baffa, ai ita 'karama ce, sannan sunan iyakar ka ce". "Allah ya miki Albarka Sumayya, yau kusan shekaru sha bakwai da auren ki, ba ki taba janyo mini bacin rai ko jin kunya ba, ina fatan ki dore da hakan, ina matu'kar jin dadi, Ina alfahari da kasancewa ta uba a gare ki, Àllah ya miki shirya miki zuri'a, ya faranta miki, ya buda miki kofofin alheri". Cikin kukan farin ciki ta ke fadin "Ameen Baffa!ni ma Ina alfaharin da ka kasance uba mai kare mutunci da martabar yaransa a gidajen aurensu madallah da uba irin Baffah na". Sa'adah da ke 'daki tamkar mujiya ta ji wani 'kullutun ba'kin ciki ya mamayeta tun farko dama tana kishin taga iyayen ta suna nunawa Sumayya soyayya sama da ita, duk da Inna ta fi wannan abin dan ta cusa mata takaici, amma Baffah kowa yasan itace 'Yar gaban goshinsa, amma wai yau ita ya ke yiwa zambo, yana nunawa Sumayya ce mutum, yana ta 'kwararo mata addu'a ita ka'dai. Hawaye na zuba 'kasa 'kasa ta ce "Ni da na yi shekaru bakwai aka sako ni, sai a kore ni ko a tsine mini na bi titi ina tsince tsince". Da sauri ta tura hular kanta a baki tana cewa " Astagafirillah Ubangiji ba da Baffah na ke ba da kaina na ke, Allah na tuba, ka yafe min, ka mini albarka, ka saukaka mini lamarina, ka mayar da ni 'dakina". *SURAYYA DAHIRU* ✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU GWARAM*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A kiyaye ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Gaisuwa da fatan alheri ga wadannan groups din* *M HAUSA NOVEL* *MAMAN YUSUF FANS*. *ASMA BAFFAH FANS*. *MAMAN MAMAH NOVELS*. *HUGUMA CONVERSATION*. *THE SPARKLE*. *DUNIYAR NOVEL*. *UMMU ILHAM HAUSA NOVEL*. *MARUBUTA* *BENEFICIAL WRITERS* *ZAUREN KARATUN HAUSA*. *FAR JEED-DAH HAUSA NOVEL* *BAKANDAMIYA HIKAYA*. *QIYAS HAYAT HAUSA NOVELS *_Dukkan ku madallah na gode da yabawa*_. *Fatan alheri ga Aminyata* *SHAFA'ATU ALHASSAN BAUCHI* *Na gode sosai da yabawar ki kan rubutuna ubangiji ya dorar da zumuncin mu, Sa'adah ta ce ki rokar mata Mk*😁 *_JAN HANKALI_* *BABU MAHALUKIN DA YAKE SO A TABA MASA ABIN DA YA SHA WAHALA KAFIN YA SAMAR DA SHI BA TARE DA IZININSA BA! SABODA HAKA A CIKIN MAFI YAWAN SHAFUKAN NA KAN YI GARGADI AKAN LAIFI NE TA'BA WANNAN LABARIN TA KOWACCE IRIN SIGA BA TARE DA IZININ MAI HAKKIN MALLAKA BA. A YAU NA CI KARO DA HALIN YAU DOCUMENT WADDA AKA YI BAN SANI BA, NA ROKE KU KAR A KUMA, NASAN SOYAYYAR LABARIN CE TA KAWO HAKAN, AMMA NI KO KUNGIYAR DA NAKE CIKI NE KA'DAI KE DA IKON YIN HAKAN, INA FATAN ZA'A FAHIMCE NI, DOMIN RASHIN KIYAYEWA KA IYA ZAMA DALILIN KATSEWAR LABARIN GABA'DAYA. UBANGIJI YA BAMU DAMINA MAI ALBARKA!_* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 81_82. Zaman Sumayya ya taimaka 'kwarai wurin ragewa Sa'a damuwa, haka nan basu koma Gombe ba sai da suka kwashe kwanaki sha biyar a maimakon goma da za su yi. Ranar da suka tafi ba 'karamin filin'dakin Sa'adah ta gani ba, tana jin tamkar sun tafi da wani sashe na jikinta. *SATI BIYU* Ranar da ta ga period 'dinta na uku, hankalin ta ba 'karamin tashi ya yi ba, damuwarta ta dawo sabuwa fil. Cikin dare ta kasa barci ta rasa inda zata tsoma ranta, ga fanka na ka'dawa a sama, amma zufa ke damunta ji take tamkar ana hura mata wuta, tana zaune banda tunani iri iri ba abin da ta ke yi. Tsawon lokaci tana zaune, kafin ta tashi da 'kyar ta fita zuwa ban'daki, dan watsa ruwa. Ta fito, har za ta shiga 'daki idonta ya hango mata wayar Inna a cikin bahon kayan sana'ar ta, da mugun sauri ta juya ta 'dauko ta shige 'dakinta, dan Inna bata bari ta 'daukar mata waya. Sai da ta kintsa kanta sosai gudun staining. Sannan ta 'dauko wayar ta shiga lalubo lambar Mk! Zuciyarta na bugawa da 'karfi, cikin sa'a kuwa bai kashe wayar ba, abin mamaki kuma bugun farko ya 'dauka, ta daburce ta rasa me za tace, sanin halinta da ya yi wadda masu azancin magana suka ce yafi sanin kama. Yasa yace "me ya hana ki barci?" Cikin rawar murya tace " Malam!" Sai kuma ta kasa magana kawai ta saka masa kuka sosai. Kukanta da yake ji ya taimaka wurin sake jefa shi ru'danin da yake ciki, tun rana yake cikin fargaba da yaga kwanan wata a wayarsa. take ya tuno a irin wannan kwanan watan Sa'adah ke fara ala'adarta kenan tana gaf da fita daga matarsa, tun lokacin, ya rasa kwanciyar hankalinsa. Ya tabbatar itama dalilin da yasa take kokawa kenan. Ya rasa me zai ce mata. Tsawon lokaci suna haka, tana rera masa kuka, shi kuma yana ri'ke da wayar a kunnensa yana sauraronta, sai kuma ya ji 'kiran ya katse. Ya duba sai ya ga ashe ita ta 'kira, wata'kila kudin wayar ne ya 'kare. Bai yi jinkiri ba, ya bi bayanta, ta 'dauka ta na cigaba da kuka tamkar matar sabon mamaci. A hankali ya ce "ki daina irin wannan kukan za fa ki ha'du da ciwon farat 'daya".
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157