Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 135

Chapter 135

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dauketa kwalliya ba, domin ko a gida haka nake". Da sauri Sumayya ta ce "gaskiya ce sai na fa'da miki, Hajiyar Bichi na gurin, duka danginsa suna gurin, ki je dubiya cikin irin wannan kwalliyar tamkar me shirin shiga gasar miss Beauty. Ba nadama ba komai a al'amuranki". Inna ta ce "ta shi ki wanke fuskarki sai ki dauko Hijabin ki dora, ai kinsan yadda hijabi ma yake karbar ki". Ta mike tana kunkuni wadda yake nuna Sumayya ta fitineta da yawa, dan yanzu ta fi zaman gidanta, to wannan satin ma ba komawa zata yi ba, har sai ta nemeta da kanta. Yayin da Sumayya ta ce "Ai yanzu kin tabbatar zaki samu burin ranki dole ki tattaro dukkan iyashege ki dawo da shi". Ai kuwa Sa'aadah ta fasa uban ihun kuka. dai dai lokacin Baffah ya shigo, ya dinga tambayar ba'asin kukan da take yi mai daukar hankali. Ai kuwa ta fito cikin kuka ta ce "Baffah shata mini layi da Maman Khalifa, ta takura ni, ta matsa mini, saboda ta san duk abin da ta yi mini Inna ba zata ce ta yi laifi ba". Ya murmusa ya ce "Uwata an taba shiga tsakanin hanta da jini ne, inace da dukkan uku hade mini kai kuka yi. Yanzu kuma sai kice na shata miki kayi da ita? Ni bana haka, ya kalli Sumayya ya ce ke kuma ki ri'ke girmanki ai dai yanzu kin wuce kisa ta kuka irin haka". Murmushi sosai Sumayya ta yi, cikin sanyin muryarta ta ce "Baffa daga na ce bai kamata ta je dubiya da kwalliyar da ta yi bane shikenan fa laifin nawa, kuma gani na yi tunda ba zance zata je ba, dubiya ne ai sai ta rage zumudi". Dariya ta kwace wa Baffah ya shige dakinsa. Ba tare da ya yi magana ba. Yayin da Sa'adah ta cigaba da kuka sosai, har Zainab ta gaji ta shigo gidan a fusace. Ganin kukan da take yi, ya tayar mata da hankali ta yi zaton ko Mk ya amsa Kiran mahallicinsa ne. Amma da ta ji ba'asin kukan sai itama ta hau dariya har tana fadin "Yo dama Ni nasan ba wani bata sonsa, idan akwai abin da na gasgata a duniyata, to kuwa son da take yiwa Uncle na cikin su". Ai kuwa ta mi'ke a fusace ta ce "Wallahi Zainab har yau din nan ina jin karfi a tare da ni, ya ishe ki". Zainab ta watsa mata harara ta ce "Da shekarun nan naki, da ilimin lauyancin na ki, da Jawad duk basu sa kin ji cewar kin girma ba? Amma kuwa dai kin ji kunya, kuma na gasgata Anty Sumayya lallai murnar zaki komawa muradin zuciyarki yasa ki wannan fallin, gara ma ki 'dore da kyawawan dabi'un da Kika dauka a shekaru bakwai din nan domin dai kin san yanzu ke Uwargidace kina da amarya mai tsananin wayo da kissa". Ba'kin cikin maganar Zainab ya sake sawa ta fashe da sabon kuka tana fa'din " Asibitin ma ba zani ba". Baffah ya fito ya dubi Zainab ya ce "Ni na fi ku fahimtar Iyah tuni Mutari ya fita a ranta, biyayya kawai zata mini, zuwa duba shi ma ai dole na yi mata, ta kuma yarda zata mini biyayya, dan haka ku daina cewa tana sonsa, ko dan shi ta yi kwalliya domin kuwa dukkan mu shaida ne akan Iyah dangin Dawisu ce". Jin hakan ya sa ta yi shiru. Yayin da Zainab ta ce "To Baffa ka fa'da mata a biyayyar da zata yi maka ta hada har da sanin ta girma, kar ta koma ta zama ta bizaro a gidan Uncle domin yanzu ba ita ka'dai bace, tana da kishiya mai fi'ilin tsiya". Baffah ya murmusa ya ce "ke kam Zainab sai a gaishe ki, dukkan mace ai da inda take da tasiri, Ni kuwa na san ko mata uku ne da Mutari ban jin Iyah zata kasa samun kansa, ai duk wannan shagwabar da take yi na gata ne". Daga haka ya fice ya na fadin "lallai ki fito ku je dubiyar nan Iyah, kinga ba lalle Zainab ta sake samun sukunin fitowa a gobe ba". Ta fito cikin bakar doguwar riga mai kyau. Tana rataye da Yar karamar jaka, kafarta sanye da flat din talkalmi wadda mahadin jakar ne, powder ce kawai a fuskarta. Zainab ta mike ta na cewa "Inna sai mun dawo". Har suka isa asibitin Sa'adah bata ce kala ba, duk da Zainab na janta da hira. A wajen asibitin Zainab ta samu jikin bishiya ta yi fakin. Suka fito suka taka ciki da kafafuwansu. Da Abbas suka fara yin tozali, yana zaman jiran Farida ta fito ya mayar da ita gida, dan haka ya mike ya musu jagora har dakin da Mk yake kwance. A zaune suka taradda shi, Farida tana tsaye a gabansa hanunta na dama ri'ke da hannunsa, yayin da hannun na hagu ri'ke da kwandon zuba abinci, alamun tafiya zata yi. Zuciyar Sa'a ta buga da tsananin gaske, ta zabura, zata koma da baya, Zainab da Abbas kawai suka lura da hakan, Dan haka cikin hikima Zaynab ta ru'ko hannun ta da karfin gaske, kan dole suka karasa shiga sosai. Zainab suka gaisa da Farida ta tambayi mai jiki, sannan ta gaida Mk da ya yi mutuwar zaune, saboda yadda ya ji wani abu da bai san menene ba ya dirar masa, gashi dama fama yake da rashin karfin jiki. Surayya Dee ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *GAISUWAR GIRMA GA* *HAJ SALIHA A.A. ZARIA.* *MARUBUCIYAR BEGE* *ALLAH YA KARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA MAI ALBARKA*. 104-106. Farida na ri'ke da hannun Mk, ta kalli Sa'a da murmushi ta ce "Maraba da Gogel, karaso kusa mana". Takaici a zuciyar Sa'adah tamkar ta rushe da kuka, ta ki sakar masa hannu dan ta nuna mata itace matarsa. Sannan dan ta tabbatar mata ita bakuwa ce yanzu a wurin Mk, shine take mata iso a gabansa? Ta daure ta hadiye damuwarta ta yi kamar bata ga hannuwansu a sarke ba, ta cewa Farida "Sannun ki". Daga inda take tsaye ta kalli Mk ta ce "ya ya jikin?" Daga haka ta tsuke bakinta, tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta, tabbas Mk ne ya wula'kanta ta saboda ya nunawa Farida ita ba wata tsiyar ba ce. Shiyasa ya ki zame hannunsa da yake cikin nata. Amma ai ya yi da yar halak. A hankali Mk yake kallonta ta kasan ido, yana nazartar yadda take kokawa da fishin da ya ke yun'kuro mata. Cikin hikima ya zare hannunsa a hannun Farida, gumi sai yanko masa yake yi. Da sauri Farida ta 'kara karfin A.C da gudun fanka, saboda zufar da taga na karyo masa wadda kawai ta fargaba ce. A ransa ya dinga nazarin anya zai iya jarumtar ri'ke mata biyu kuwa? Saboda yadda ya dinga zullimin kasancewarsa a gabansu a lokaci 'daya. Mk na wanna tsinkayen ya ga Farida ta ajiye kwandon hannunta tabbacin ta fasa tafiyar kenan. Wato duk ha'kurin mace

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});